Ads

Tuesday, 4 June 2019

Illolin da kayan kwalliya ke haifarwa

Babu shakka kayan kwalliya na taimakawa matuka wajen bunkasawa da kuma kara fito da kyanki. Kai kayan kwalliya irin na zamani ba kayata kyau ba ma har kawar da muni suke yi. Zan iya cewa irin kayan kwalliyan da ake da shi yanzu da wadanda ake kirkira a kullum, amshin addua ne ga masoya kwalliya a duk fadin duniya.

KARANTA: "ILOLIN SHAFE-SHAFEN BLICING GA MATA"


Sai dai akwai matsala. Sau daya yadda muke amfani da kayan kwalliyan kan iya haifarwa fatarmu matsalar da kayan kwalliyan ko dubu nawa ba za su iya rufewa ba. Insha Allahu yau Duniyan Fasaha ta kawo muku hanyoyi guda uku (3) da ake amfani da kayan kwalliya wadanda fata da ace tana da baki da ta koka:

1.==> Kwana da kwalliya a fuska: A lokacin da muke barci ne jikinmu ke aiki tukuru wajen kawo karshen matsalolin da sassan jikinmu ke fuskanta, ba’a bar fata a baya ba. A yayin da muka kwanta barci da kwalliya, hakan baya samuwa domin kuwa kayan kwalliya na yin kane kane a cikin kofofin fata su hana ruwa gudu. A dan haka sinadaran da zasu karawa fatarmu inganci, kyawu da sheki ko dai daga wani mai da muka shafa akan fatar ko kuma wanda jikinmu ya sarrafa daga abinci ba zasu iya yin amfaninsu ba yadda ya kamata.

Karanta: Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi


Idan mutum mai saurin samun kuraje ne, hakan yakan kawo su da gaggawa, idan ma ba kya yin kuraje to tabbas za ki tashi daga barci kiga fatarki ta rasa shekinta da kyawunta. Ci gaba da yin hakan zai tabbatar da lalacewar fatarki a nan gaba. Ki tabbatar kin wanke kayan kwalliya tsaf daga fatarki, daga su har kamu kamunsu kafin ki yi barci da daddare dukkuwa irin gajiyar da kika yi.

2.==> Amfani da kayan kwaliyan da irinsu bai dace da irin fata ba: Idan fatarki tana da maiko, ki ka je kika sayi kayan kwalliya masu tushe mai maiko, toh kinyi amfani da kudinki kin jibgawa kanki aiki, gani da yadda suke da matukar tsada ma a yanzu ya sa ya cancanta ayi maki jaje. Dalili kuwa shine maimakon ki kara kyau, da kin shafa sai fuska ta cika da maiko.

Banda toshe kofofin fata da kayan kwalliyan sukayi, ga kuma maiko ya zo ya kara na shi akai. Hakan yana haifar dawa fata matsala matuka.

Haka kuma idan kina da busasshiyar fata kika fara amfani da kayan kwalliya marasa maiko, nanma fa akwai matsala domin kuwa fatarki zata yi ta bushewa har ta fara yamushewa ta zama kamar ta tsohuwa. Banda hakan ma, wani lokaci irin sinadaran da ke cikin kayan kwalliya masu hatsari ne ga lafiyar fata, shi yasa za gi ga yawanci an rubuta cewa ki dan gwada kadan a matse matsin gwiwar hannunki na tsahon awanni kafin ki fara amfani da shi. Amma da yawanmu bama yin hakan. Sai an gama shan kyau, fata kuma ta zo ta zama kamar taswirar Nijeriya, a zo ana cewa an samu ‘skin reaction’ da ba’a san dalilin sa ba.

3.==> Amfani da kayan kwalliyan da suka tsufa: Brushes din da ake amfani da su wajen yin kwalliya da bakin kayan kwalliya na matsawa irin su foundation gurin taruwar kwayoyin cuta suke zama. Shi yasa aka shawarci ma’abota kwalliya da su tabbatar cewa ko da yaushe sun ajiyesu a guri mai tsabta, sun kuma tabbatar da ba’a hada amfani da su da kowa ba.

Karanta: Yadda za a magance kodewar fata


Ban da haka ana so a daina amfani da mascara guda daya bayan wata 3, shi kuma foundation bayan shekara daya. Idan basu kare ba kawai zubar da su ake. Brushes kuma za’a iya wanke su a cikin ruwan zafi domin kashe kwayoyin cutar lokaci lokaci. Ajiye kayan kwalliyan nan a cikin jaka daya su hada datti su hada datti ba alkahairi bane ga fatarki, wani lokacin ma har kaisu baki ake yi wanda anan ma zasu iya kwaso matsala daga yawun baki. Ya kamata dai a kiyaye, domin ni fa na fi son naga kowa tsaf tsaf, fata na sheki kamar wancan abun da na manta sunashi

WANE IRIN WAYA YA DACE KA SAYA?

 Wane irin waya ya dace ka saya?
amsar tana cikin me zakayi da wayar, mukan Sami matsala wajan siyan waya bamu san me zamuyi da ita ba Ko kuma wana irin sabon abu tazo da shi ba a'a kawai mai tsada ce to tana da kyau. Ba haka bane akwai Karin kudi na sunan kamfanin waya, domin zaka samu waya ta kamfanin Samsung da ta kamfanin HTC sunfi kowane kamfani tsada bayan akwai kamfanunuwa wadanda suke wayoyi masu kyau da sauki irinsu xiami, plus1, infinix da sauransu. Mun gwammace mu Sai mai tsadar nan kawai Dan ace na rike waya mai tsada. Akwai Abubuwa masu amfani guda biyar da su suka fi komai amfani a waya wato RAM, PROCESSOR, GRAPHICS,CAMERA Sai kuma Operating system wani lokacin internal storage.

RAM.

RAM ana kiransa da random access memory wato memory ne da yake Shiga ko ina dan ganin waya ta tafi dai dai, kuma yana da matukar amfani a cikinta domin shine yake bayyana me waya take da karfin yi, me zata iya dauka na application domin akwai game da zaka ga nauyinsu kadai yakai 5GB kasan dole in aka ce RAM dinka karami ne bazasuyi ba ko kuma kaga hasalima wayar tana daddakirewa wato tana slow in kayi sa'a yayi kenan. A wannan zamani yawanci wayoyin da akeyi suna zuwa da RAM Wanda ba ya gaza da 1GB sai dai in yan China ne wato wadanda basu da kyau domin duk operating system da yakai 4.0  a wayar Android dole yana bukatar wannan RAM din. Dan haka Ina bada shawara ka dinga tambaya
Ko kuma ka Shiga settings> Apps> running a kasa zaka ga yawan ram din nawa Akai amfani da shi da kuma nawa ya rage.

PROCESSOR.
Processor wani abu ne da ake sawa ajikin injin waya wanda yake temakawa wajan saurin aiki, suna tafiya tare ko yaushe da RAM domin processor baza ta bada saurin da ake bukata ba matukar ba a saka mata RAM din da yadace da ita ba misali. Akwai tsarin sa processor biyu ko hudu da akeyi yanzu wato dual core, ko kuma quad core. Amma in kasa wannan processor din bakasa RAM din da yakai 1GB ba kwarai wayar bazatai saurinba domin kamar jiki Ba lafiya amma zuciya tanasan ai tafiya kaga wannan bazai yiwuba so shima anan haka yake. Yadda zaka gane ya karfin Processor dinka take shine zaka Shiga settings>  About phone/tablet> device information zaka ga yawan RAM da kuma Karfin Processor ana aunashi da alamar GHz kuma da yawan su a cikin wayar wato biyu ne ko hudu.


GRAPHICS.

Graphics yana nufin kyan zane da fitar kaloli a jikin waya. Manyan wayoyi sukan bada graphics mai matukar kyau da zaka ga screen yayi kyau kana kallo kamar gaske in kana game kamar ka zaro mutum domin 2D da 3D sun fita yadda ya kamata. Kasancewarsa wani abu da yawanci masu game ne suka fi damuwa da shi amma mutane suna san ganin screen yayi kyau. Kana gane kyan graphics daga screen amma yadda karfin sa yake sai an sa application kamar Antutu benchmark ko CPU-z zasu gayama kyan graphics din wayarka. Ana auna shi a pixels.

CAMERA

kasancewar muna zamanin da photo yazama wani abu mai matukar amfani yasa camera a waya mai kyau take dadawa waya mutunci. Kasancewar abune mai sauki wajan gane karfin camera domin ana rubutawa a bayan waya kasan camera din ya karfinta yake ko da babu zaka iya dubawa in ka Shiga Camera> settings> picture size. Zaka ga kafin camera yawanci Yana farawa daga 5MP wato mega pixels zuwa 13MP Wanda yanzu shi yafi kowanne karfi.

OPERATING SYSTEM (OS)

Kasancewar kullum ana kara gyara Android operating system shiyasa kasamu babba zai kara bayyana me waya zata iya akwai application da zaka ga in os dinka yayi kasa da 4.0 baya dauka. Misali Emoji smiles basayi har sai OS dinka yakai 4.4  wato KitKat shi yasa ka samu sabo shi zaifi, zaka iya duba Wana irin operating system ne a waya in ka Shiga settings>  about tablet/phone >  Android version. Zaka danna Android version sau uku da sauri Dan ya nuna Maka sunan OS din.

Sunan Android Operation system

Android donuts 1.6
Android Eclair 2.0
Android Froyo 2.2
Android Ginger Bread 2.3
Android Honey Comb 3.0 na tablets ne kawai
Android ice cream  sandwich 4.0
Android Jelly Beans 4.1- 4.3
Android KitKat 4.4
Android Lollipop 5.0

Internal Storage

Internal storage shine iya adadin GB da waya take dauke da shi Ba tare da kasa memory card bawayoyin sukan zo da wani wae da zaka sa photo, Waka da videos a cikin wayarka. Domin wasu basu cika san amfani da memory Ba shi yasa sunfi san amfani da waya mai babban internal storage yawanci Yana farawa daga 2GB zuwa 32GB wasu wayoyin har 64GB, 128GB. Zaka iya duba adadin  internal storage in ka Shiga settings> storage.

Yadda ake rooting na android

Kafin Kasan ya ake rooting, ya kamata kasan  menene rooting kaji ana cewa nayi rooting ko zan rooting kai ma kake sanyi? Ko kuwa kaga ana maganrsa a dandalin internet ne ? Rooting wata hanyace ta karawa wayoyi ko tablet din android karfin aiki wato ka samu damar sa wasu application da Suke San suga an Samar da wani Abu da ake cewa super user binary ana sashi da alamu #superuser ko #superSU wannan hanya Tana sa guarantee da kamfanonin wayar suke ya wargatse har takansa waya lalacewa Amma amfaninta yafi hatsarinta yawa. In ba a bI hanyar yi dai-dai ba amma in anbi hanyoyin za aji dadin aikin.

Mene rooting?
Rooting kamar jailbreak ne a iPhone ga Wanda yayi amfani da wayar iPhone a da kuma Yana Ba masu amfani da waya damar chanja waya ainihin kwakwalwarta, hasali ma Yana bada damar chanja komai na waya zuwa yadda ake so. Da rooting zaka tsallake duk wani shinge da kamfanin da suka kera wayarka suka Sama Dan ragewa wayarka dadin amfani. Zaka sa applications masu matukar yawa da amfani,rage ko kara saurin wayar kai hatta da shi android din zaka iya sa sabon da Google suka Saki ko kamaYar da shi karami Wanda kake so ma'ana kana da yanci akan wayarka.

Saboda me Zakai rooting?

Abinda yake sawa ana rooting shine Google sun fito da sabon Android wato an kara wasu abubuwa kai kuma wayarka basu da wannan kana San sawa wayarka Amma kamfanin bai fitar Ba Sai wasu da ake kira developers ne sukai kamar irinsu CyanogenMod wadan da ake kira da Flash ROMs, Ko kuma an samo wata hanya ta saukaka browsing ance Sai anyi rooting kai Kuma wayarka babu. Irinsu browsing da MTN da subscription din blackberry ko na Glo.SU kuma applications sin ance Sai anyi rooting. Amma akwai applications da suke da dadi sosai da zasu sa kai rooting irinsu titanium Wanda zaka ajiye wayarka a memory dinka da sauransu.

Saboda me zaka ki yin rooting?

Abu biyu da zasu saka ka Ki rooting shine ka cire guarantee din wayarka ko kuma ka lalata wayarka a hanyar yi
Cire guarantee kamfanoni suna cewa in kai rooting ka cire  guarantee da suka saka Saboda duk wani shinge da suka saka ka tsallake shi Amma ka Sani in ka bukaci cire rooting zaka iya cirewa duk sanda ka so. Kaga wannan Ba matsala Ba ne.
Lalata waya. A kan samu tsautsayin lalacewar waya yayin rooting Amma Sai in Ba abi hanyar yin rooting din Dai Dai Ba in kabi hanya Dai Dai zakai cikin Nasara ka Gama Ba matsala Dan haka ka tabbata oa Bi hanyar da ta dace.

Abinda zakai kan kayi rooting.
Ana bukatar ka samu charge yakai a kalla kaso saba'in a cikin wayarka sannan ka tabbata kaje settings> developers options> USB debugging ka saka shi Kafin kai komai.

Yadda ake rooting.

Ana rooting ta hanyoyi guda biyu wato ta hanyar amfani da naura mai kwakwalwa da kuma hanyar da Ba amfani da naura mai kwakwalwa. Akwai applications guda biyu da suna da karfi da kyau wajan rooting Ba tare da computer Ba wato Ba na'ura mai kwakwalwa.
Framaroot da Towelroot Sai a computer akwai vroot da kingo root.

Towelroot

Hanya mai sauki da zakai rooting din wayarka ta android ahine towelroot zaka iya samun application din  a nanAmma Sai kaje settings>security>unknown source ka zaba sannan zai Shiga kamar Daya daga cikin application na wayrka Sai ka Shiga ka danna madanni Daya dake jikin fuskar application din zai kashe wayar yasake kunnanta Bayan ya Gama.



Framaroot

Kusan ko wace waya Framaroot na iya rooting dinta Ba tare da wahala Ba Sai Dai Yana da hanyoyi guda uku Wanda duk amfaninsu  daya Kawai in wani baimaka Ba Sai ka sake gwada wani akwai Barahin, Boromir da Faramir duk zasuyi Maka rooting sannan zai Baka sakon nasara sannan Sai ya tambayeka ka sake kunna wayarka Sai ka akshe ka kunna kasa rooting.
Hanya ta biyu wato amfani da computer Amma ita ma akwai hanya biyu akwai masuyin rooting babu internet akwai kuma wadanda Sai da internet kamar VRoot nayi babu internet Sai Kingo root da internet.

Vroot
Da farko zakai downloading vroot a internet Sai kasa ta cikin computer Bayan ka Gama ka kunna ta Sai ka jona wayarka da USB cable zata fara checking har zuwa tasa Maka sunan wayarka da model dinta, sannan zai Baka madannin root Sai ka JIRA zuwa ya Gama ya Baka sakon Nasara. Zai sake kashe wayar sannan zata kama da kanta ka samu rooting Kenan.

Kingo root
Bayan kayi download din application din kingo root Sai ka kunna internet dinka a computer taka ka jona wayarka zuwa computer Sai ka Jira har Sai wayarka ta ganu a jikin computer sannan Sai ka dannan madannin root dake jiki zai yi zuwa ya Gama.

Bayan kayi Daya daga cikin wadannan hanyoyi akwai hanya da ake gane aiki yayi ko bebe Dan wani lokacin basa saka superSU application a waya Sai kai download dinsa daga playstore zaka saka root checker a wayarka zata gayama kayi rooting ko bakai ba.

Amma duk da amfani da wannan rooting yake bayarwa wani lokacin akan so a cire shi to uanyar cirewa shine kaje cikin superSU dinka ka danna madannin remove root zai fita.

Monday, 3 June 2019

*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramdaniyyat (1440H)

               *[1]*
Alakar Alkur'ani Da Watan Ramadan

1. Saukar da Alkur'ani a cikin watan Alkur'ani har sau biyu, watau saukarwa ta farko zuwa saman duniya ta kusa a Baitul Izza da sauka ta biyu zuwa ga Annabi SAW yayin da yake kebanta da kansa a kogon Hira, wannan duka yana nuna kakkarfar alakar dake tsakanin wannan wata mai albarka da Alkur'ani mai girma.

2. Manzon Allah (SAW) ya kasance yakan hadu da Mala'ika Jibrilu a duk shekara a watan Ramadana suna bitar Alkur'ani. A shekararsa ta karshe a duniya sun hadu sau biyu sun yi bitar Alkur'ani. Wannan yana kara tabbatar da kakkarfar alakar wannan watan da wannan babban littafin watau Alkur'ani.

3. Annabi (SAW) ya kwadaitar da al'ummarsa a kan tsayuwar dare don raya kwanakin wannan wata mai alfarma, ya yi musu albishir din gafarar zunubansu da suka gabata idan su aikata haka. Ya zamanto yana kara kaimi wajen ibadarsa da tsayuwarsa ta dare, yana tashin iyalansa daga barchi don su yi koyi da shi yayin da goman karshe ta shiga ta wannan watan. Duk wannan wani babban dalili ne mai tabbatar da karfin alakar watan Ramadan da wannan muhimmin littafin a rayuwar Musulmi watau Alkur'ani.

4. Musulmi a ko'ina a fadin duniya suna tashi tsaye don karfafa dangantakarsu da wannan littafi ta wajen karanta shi da karantar da shi da tuntuntuni cikin ayoyinsa ya yada koyarwarsa a birni da kauye ta hanyoyi daban-daban wadanda suka hada da karantar da shi a masallatai da majalisan ilimi da makarantu da daukar nayin yada karatunsa da tafsirinsa a kafofin sadawarwa daban-daban wadanda suka hada da Radiyo da Talabijin da hanyoyin sadawarwa na yanar gizo-gizo (internet) da sauransu.

5. Madalla da duk wanda ya tsinci kansa cikin wannan aiki na alheri da raya sunnar Mazon Allah (SAW). Allah muke fata ya karbi ayyukanmu nagari ya yafe mana kurakuranmu ya sanya mu cikin 'yantattu a wannan watan. Amin.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[2]*

Kaurace Wa Alkur'ani: Kashe-Kashensa Da Matakansu:
1. Allah (SWT) yana cewa:
(Manzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riki wannan Alkur’ani abin kaurace wa.”).
2. A wannan ayar Allah (SWT) ya bayyana yadda Manzon Allah (SAW) yake ta kokawa game da halayyar kafirai wadanda suke bijire wa Alkur’ani da ya zo yana karanta musu suka rika yi masa izgili da ta’annuti iri-iri, duk da cewa wajibi ne a kansu su yi imani da shi su mika wuya a gare shi.
Akwai matakai guda hudu na kaurace wa Alkur'ani:
Na farko, shi ne bijire masa da kafirce masa, kamar yadda kafirai suka rika nuna wa lokacin da Manzon Allah (SAW) yake karanta musu ayoyisa, har suka rika yi masa izgili suna sifanta shi da munanan siffofi don su sa mutane su guje shi, suka rika cewa tsafi ne ko waka ce ko su ce bokanci ne da dabo.
Na biyu, kaurace wa karatunsa da tilawarsa. Wajibi ne a kan kowane Musulmi ya zamanto mai karanta Alkur'ani lokaci bayan lokaci tare da kokarin haddace abin da ya sauwaka daga cikinsa ayoyinsa. Zunubi ne babba ga Musulmi ya yi watsi da karatun Alkura'ni gaba daya saboda bijirewa. Kamar yadda yawancin malamai suka bayyana cewa sakaci wajen barin karatunsa shi ma laifi ne koda kuwa babu bijire wa a ciki.
Na uku, kaurace wa tuntuntuni game da ma'anoninsa da kokarin fahimtar hukunce-hukuncesa. Domin babbar manufar da ta sa Allah ya saukar da shi ita ce saboda a fahimci ma'anoninsa a yi aiki da karantarwarsa. Don haka masu kiraye-kirayen cewa a daina taimaka wa wajen yada tafsirin Alkur'ani a kafofi watsa labarai a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan suna kira ne zuwa ga kaurace wa fahimatar da mutane karantarwar Alkur'ani da kusanto musu da ma'anoninsa domin aiki da shi.
Na hudu, kaurace wa aiki da hukunce-hukuncesa da watsi da shari'arsa da rashin zartar da umarninsa da haninsa. Kamar yadda wasu shugabannin Musulmi suke yakar kafa shari'ar Musuluci cikin al'umma suke nuna gabarsu a fili game da duk wani yunkuri na tabbatar da haka. Wannan shi ma nau'i ne na kaurace wa Alkur'ani wanda Allah ya ba mu labarin cewa Mazonsa ya koka game da faruwarsa a cikin al'ummarsa.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[3]*

*Karatun Alkur'ani (1)*

1. An shar'anta karanta Alkur'ani ga wanda ya haddace shi da ma wanda bai haddace shi ba. An fi saurin manta Alkur'ani fiye da kowane zance da za a haddace. Allah ya yi wa Alkur'ani wasu abubuwa guda biyu:
Na farko, Allah ya kaddara haddarsa ta fi haddace kowane zance sauki ga duk wani mai kykkyawar niyya da manufa.
Na biyu, An fi saurin mance shi fiye da kowane zance da mutum kan haddace.

2. Duk wanda ya rungumi karatun Alkur'ni to cikin gaggawa zai yi katarin samun sa. Hakanan kuma duk wanda ya yi sakaci da karatunsa, to cikin dan kankanin lokaci zai rasa shi.

3. An karbo daga Abdullahi dan Mas'ud (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: "Tir da wanda zai rika cewa: 'na manta aya kaza da kaza', sai dai ya ce an mantar da shi. Ku rika bitar Alkur'ani domin ya fi saurin kubucewa daga zukatan mazaje fiye da rakuma daga dabaibayinsu". [Bukhari#5032 da Muslim#790].

4. Gwargwadon yadda mutum zai rika bijire wa aiki da karantarwar Alkur'ani, to hakanan shi ma Alkur'ani zai rika kubuce masa.
Malam Dhahhak yana cewa: "Babu mutumin da zai karanci Alkur'ani sannan ya manta shi sai saboda wani zunubi da ya aikata". Sannna sai ya karanta fadar Allah da yake cewa: (Abin da kuma ya same ku na wata masifa to saboda abin da hannayenku suka aikata ne). [Shura, aya ta 30]. Sai kuma Dhahhak ya ce: "To shin akwai musibar da ta kai mance Alkur'ani?!". [Ibn Abi Shaiba#29996].
5. Yana da kyau mutum ya rika sauraron karatun Alkur'ani daga wani makaranci, domin kunnuwansa ma suna da hakki a kansa kamar sauran gabobinsa. Annabi (SAW) ya saurari karatun Alkur'ani daga Abdullahi dan Mas'ud (RA). [Dubi, Bukhari#5055 da Muslim#800].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) [4]

*Karatun Alkur'ani (2)*

1. Ma fi karancin lokacin da ake son a yi saukar Alkura'ni a cikinsa shi ne a yi a ckin kwanaki uku.
An ruwaito cewa an hana sauke shi a cikin kasa da kwana uku, domin kada a kasa fahimtar ma'anoninsa. [Dubi, Ahmad# da Abu Dawud#1394].

2. Galibi wanda zai yi saukar Alkur'ani a cikin kasa da kwana uku to ba zai iya samun damar fahimatar ma'anoninsa yadda ya kamata ba, domin yawancin magabata na kwarai duk da zurfin fahimtarsu da kaifin kwakwalwarsu ba su yarda su yi saukar Alkura'ni a cikin kasa da kwana uku ba don gudun kasa su kasa samun cikakkiyar fahimtarsa, to ballanata kuma mu a yau.

3. Mutum yakan samu khushu'i daga sauraron sautin karatun Alkur'ani yayin da ake karanta shi amma wannan khushu'in ba zai dade ba zai neme shi ya rasa bayan ya gama sauraronsa. Amma wanda ya sami fahimatar ma'anonin abin da yake karantawa, to khushu'in da zai samu yakan wanzu tare da shi, ya kuma yi masa tasiri a zuciya. Samun haka kuwa ba zai yi wu ba sai idan an karanta shi cikin natsuwa da bin haruffansa daki-daki. Ya inganta daga Abdullahi dan Mas'ud yana cewa: "Ku yi saukar Alkura'ni cikin mako daya, kada ku yi saukar sa a kasa da mako". [Sa'id bn Mansur, Tafsir#146]. Don haka ne Mu'azu dan Jabal (RA) yake ganin makruhi ne ya sauka a cikin kasa da mako daya. [Dubi, Abu Ubaid, Fadha'ilul Kur'an, shafi 180].

4. Wasu daga cikin magabata sun amince da a yi sauka a kasa daga kwana uku, wasu ma daga cikinsu sun rika yin haka, kamar Sayyidina Usman da Tamimud Dari da Sai'du dan Jubair da Mujahid da Imamus Shafi'i da Abu Hanifa. Wadannan duka sun kasance suna yin sauka a kullum. [Dubi, Al-Marwazi, shafi 157].
Sa'idu Ibn Musayyab shi kuma yakan yi sauka a duk darare biyu. Hakanan shi ma Al-Aswad dan Yazidu yake yi a cikin watan Ramadan. [Dubi, Al-Marwazi, shafi na 157 da Ibn Sa'ad, Juzu'i na 6, shafi na 73].
5. Amma abin da ya fi falala shi ne rashin sauke Alkur'ani a cikin kasa da kwana uku, sai dai a lokuta masu falala kamar goman karshe na watan Ramadan.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[5]*

*Mance Haddar Alkura'ni*

1. Babu shakka duk wanda ya manta Alkurani saboda bijire masa da watsi da shi, to ya tabbata mai laifi ne a wurin Allah. Malamai ba su yi sabani a kan haka ba.

2. Hakanan wanda ya manta wani abu da ya haddace na Alkur'ani saboda tsufa ko rashin lafiya ko wata musiba da ta same shi, wannan ba shi da wani laifi da za a kama shi da shi.

3. Ibn Rushd Al-Maliki ya kawo ijma'in malamai a kan cewa mutumin da ya manta abin da ya haddace na Alkur'ani saboda shagaltarsa da wani lilimi na wajibi ko na mustahabbi bai zama mai laifi ba. [Dubi, Masa'ilu Ibn Rushd, shafi na 691].

4. Malamai sun kasu gida biyu game da wanda kasala da sakaci suka sanya shi ya mance abin da ya haddace na Alkurani:
Kaso na farko, suka ce, duk wanda ya yi haka to shi mai zunubi ne a wurin Allah. Wanna shi ne ra'ayin Ibn Taimiyya, kuma shi ne mazhabar Shafi'iyya. Al-Rafi'i da Ibn Hajar Al-Haitami daga cikin malaman Shafi'iyya sun lassafa haka daga cikin manyan zunubai. [Dubi, Al-Haitami, Azawajir, juzu'i na 1, shafi na 200-201].
An ruwaito hadisai da yawa dake nuna mummunan sakamakon wanda ya haddace Alkur'ani sannan ya manta, sai dai dukansu hadisai wadanda ba su tabbata ba. [Dubi, Abu Dawud#461, 1474 da Tirmizi#2916].
Amma dai yawancin magabata sun kasance suna tsanantawa game sakaci wajen manta haddar Alkur'ani.
Kaso na biyu, suka ce, ba kyau mutum ya manta abin da ya haddace na Alkur'ani, amma ba zama mai zunibi ba a kan haka sai dai idan ya yi daina aiki da shi ne ya kaurace masa. Daga cikin masu wannan ra'ayi akwai Sufyanu bn Uyaina da Abu Yusuf almajirin Abu Hanifa.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[6]*

*Shawara A Rayuwar Musulmi*

Allah Ta'ala yana cewa:-

*"Da kuma wadanda suka amsa kiran Ubangijinsu suka kuma tsai da salla, al'amarinsu kuwa (suna) shawara ne a tsakaninsu, suna kuma ciyarwa daga abin da muka arzuta su".* [As-Shura, aya ta 38].

1. A wanan ayar Allah ya bayyana muhimmancin shawara a kan muhimman al’amura na addini da rayuwa.

2. Gwama batun salla tare da na shawara a wuri daya ya nuna cewa duk mai kula da sallarsa yadda ya dace shi ne ya kamata ya zama abokin shawara, domin kuwa shi ne Allah zai tsare shi daga son zuciya da rashin nutsuwa.

3. Yin shawara sananniyar al’ada ce a wurin mutanen Madina, duk sanda wani muhimmin abu ya taso sukan hadu su yi shawara a junansu. Ta hanyar shawara ne suka kai ga cim ma matsayar yin imani da kiran Manzon Allah (SAW) lokacin da wakilansu suka zo musu da labarin da’awarsa daga Makka.

4. Sahabban Annabi (SAW) sun kasance masu haduwa don gudanar da shawara cikin dukkan muhimman al’amuransu. Sun yi shawara lokacin shugabantar da sayyidina Abubakar bayan rasuwar Manzon Allah (SAW), kamar yadda suka yi shawara lokacin yakar masu ridda da sauran al’amura masu yawa. Manzon Allah (SAW) shi ne babban abin koyinsu a nan domin ya kasance mai neman shawararsu a kan abubuwa idan sun taso.

5. Duk abin da Allah da Manzonsa (SAW) suka riga suka yi hukunci a kansa, to babu sauran neman shawarar wani game da daukar wannan hukucin ko rashi daukarsa, kamar yadda Allah ya bayyana cikin Suratul Ahzab, aya ta 36. Sai dai idan al'amari ne da Allah ya bar lokacinsa da mahallinsa a bude, to wannan ana iya yin shawara domin zabar sanda ya dace da inda ya dace a aiwatar da shi, kamar sha'anin Jihadi da sulhu da makamantansu.

6. Neman shawara sunna ce a kan duk wani abu da Allah bai riga ya yi hukunci a kansa ba, kamar al'amuran da suka shafi maslahar al'umma da ta kasa da ta dukiya da tsare-tsaren gudanar da rayuwa ta yau da gobe.

7. Idan Shugaba ya kawo shawara a gaban Musulmi, sai suka hadu a kan ba shi shawara iri daya, to bai halatta ya saba musu ba, domin hakan zai iya jefa al'umma cikin fitina da rarrabuwar kai.

8. Amma idan suka saba a kan lamarin, to idan ya zamanto shi shugaba ne mai ilimi ya kuma san yadda zai dubi al'amarin da iliminsa har ya fita da kyakkyawan ra'ayi, to ya halatta ya saba musu.

9. Amma idan ba mai ilimi ne ba, ko bai san komai game da abin da ya nemi shawara a kai ba, to bai halatta ya saba musu ba, domin idan ya ce zai saba a nan to son zuciya ne zai shigo ciki ba ilimi ba. Allah kuwa ya yi umarni ne da a mayar da al'amari zuwa ga masanansa, domin su ne za su iya tantance abin da ya dace, kamar yadda ya zo a cikin Suratun Nisa'i aya ta 83.

*Allah ya sa mu dace. Amin.*
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[7]*

*Umara A Ramadan Da Umara A Watannin Hajji*

1. Umara a cikin watan Ramadan tana da gwaggaban lada kamar yadda ya zo a cikin hadisi. [Dubi, Bukhari#1782 da Muslim#1256].

2. Annabi (SAW) ya yi umara hudu a rayuwarsa, dukkansu a cikin watan Zul-Kida, wato daya daga cikin watanni hajji, wato watanni masu alfarma. Wannan dalili ne da yake nuna cewa umara a watannin hajji ta fi falala a kan yin ta a watan Ramadana.

3. Hadisin da ya zo da cewa: "Umara a watan Ramadana tana daidai da hajji" yana bayanin falalarta ne ba fifikonta ba.

4. Maimaituwar Umarar Manzon Allah (SAW) a daya daga cikin watannin hajji har sai hudu dalili ne da yake nuna ya yi hakan ne da manufa ba kawai dace ne aka samu ba. Aikin da aka yi ta maimaita shi ya fi wanda kawai kwadaitarwa aka yi a kansa da baki ba tare da samuwar aiki ba.

5. Magabata sun fi yin umararsu a watannin hajji har hakan ya sa Umar (RA) ya rika umartar su da suka rika yin ta a sauran watannin domin kada a samu wasu lokuta da Harami zai kasance babu jama'a a cikinsa.
Ramadaniyyat (1440H) *[8]*

*Dr  Sani Umar R/lemo*

*Babbar Magana: Ranar Lahira*
Allah yana cewa:-
*(Ya ku wadanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kowane rai ya dubi abin da ya aikata domin gobe (lahira)…) [Al-Hashri, aya ta 18].*

1. Mutuwa ba ita ce karshe ba. Mutuwa mafarin wata rayuwa ce mai tsawon gaske, mai ciki da dadi ko wahala, mai kunshe da farin ciki ko bakin ciki. Duk mai kokwanto game da rayuwar lahira mahaukaci ne ba mai hankali ba.

2. Rayuwarmu a nan duniya tana cike da zalunci da ta'addanci da rashin gaskiya da miyagun ayyuka. An mayar da karya ita ce mafita, yaudara kuma ita ce wayo, munafurci kuma ya zama wayewa.

3. A rayuwarmu a yau muna ganin ana hukunta marar laifi a kyale masu laifuka, ana kuma wulakanta mai mutunci sannan a karrama fitsararre. Don haka idan har mun yarda da cewa Allah adalin Sarki ne, to babu makawa dole ne mu yi imani da samuwar wata rayuwa bayan wannan ta duniya da muke ciki, watau rayuwa wadda a cikinta ne Allah zai mayar wa kowane mai hakki hakkinsa, ya hukunta duk wani mai laifi gwargwadon laifinsa. Duk wani mai hankali da ya san ya kamata dole ne ya yarda da haka.

4. Yarda da lahira da imani da sakamakon cikinta ne kadai zai hana wa dan'adam zaluntar dan'uwansa, zai kuma kara wa mutumin kirki kwarin gwiwar aikata ayyukan alheri, domin yana da tabbacin cewa zai ga kyakkyawan sakamakon aikinsa.

5. Ashe bai kyautu mu ci gaba da tunatar da junanmu wannan babbar maganar ba?
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[9]*

*Hikimar Imani Da Kaddara*

1. Ibnul Jauzi ya ba da labari cewa: Wata rana wani mutum ya fadi ya suma, sai mutane suka zaci cewa rai ya yi halinsa. Sai nan da nan aka nemo mai wankan gawa, aka dora shi a kan abin wanka. Zuba wa mutumin nan ruwan sanyi ke da wuya sai ya yi zumbur ya tashi tsaye, daga nan sai shi kuma mai wankan gawa ya firgita saboda tsananin tsoro ya fadi ya mutu nan take.

2. Wannan yana tabbatar da cewa komai kaddara ce. Don haka ka ci gaba da kokarinka a kan gaskiya da jajirce mata, kada tsoron mutuwa ya hana ka riko da ita da tsayawa a kanta. Ajalin kowa a lissafe yake a wurin Allah. Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.

3. Ka yi aikinka domin rayuwarka ta duniya kamar ba za ka mutu ba har abada, ka kuma nemi lahirarka kamar gobe ne ranar mutuwarka.

4. Imani da kaddara shi ne rayuwa, shi ne zai zamo maka haske yayin da ka shiga cikin duhu. Da shi ne za ka rika hango mafita yayin da kake fuskantar wani tsanani.

5. Imani da kaddara shi ne abin da yake kwantar wa da bawa hankali, ya dawo masa da nutsuwarsa cikin kankanin lokaci. Idan ka rasa da daya, to ka dubi wani shi 'ya'ya biyu ya rasa, sai ka gode wa Allah. Idan ka yi asarar dubu daya, to ka dubi wanda ya yi hasarar dubu biyu, sai ka gode wa Allah. Da wannan ne za ka fahimci sirrin imani da kaddara.

6. Don haka mu aikata aikin alheri tukuru, kada mu samu damuwa don mun kasa cin nasarar abin da muka sa a gaba. Kada kuma mu fitar da kauna don mun ga tafiyarmu tana kara tsawo ba tare da mun cimma inda muka nufa ba.

7. Mu kasance tare da 'Kaddara' koyaushe kamar mutumin da ya zo tsallaka hanya mai cike da zurga-zurgar ababan hawa, idan zai rika tuna hatsurran ababan hawa, to har abada ba zai tsallaka wannan hanya ba. Hakanan idan zuciyarsa ta fada masa cewa zai iya tunkarar wadannan ababan hawa ya ture su wuri guda ya wuce abinsa, to ba zai kai labari ba. Amma idan ya nutsu ya ketare hanyarsa cikin taka-tsantsan, to wannan shi ne mai hankali. Sannan idan ya ketare lafiya sai ya yi wa Allah godiya, idan kuma wani abin ki ne ya faru da shi, to zai tuna cewa ba sakacinsa ba ne, hukunci ne kawai na kaddara. Allah yana cewa: (Lalle Mu Mun halicci komai da kaddara). [Suratul Kamar, aya ta 49].
Dubi, Ali At-Tantawi, Suwarun Wa Khawatir, shafi na 125-126.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[10]*

*Gajeruwar Hanyar Rushe Musulunci*

1. Mafi gajartar hanyar rushe addinin a jiya da yau ita ce rushe kima da darajar masu karantar da shi a idanun al'umma.

2. Tun da jimawa makiya Musulunci suka fahimci wannan. Don haka suka yi uwa da makarbiya wajen sukan masu dauke da karantarwar addinin Musulunci, kamar sahabbai da tabi'ai da manyan malamai, domin cim ma mummunar manufarsu.

3. Imamu Ahmad bn Hanbal yana cewa: "Idan ka ga mutum yana sukan sahabban Manzon Allah (SAW), to ka tuhumce shi da kin Musulunci". [Ibn Kasir, Al-Bidaya, juzu'i na 11, shafi 450].

4. Wannan dalili ne ya sanya makiya Musulunci suka rika sukan sahabbai, kamar Abu Huraira da Nana A'isha, domin rushe tarin ilimin da suka karbo daga Manzon Allah (SAW). Suke kuma sukan malaman tabi'ai, irin su Muhammad bn Shihab Az-Zuhri, domin lalata dimbin hadisan da ya ruwaito daga sahabbai.

5. A kullum masu kin su ga ci gaban addinin Musulunci fatansu shi ne su sami abin da za soki wani wanda ya yi fice cikin al'umma wajen yada karantarwar Musulunci domin su cire ganin kimarsa da mutuncin daga zukatan al'umma, su kuma haramta musu sauraron karantarwarsa da karuwa da fadakarwarsa.

6. Don haka duk masu kokarin bata sunan malamai su sani ba shi karankansa malamin suke kokarin rushewa ba, a'a suna sa'ayi ne don ganin sun rushe da'awarsa da karantarwarsa wadda gado ne na Annabi (SAW) a hannunsa. *Allah ya ganar da mu. Amin.....*
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[11]*

*Sukan Malaman Sunna: Hassada Ga Mai Rabo Taki Ce*

1. Sukan malamai magada annabawa masu karantar da mutane addinin Allah wani mugun abu ne da ya dade a cikin al'umma, kuma salo ne na wasu masu miyagun akidu da bidi'o'i da suke da damuwa game da rawar da malamai suke takawa wajen bayyana wa mutanen munin akidunsu. Hakanan mutane masu dauke da cutar hassada a zukatansu sukan damu da ganin karbuwa da wani malami ya samu a wurin al'umma da tasirin da kalmarsa take da shi a tsakaninsu, don haka suke ganin cewa su fa zakaransu ba zai taba yin cara ba har sai ta hanyar sukan malamai da tuhumarsu da yi musu karerayi.

2. Daga cikin labaran da tarihi ya tabbatar mana na irin wadannan mutane akwai abin da ya faru da babban malamin sunnar nan, wato Abu Umar Ahmad bn Muhammad at-Talamanki Al-Maliki (ya rasu shekara ta 429H).

3. Ya kasance babban malami ne masanin Alkur'ani da hadisi da ilimin fikihu. Ya yi rubuce-rubuce da dama a fannonin ilimi masu yawa. Ya yi sanadiyyar shigar da ilimi mai yawa cikin yankin kasar Andalus, kuma mutum ne mai matukar kishin Shari'a da Sunna.

4. A shekara ta 425 ne aka samu wasu gungun 'malamai' wadanda suka shirya taro a gidan daya daga cikinsu, inda suka zauna suka rubuta tuhumar karya a kansa cewa, wai yana da akidar 'Khawarijawa' watau akidar masu fito-na-fito da masu mulki ta hanyar amfani da karfi da kuma kafirta musulmi masu aikata kaba'ira.

5. Wannan tuhuma ita ce ta sa har aka gurfanar da Imam Abu Umar gaban Alkali Muhammad Fartun, aka kuma samu mutane goma sha biyar wadanda suka ba da shaidar zur a kan tabbatar da wannan tuhuma da ake yi masa. To amma daga bisani bayan alkali ya yi bincike sai ya gane cewa wannan tuhumar da ake yi Imam Abu Umar tuhumar banza ce babu kanshin gaskiya ko kadan a cikinta, don haka sai ya sallame shi, ya kuma rubuta masa takardar wanke shi daga wannan zargi ya danka masa a hannunsa.

6. Tun daga lokacin Allah ya ci gaba da daukaka sunan wannan malami, ya kuma ci gaba da raya iliminsa cikin al'umma tsawon zamani har zuwa yau kimanin shekara dubu ke nan. Su kuma wadanda suka so rusa shi sai Allah ya rusa kadararsu, a yau ba wanda aka san ko da sunansa daga cikinsu ballanta a ambaci alherinsa a yi masa kyakkyawar addu'a. Ashe yanzu wannan bai isa izina ba?
[Dubi, Ibnul Abbar, At-Takmilah, juzu'i na 1 shafi na273, da Az-Zahabi, Siyarun Nubala' juzu'i na 17, shafi na 568].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[12]*

*Al-Imam Ibn Abi Zaid Al-Kairawani Da Sufayen Zamaninsa*

1. Kamar yadda Allah (SWT) ya ba wa annabawa mu'ujizoji domin tabbatar da gaskiyar annabcinsu, hakanan yake gudanar da wasu karamomi a hannun wasu bayinsa nagari, domin nuna girman matsayinsu a wurinsa da taimaka musu a kan wani lamari da ya shafi addaninsu ko rayuwarsu.

2. Ahlusunna duka sun yi imani da karamomin waliyyan Allah, saboda abu ne da ya tabbata a Alkur'ani da hadisan Manzon Allah (SAW) masu yawa. Babu mai ja a kan haka sai mabiya ilimin Falsafar Girikawa da Mu'utazilawa da wasu daga cikin Ash'ariyya.

3. Sukan wani babban malamin Sunna da tuhumarsa da cewa bai yarda da karamar waliyyan Allah ba suka ne ga ingancin akidarsa ta Sunna. Wannan kuma shi ne abin da ya faru ga babban malamin nan na fikihun Mazhabar Malikiyya, watau Abu Muhammad Abdullah dan Abu Zaid Al-Kairawani marubucin lilttafin 'Risala' shahararren littafin fikihun nan a kasar Hausa da sauran duniyar Musulmi.

4. Yadda al'amarin ya faru kuwa shi ne, akwai wani malami mai da'awar Sufanci ana kiransa da suna Abdurrahim As-Sikilli. Shi wannan wani mutum ne mai nuna walittaka, yana kuma da'awar yana da wasu karamomi, wanda hakan ya kai shi ga da'awar ganin Allah ido-da-ido a matsayin karama, aka kuma samu wasu suka fara gaskata shi.

5. Ganin yadda wannan mutum ya fara wuce iyaka da zurmewa cikin bata ya sanya Imam Ibn Abi Zaid Al-Kairawani ya rubuta littattafai biyu don yi masa martani, na farko mai suna "Kitabul Kashf". Na biyu kuma "Kitabul Istizhar" inda ya bayyana karyar waccan da'awar ta wancan sufin malami.

6. Bayyanar wadannan littafai guda biyu ke da wuya sai magoya bayan wannan malami daga cikin sufaye da wasu masu danganta kansu da ilimin hadisi, suka shiga sukan Imam Ibn Abi Zaid da tuhumar sa da cewa yana karyata karamar waliyyai bai yarda da ita ba. Suka rubuta takarda zuwa ga shehin malamin nan na kasar Bagadaza a lokacin watau Abubakar Al-Bakillani, suna bukatar ya fadi wani abu game da wannan lamari. Al-Bakillani ya rubuta littafinsa mai suna "Al-Fark bainal Mu'ujizat Wa Karamatil Auliya'.." idan ya tabbatar da gaskiyar Karamar waliyyai, ya kuma wanke Ibn Abi Zaid daga zargin da ake yi masa, ya nuna cewa Ibn Abi Zaid ba yana inkarin karamomi ba ne, yana sukan masu wuce gona da iri ne wajen da'awar karamar karya irin su Aburrahim As-Sikilli.

7. Wannan bayani na Al-Bakillani shi ne ya rufe bakin duk wani mai sukan Ibn Abi Zaid, hakar 'yan bid'a na ganin sun rusa kadarinsa ta kasa cim ma ruwa, Allah ya ci gaba da yada hasken iliminsa har yau har gobe insha Allah.
[Dubi, Alkadhi Iyadh, Tartibul Madarik, juzu'i na 4, shafi na 492-497, da Wansharisi, Al-Mi'iyarul Mu'urib, juzu'i na 2, shafi na 392].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H): *[13]*

*Yada Alfasha A Cikin Al'umma*

1. Allah (SAW) ya ce:
(Lalle wadanda suke son yaduwar mummunan abu game da wadanda suka yi imani suna da (sakamakon) azaba mai radadi a duniya da lahira, kuma Allah (Shi) Yake da masaniya, ku kuma ba abin da kuka sani) [Suratun Nur, aya ta 19].

2. Wannan ayar ta kunshi bayanin haramcin yada barna a cikin muminai ko da kuwa ta hanyar baza labarinta ne, domin yin haka zai taimaka wajen tallata ta a zukatan masu raunin imani da lalata kyakkyawar zamantakewar al'umma da gurbata tarbiyyarsu.

3. Mai kuzuzuta labarin wasu miyagu halaye na jama'a ya fi laifi a wurin Allah fiye da wanda zai aikata su a boye, domin mai aikata laifi a boye yana yin abin da kansa kadai zai cutar ba zai cutar da wani ba. Amma wanda yake kuzuzuta labarin miyagun dabi'u cikin al'umma wannan laifi ne da zai cutar da dukkan daukacin al'umma, ba kawai zai takaita a kansa shi kadai ba ne.

4. Yada labarin mummunan abu da ke faruwa a cikin al'umma da terere da masu aikata shi haramun ne a Shari'a. Ya kuma zama haramun ne ba don yana labarin karya ba, a'a sai domin mummunan tasirin da yake yi na wargaje zamantakewa da rusa katangar kunya a cikin al'umma.

5. Babban malamin nan tabi'i Ada'u dan Rabah yana cewa: (Duk mai yayata alfasha, to ya cancanci mummun horo ko da kuwa gaskiya yake fadi). [Dubi, Ibn Abi Hatim, Tafsirinsa Juzu'i na 8, shafi 2550].

6. Wanda duk yake yada labaran miyagun laifuffukan da wasu suka aikata ko da kuwa ba ya kama sunan kowa, to yana aikin ruguza al'umma ne, domin kuwa yana koya wa masu karancin tarbiyya wannan laifin ne, yana kuma tunatar da wadanda suka manta da shi, sannan yana zaburar da wadanda suke fargabar aikatawa domin ya nuna musu cewa a kalla wannan laifin mai yiwu wa ne ga duk wanda ya sa kansa, domin ga misali a fili.

7. Wajibi ne a kan masu magana a kafofin watsa labarai (Rediyo da Talabijin da Yanar gizo-gizo) su guji wannan mummunan hali, su daina yada labaran ababan kunya da alfasha a cikin al'umma, musamman yayin da wasu suke gaban kutuna ana shari'arsu, idan kuwa sun ki, to su sani mummunan sakamakon da Allah ya ambata yana nan yana jiran su. Allah ya kiyaye mana imaninmu. Amin.

8. An karbo daga Sauban (RA) ya ce: Annabi (SAW) ya ce: “Kada ku cutar da bayin Allah, kada kuma ku kunyata su, kada ku bibiyi al’aurarsu, domin duk wanda ya bibiyi al’aurar dan’uwansa Musulmi, to shi ma Allah zai bibiyi al’aurarsa har cikin gidansa ya kunyata shi.” [Ahmad #22402].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*
Ramadaniyyat

 (1440H) *[14]*
*Saukin Kai A Rayuwar Manzon Allah (SAW)*

1. Manzon Allah (SAW) mutum ne mai matukar saukin kai da tawalu'u ga kowa. Babu wanda ya taba tuhumar sa da girman kai har ma daga cikin manyan makiyansa na farko wadanda suka yi ta neman hanyar da za su bata shi a idon duniya, amma duk da haka ba wani daga cikinsu da ya yi tsaurin ido ya tuhume shi da girman kai.

2. Manzon Allah (SAW) ya kasance lahira kadai yake hangowa da zuciyarsa, amma duniya sam ba ta gabansa, don haka ya kasance bawan Allah na gaskiya, mai saukin kai ga muminai. Yakan dade a tsaye tare da tsohuwa mai bukatar zantawa da shi. Yakan je ya dubo marar lafiya. Yakan kuma tausaya wa mai rauni, ya taimaka wa mabukaci. Yana wasa da kananan yara, yana tsokanar iyalansa, yana cin abinci tare da sahabbansa. Yakan zauna a kan dandamalin kasa, har ma yakan yi barci a kanta idan ya bukaci haka, ko kuma ya kwanta a kan kungurumin tabarma wadda babu shimfida a kanta. Shuhura da neman suna ba sa gabansa, tunaninsa koyaushe shi ne neman yardar Allah (SAW).

3. Yana cewa: "Ni bawa ne kawai, ina cin abinci kamar yadda bawa yake ci, ina zama kamar yadda bawa yake zama".[Al-Baghawi# 2839].

4. Yayin da wani ya gan shi sai kwarjininsa ya cika masa ido da zuciya, har jikinsa ya fara bari, sai Manzon Allah (SAW) ya shiga lallashinsa da kwantar masa da hankali, yana fada masa cewa: "Kwantar da hankalinka, ni dan wata mace ce a Makka da take cin kilishi". [Ibn Majah# 3312].

5. Ya ki jinin ya ji ana wuce iyaka wajen yabonsa, don haka yake tsawatarwa yana cewa: "Kada ku wuce iyaka wajen yabona, kamar yadda Nasara suka wuce iyaka wajen yabon dan Maryam, ni kawai bawan Allah ne, sai ku ce bawan Allah kuma manzonsa". [Bukhari#3445].

6. Bai yarda wani ya mike masa tsaye ko ya tsaya a bayansa yana zaune da sunan girmamawa ba. Duk sanda ya zo majalisa, to yakan zauna inda duk ya sami wurin zama. Idan yana cikin sahabbansa kuwa yakan saje da su har bako idan ya zo ba ya iya tantance shi a tsakaninsu.

7. Wannan digo ne daga tekun kyawawan halayen Manzon Allah (SAW) da saukin kansa, wadanda da su ne ya gagari duk makiyansa, da kuma su ne ya mamaye zukatan mabiyansa, har suka so shi suka kuma kaunace shi fiye da komai a rayuwarsu.

8. Mu kwatanta wasu daga cikin kyawawan halayensa a rayuwarmu, don mu ga irin girman tasirin da za su yi mana wajen samun nasara a komai na rayuwarmu.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[15]*

*Musulunci Cikakken Addini Ne* Allah yana cewa: (A yau na cika muku addininku, kuma na cika muku ni’imata, kuma na yardar muku Musulunci ya zamo shi ne addininku.) [Al-Ma'idah, aya ta 3].
Wannan aya ce da a ka saukar wa Manzon Allah (SAW) a ranar juma'a a filin Arfa a lokackin hajjinsa ta karshe. Wannan ayar ta tattaro abubuwa masu matukar muhimmanci a rayuwar Musulmi, domin tana dora su a kan mikakkiyar hanyar fahimatar addinin Musulunci. Cikin abubuwan da ayar ta kunsa akwai:

1. Addinin Musulunci ya cika tun lokacin da wannan ayar ta sauka. Duk abin da bai zama addini ba kafin saukar da wannan ayar, to ba zai taba zama addini ba bayan saukarta. Don haka duk wata bidi’a a addini bata ce, aiki da ita yana cin karo da wannan ayar. Shi ya sa Imamu Malik (RH) yake cewa: “Duk wanda ya kirkiri wani sabon abu a wannan addini, wanda magabatan wannan al’umma ba su san shi ba, to wannan yana ganin Annabi (SAW) ya ci amanar manzanci, domin Allah (SWT) yana cewa: “....A yau ne na cika muku addininku, kuma na cika muku ni’imata, kuma na yardar muku Musulunci ya zamo addininku.” To duk abin da ba zai zama addini a waccan rana ba, to a yau ma ba zai tava zama addini ba.” [Ibn Hazm, Al-Ihkam, juzu’i na 6, shafi na 58 da As-Shatibi, Al-I’itisam, juzu’i na daya shafi na 494].

2. Shari’ar Allah wani dunkulallen tsari ne wanda bai yiwuwa a yi masa gunduwa-gunduwa, a yarda da wani bangare, a yi watsi da wani; dole ne a yarda da shi a dunkulensa, musamman abin da ya shafi akida da ibada da mu’amala ta zamantakewar mutum da iyalinsa ko ta al’umma ko ta kasa da kasa. Duk wadannan abubuwa a dunkule su ake cewa ‘addini’, su ne kuma abin da Allah ya ce ya cika shi, kuma shi ne ni’imar da ya ce ya cika ta. Wadannan abubuwa a jumlace su ne tsarin rayuwa wadda Allah ya yarje wa muminai su rayu a kanta.

3. Musulunci shi ne mafi girman ni’imar da Allah (SWT) ya yi wa wannan al’umma. Duk wanda ya saki wannan addini na Musulunci, ko ya ki karbar sa, to ya haramta wa kansa rayuwa cikin ni’ima, ya zabi rayuwar musifa da wulakanci da kunci a duniya da lahira.
Dr. Muhd Sani Umar R/lemo
Ramadaniyyat (1440H) [16]
*Mafi Munin Butulci*
Allah Ta'ala yana cewa :-

1. (Shin ba ka ga wadanda suka musanya ni’imar Allah da kafirci ba, suka kuma jefa mutanensu gidan hallaka?) [Suratu Ibrahim, aya ta 28].

2. Babu shakka duk wanda ya karanta tarihin duniya tun kafuwarta zuwa yau zai tabbatar da cewa, Allah bai yi wa dan’adam wata gagarumar ni’ima wadda ta kai aiko da manzanni ga mutane ba.

3. Don haka babu wadanda suka cika butulu kamar wadanda suka bijire wa annabawa suka kuma karyata su.

4. Mafi girman ni’ima cikin dangogin wannan ni’imar ita ce ni’imar aiko da Manzon Allah Muhammadu (SAW), don haka babu mafi munin butulci kamar kafirce masa da watsi da karantarwarsa
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[19]*

*Sallar Juma'a Ga Matafiyi (2)*

1. Matafiyi yana iya bin sallar juma'a don ya samu falalar sauraron huduba, ya kuma rabauta da addu'ar Musulmi. Sai dai ba zai iya hada ta da sallar la'asar ba, domin sallar juma'a salla ce mai zaman kanta ba ita ce sallar azahar ba. Shi kuma hada salloli ana yin sa ne tsakanin Azahar da La'asar ko Magariba da Isha'i a lokacin daya daga cikinsu.

2. Idan matafiyi yana son hada sallar azahar da la'asar a ranar juma'a, to yana iya bin sallar juma'a da niyyar azahar, sannan sai ya hada ta da sallar la'asar, domin shi a wurinsa ya yi sallar azahar ce ba juma'a ba. Wasu daga cikin malamai sun hana sallatar juma'a da niyyar azahar, amma babu wata kakkwarar hujja a kan haka, domin sabanin niyya tsakanin liman da mamu ba ya tasiri wajen hana bin sallar junansu, bisa zancen malamai mafi rinjaye.

3. Matafiyi zan iya limancin juma'a ga mazauna gari bisa zance mafi inganci. Domin kasancewar juma'a ba ta wajaba a kansa ba ba ya nufin rashin ingancin juma'arsa idan ya sallace ta, duk kuwa wanda sallarsa ta inganta to limancinsa ya inganta.
4. Ya tabbata cewa Sayyidina Mu'awiya (RA) ya yi tafiya zuwa wani gari da ake kira An-Nukhaila, kuma ya yi mutanen garin sallar juma'a. [Duba Ibn Abi Shaiba#5501]. Hakanan shi ma Sarki Umar dan Abdul-Aziz ya je wani gari da ake kira As-Suwaida'u, tafiyar kwana biyu daga Madina, kuma ya ja su sallar juma'a duk kuwa da yana matafiyi. [Dubi Ibn Abi Shaiba#5500].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat: (1440H) *[20]*

*Kyauta Tsakanin Musulmi Da Wanda Ba Musulmi Ba*

1. Kafirai kashi biyu ne:
Kashi na farko, su ne masu yakar Musulmi da cutar da su da shirya musu mummunan tanadi, to wadannan wajibi ne ga Musulmi su matsa musu lamba har sai sun daina cutar da su, sun zabi zaman lafiya.

2. Kafirin da ya fi karfin Musulmi, watau ya zamanto ba za su iya kare kansu daga cutarwarsa ba sai ta hanyar kyautata masa da ba shi wani abu daga dukiyarsu, to babu laifi idan sun yi haka don su kubuta daga sharrinsa da zaluncinsa.

3. Annabi (SAW) ya yi niyyar ya ba wa Kabilar Gadafana rabin kayan amfanin gonar mutanen Madina domin ya kare Musulmi daga sharrinsu. Kuma ya kanyi irin wannan siyasar ga munafukai a Madina duk kuwa da cewa sharrinsu ya bayyana a fili.

4. Kashi na biyu, wadanda ba Musulmi ba amma ana zaune da su lafiya, ko dai wadanda wurin zama ya hada su da Musulmi ko kuma wadanda ake da yarjejeniyar zaman lafiya da su, to wadannan ya halatta a kyautata musu, domin idan kyautata musu zai jawo hankalinsu su karbi Musulunci, to yin haka abu ne mai kyau. Kuma duk wanda ya yi musu alheri da wannan manufar to yana da lada a wurin Allah.

5. An samu wasu daga cikin sahabbai wadanda sukan aika kyaututtuka ga makotansu wadanda ba Musulmi ba, kamar Abdullahi dan Abbas da Abdullahi dan Amru da A'isha, Allah ya yarda da su baki daya. Ya tabbata cewa, wata Bayahudiya ta nemi taimako wajen Nana Ai'sha kuma ta taimaka mata. [Dubi, Bukhari#1049 da Muslmi#903].

6. Annabi (SAW) yakan karbi kyautar wadanda ba Musulmi ba, kuma yakan yi musu tukwici a kai. An karbo daga Abu Humaid As-Sa'idi (RA) ya ce: Sarkin Aila (Banasare) ya aiko wa Annabi (SAW) kyautar farar alfadara da mayafi. [Bukhari#1481 da Muslim#1392].

7. Ya halatta a karbi kyaututtukansu na bukukuwansu, sai dai abin da suka yanka don abubuwan bautarsu, wannan bai halatta a ci ba. [Dubi, Ibn Taimiyya, Iktidha'u Siradil Mustakim, juzu'i na 2, shafi 51-52].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[21]*

*Tsayuwar Dare*

1. Tun da farko da Allah ya fara yi wa Annabi (SAWA) wahayi a Makka ya umarce shi da tsayuwar dare, watau sallar dare. Wannan kuwa yana nuna girman falalarta, domin tana daga cikin abubuwa da ke kara wa bawa jajircewa da juriya a kan hanyar Allah, saboda ta kunshi karfafa alaka tsakanin bawa da Ubangijinsa.

2. Sallar dare ita ce sallar nafilar da ta fi kowace falala, kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake cewa: "Mafificiyar salla bayan ta farilla ita ce sallar tsakar dare"[Muslim#1163].

3. Abubuwan da suka sanya sallar dare ta fi falala su ne:
Na daya, Dare shi ne lokacin da Allah Ta'ala yake sauko wa saman duniya ta kusa, yana neman wanda zai tambaye shi ya ba shi da wanda zai roke shi ya amsa masa da wanda zai nemi gafararsa ya gafarta masa, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya bayyana a hadisin Abu Huraira. [Dubi, Muslim#758].
Na biyu, dare shi ne lokacin da mutane suke koma wa gidajensu don barci da hutawa, saboda haka mai tsayawa a cikinsa domin yin ibada zai samu kadaita da Ubangijinsa, zuciyarsa za ta samu cikakkiyar nutsuwa da gaskiyar koma wa ga Allah ba tare da wani ya san me mutum yake ciki ba. Ibadar boye ta fi ibadar sarari falala, domin da wuya riya ko yi don a gani su shiga cikinta har su gurbata ta kamar yadda yakan faru ga ibadar da ake yin ta da rana ido na ganin ido.
Na uku, Mai tsayuwar dare yakan samu taimako da tallafi daga Allah a cikinsa fiye da sauran ibadu, don haka ne Allah ya sanya shi cikin ayyukan farko da umarci Annabinsa (SAW) da shi a farkon aiko shi.

4. Mun shiga goman karshe ta wata mai albarka wadda Annabi (SAW) yakan ninninka ibadarsa a cikinsu yakan yi kokarin da ba ya yinsa a sauran kwanakin Ramadana kamar yadda Nana A'isha ta bayyana. [ Muslim# 1175]. Don haka yana da kyau mu ribace ta, don mu dace da gafarar Allah da rahamarsa, mu rabauta da samun ibadar daren lailatul Kadari wadda ibada a cikinsa ta fi ibadar watanni dubu da babu ita a ciki, watau ibadar shekara tamanin da uku. Allah ya sa mu dace. Amin.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[22]*

*Su Ma Al'ummu Ne Kamarmu*
Allah Ta'ala yana cewa:
(Kuma babu wata dabba da take tafiya a bayan kasa, kuma babu wani tsuntsu da yake tashi da fukafukansa, face (su ma) al’ummu ne irinku. Ba Mu yi sakacin barin wani abu ba a cikin littafi, sannan kuma zuwa ga Ubangijinsu ne za a tara su) [Al-An'am, aya ta 38].
A cikin wannan ayar Allah (SWT) ya sanar da bayinsa abubuwa kamar haka:-

1. Ya wajaba mutane su sani ba su kadai Allah ya halitta a wannan duniya ba, balle su yi zaton zai bar su sakaka babu wani tsari da zai dora su a kai ko wata doka da zai gindaya musu. Duk halittar da Allah ya yi a sama ko a kasa ko a ruwa, to ya tanadar mata wani tsari da take tafiya a kansa, hatta dabbobi da ya halitta yana gudanar da rayuwarsu ne cikin wani tsari da ya dora su a kai. Don haka ya zama wajibi rayuwar mutane ta kasance tana gudana a kan irin tsarin da Allah ya tanadar musu su gudanar da rayuwa a kansa, wanda shi ne shari'ar da ya aiko annabawansa da ta.

2. Allah (SWT) bai bayyana mana inda muka yi kama da dabbobi da tsuntsaye ba; ya bar mana abin a bude don mu gudanar da tunaninmu mu gano fuskokin kamanceceniyar da kanmu, wanda yin haka zai kara mana nutsuwa da saduda ga hukuncin Allah.

3. Babu abin da Allah (SWT) ya bari bai rubuta shi a cikin Lauhil Mahfuz ba, domin ya umarci Alkalamin kudura da ya rubuta duk abin da zai faru tun farkon duniya har zuwa tashin alkiyama. Yarda da haka yana cikin imani da kaddara wanda wani rukuni ne daga cikin rukunan imani.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadiniyyat (1440H) *[23]*

Rama Mugunta Da Alheri: *Darasi Daga Rayuwar Ibn Taimiyya*

1. Allah Ta'ala ya ce:
(Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama daya ba. To ka ture mummuna da abin da ya fi kyau, yayin nan sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce ya zamanto kamar wani masoyi ne na kut da kut) [Fussilat, aya ta 34].

2. Imam Ibnul Kayyim yana magana a kan kyautata wa makiyi yayin da yake tsaka da rashin mutuncinsa, malam ya ce:
"Duk wanda yake son ya fahimci wannan babban matsayi, to ya karanta sirar Manzon Allah (SAW) da mu'amalarsa da mutane zai ga wannan dabi'a a fili. Babu wani wanda ya fi Manzon Allah siffantuwa da wannan kyakkywar dabi'a kamar Manzon Allah (SAW), sai kuma magadansa, kowanne gwargwadon kasonsa daga kayan gadonsa.
"Ban taba ganin mutumin da ya siffantu da wadannan kyawawan siffofi ba kamar Shaikhul Islam Ibn Taimiyya, Allah ya ji kansa. Wani daga cikin manyan abokansa yana cewa: 'Ina ma a ce zan iya kyautata wa abokaina kamar yadda Ibn Taimiyya yake kyautata wa makiyansa. Ban taba jinsa yana yi wa daya daga cikinsu mummunar addu'a ba, koyaushe sai dai na ji shi yana yi musu addu'o'i na alheri'.
"Wata rana na kawo masa albishir na mutuwar wani babban makiyinsa mai tsananin nuna masa gaba da cutarwa, amma sai ya daka mini tsawa, ya kama fadar 'Inna Lillahi Wa inna ilaihi raji'un'. Nan take ya tashi ya nufi gidan mamacin don yi wa iyalansa ta'aziyya, har ma ya rika fada musu cewa: 'Ni zan zama madadinsa a wurinku, kuma duk abin da kuke bukata na taimako zan yi muku'. Wannan ya yi matukar faranta musu rai, suka yi masa kyakkyawar addu'a, suka kuma girmama shi matuka".
[Dubi, Ibnul Kayyim, Madarijus Salikin, juzu'i na 2, shafi na 328-329].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[24]*

*Kashe-Kashen* *Abokan Hulda*
*Abokan hulda kashi hudu ne*

*1. Na farko, wadanda kake bukatar hulda da su a koyaushe, dare ne ko rana, kamar yadda kake da bukatar ci da sha. Babu ranar da za ka daina bukatarsu a rayuwarka. Wadannan su ne malamai na Allah, wadanda suka san umarni da hani na Ubangiji, suka san hanyoyin makircin Shaidan ga dan'adam, suka kuma san cututtukan zukata da magungunansu. Su ne masu yin nasiha don Allah a bisa littafin Allah da sunnar Manzon Allah (SAW).*
*
2. Kashi na biyu, su ne wadanda hulda da su take kamar hulda da magani da za ka bukata yayin da kake rashin lafiya, da zarar ka samu lafiya sai ka dakatar da hulda da shi. Wadannan su ne wadanda kake kulla huldar rayuwar duniya ita kadai da su. Duk sanda bukatarka a wajensu ta kare sai kowa ya kama gabansa.*

*3. Kashi na uku, su ne wandanda hulda da su ta zamo maka kamar wata cuta mai wuyar magani. Su ne wadanda ba za ka ci ribar duniya ballantana ta lahira a wajensu ba. A madadin haka ma sai dai su jawo maka asarar duniya ko ta lahira ko duka biyun. To duk wanda ya rungumi hulda da irin wadannan to ya sani zai kashe kansa ne murus.*

*4. Daga cikin wannan kashi akwai wanda hulda da shi kamar ciwon hakori ne mai tsanani, amma da zarar an cire shi sai mutum ya sami lafiya. Akwai kuma wanda hulda da shi take kamar zazzabi mai zafi. Shi ne mutumin da yake da rangwamen hankali, wanda bai iya magana ba ballanta ka amfana da maganganunsa, sannan bai san ya yi shiru ya saurare ka ba ballantana ya karu da maganarka. Idan yana magana sai ya rika jiji da kai yana zaton maganarsa tana birge masu sauraronsa. Amma da ya yi shiru sai kowa ya ji kamar an sauke masa wani kaya ne mai nauyi daga kansa. Idan Allah ya so jarrabar bawansa sai ya hada shi zama da irin wannan mutum, hulda da shi ta zamo masa dole. Duk wanda Allah ya jarrabe shi da haka, to ya yi kokari ya kyautata mu'amalarsa gare shi har zuwa lokacin da Allah zai kawo masa mafita, ya raba su.*

*5. Kashi na hudu, shi ne wanda hulda da shi take tamkar dafi ko guba mai hallakarwa. Idan mutum ya sake ya sha ta, to hallaka ce a gabansa babu makawa. Idan an yi dace an samu makarin wannan dafin, sai ya tsira da rayuwarsa, idan kuwa ba a sami makarinsa ba, to sai dai a shirya jana'izarsa. Wadannan su ne masu gurbataccen addini masu kokarin hallaka bawa da ingiza shi cikin sabon Allah da Manzonsa da rungumar hanyar bidi'a da bata da son zuciya. Allah ya mana tsari. Amin.*
[Dubi, Ibnul Kayyim, Bada'i'ul Fawa'id, juzu'i na 2, shafi na 273-274].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadiniyyat (1440H) *[25]*

       *Kishin Kasa*

Allah yana cewa:
(Kuma in da a ce lalle mun wajabta musu cewa: “Ku kashe kawunanku ko ku fita daga gidajenku,” da ‘yan kadan ne daga cikinsu za su aikata hakan.) [Suratun Nisa'i, aya ta 66].

1. A wannan ayar Allah Ta'ala ya nuna yadda ya dasa wa dan'adam son kasar haihuwarsa, har ma ya nuna cewa fitar da shi daga mahaifarsa daidai yake da raba shi da rayuwarsa.

2. Babu shakka yayin da aka haifi mutum ya bude idon ya ga 'yan'uwansa da ke kewaye da shi a gidansu, ya kula da kaunar da suke nuna masa da kulawar da suke ba shi, ba shakka wannan zai dasa masa son gidansu da kishinsa a zuciyarsa. Yayin da yi yi wayo har ya fara shiga jama'ar unguwarsa, ya rika cudanya da su, har ya kai ga gane amafaninsu a gare shi, ya kuma fahimci cewa sun yi tarayya da shi a cikin abubuwa da dama, wasu ma sun hada dangantaka ta jini da haihuwa da shi, to babu shakka wannan kuma zai dasa masa son unguwarsa da kishin jama'arsa.

3. Yayin da kuma ya kai munzalin babban mutum ya shiga mu'amala da 'yan kasarsa masu yare da al'adu irin nasa, ya fuskanci cewa su ma suna da dabi'u da bukatu iri daya da nasa, to daga nan ne son kasarsa da kishin al'ummarsa zai dasu a cikin zuciyarsa. Don haka duk inda ya je zai yi ta marmarin ya dawo kasarsa ta haihuwa. A kuma duk inda yake a kasarsa zai yi ta begen unguwarsu da gidan da aka yanke masa cibiya. Baba mai ja da wannan sai wanda zai yi inkarin fidira ta halitta da Allah ya wa dan'adam.

4. Duk da haka mutane sun kasu kashi hudu dangane da son gidajensu ko jama'arsu ko kishin kasashensu:

5. Kashi na farko, su ne masu nuna da son kai, wadanda ba sa tunanin taimakon kowa sai iyalansu da mutanen gidansu. Batun mahaifarsu ko kasarsu ba ya gabansu samsam. Ko da sun shiga cikin jama'ar unguwa ko ta kasa, to suna zama da su ne a matsayin 'kaska rabi mai jini'. Sau tari irin wadannan mutane ba su da wani amfani har ma ga iyalan nasu da 'yan'uwansu domin tsananin son kansu.

6. Kashi na biyu, su ne wadanda ba su manta da mahaifarsu ba, suna kishinta matuka suna kuma kokarin su ga sun amfanar da jama'ar yankinsu. Amma wajen nuna nasu kishin sukan bi kowace irin hanya halattaciya da haramtacciya, ko da kuwa ta hanyar su cutar da wasu jama'ar ne. Sukan yi kokarin tsotsar jinin wasu al'ummu da danne su da nuna musu wulakanci da tauye hakkokinsu domin su dadada wa nasu. To irin wadannan mutane annuba ne ga sauran al'ummu kai har ma ga tasu jama'ar, domin ba abin da za su jawo musu sai bala'i da bakin jini.

7. Kashi na uku, su kuma su ne wadanda 'yancin kasarsu kawai suka sani, ba su yarda cewa wasu kasashe suna da 'yanci ba. Addininsu kadai shi ne mai gata, ba su yarda wasu masu wani addini ba su ma su sami gatan yin nasu addinin. Sukan yi fafutakar danne 'yancin wasu kasashe, wani lokacin ma ta hanyar mamaya da mulkin danniya, ba kuma za su kyale su ba ta ruwan sanyi sai dai ta tsiya. To irin wadannan suna karo da asalin abin da Allah ya dasa wa mutane ne na son kasarsu da mahallansu da danginsu.

8. Kashi na hudu, su ne wadanda suka yarda da cewa Allah ya dasa wa kowa son kasarsa a halittarsa ta farko da yi yi masa. Sannan suke mu'amala da kowa gwargwadon yadda jiren kaunarsu ya da dasu a zukatansu, wadda yana farawa ne daga gida sai mahalli sai kasa. Sukan ba kowa hakkinsa gwargwadon yadda ya dace ba tare da wani ya danne na wani ba. Wannan shi ne kishin kasa na gaskiya da Musulunci ya yarda da shi, ba kishi irin na dan tsako ba, ko na kwashe duka ba. Dubi Suratun Nisa'i aya ta 36].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[26]*

*Guje wa mahallin Tuhuma*

1. Wata rana Manzon Allah (SAW) yana i'itikafi a Masallacinsa a goman karshe na watan Ramadan, sai matarsa Ummuna Safiyya ta kawo masa ziyara da daddare. Bayan sun dan tattauna da shi sai ta tashi don koma wa gidanta. Manzon Allah (SAW) ya rako ta wajen kofar Masallaci. Suna tsaye tare sai wasu sahabbai biyu suka zo shigewa ta gabansu. Da suka gan su tsaye sai kunya ta kama su sai suka kara sauri. Da ganin haka sai Manzon Allah (SAW) ya ji tsoron kada Shaidan ya jefa musu wani mummunan zato a zukatansu na ganin Annabi (SAW) a tsaye tare da wata mace. Sai ya kira su ya shaida musu cewa, wannan Safiyya ce, watau matarsa ta aure ba wata bare ce suke tsaye tare da shi ba.

2. Wadannan sahabbai suka yi mamakin wannan magana da Manzon Allah (SAW) ya fada musu, domin kuwa ko da wasa ba za su taba munana wa Annabin Allah zato ba bayan sun yi imani da gaskiyarsa da nagartarsa. Amma duk da haka sai Manzon Allah (SAW) ya nuna musu cewa Shaidan yana gudu a jikin mutum a magudanar jini, watau ba ya raina duk wata irin dama da zai samu ta ganin ya saka masa mugun tunani a ransa, ko da kuwa ya san ba lalle ne ya yi nasara a kansa ba. [Dubi, Bukhari#2038 da Muslim#2178].
DARASI:

3. Don haka kamar yadda ya wajaba mutum ya kare kansa daga duk abin da zai zubar masa da mutunci, to hakanan ya zama wajibi ya kare mutuncinsa daga duk wani surutu na mutane da mugun zatonsu, domin daga zato ne sai a fara jin miyagun kalamai sun fara fitowa Idan kuma surutun mutane ya yi yawa game da mutuncin wani, to da wuya ne bai lalata masa shi ba, duk kuwa wanda ya yi asarar mutuncinsa to ya yi asarar kimarsa ne a idon jama'a, daga nan kuma ya yi asarar komai nasa a rayuwarsa. To don gudun irin wannan mummunan karshe ya zama wajibi a kiyaye mutunci tun daga farko.

4. Bai kamata mutum mai mutunci ba ya kai kansa inda zai jawo wa kansa zargi da tuhuma, ko da kuwa shi yana ganin kansa mai tsarki ne, ba ya da wata alaka ta kusa ko ta nesa da irin tuhumar da za a yi masa. Domin abin da zai yi la'akari da shi shi ne rayuwarsa a nan duniya ba tasa ce shi kadai ba, a'a tasa ce shi da 'yan'uwansa da masoyansa, idan har ya jefa kansa cikin zargi to ya tabka wa kansa da 'yan'uwansa da masoyansa babbar asara, ya jefa kansa da 'yan'uwansa cikin bala'i wanda zai cutar da addininsa da 'yan'uwansa Musulmi, musamman idan ya zamanto babban mutum ne wanda ake koyi da shi ko ake amfana da iliminsa, don haka zubewar mutuncinsa asara ce ga Musulmi da Musulunci baki daya.

5. Saboda haka duk sanda mutum ya tsinci kansa a inda yake tsoron za a yi masa mummunan zato, to ya yi maza ya bayyana wa mutane gaskiyar lamarin, kada ya dogara da cewa ai mutane suna ganin girmansa ba za su yi masa mummunan zato ba.
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[27]*

*Hudubar Usman Bin Affan* Ta Karshe
A karshen rayuwarsa sayyiduna Usman dan Affan (RA) ya yi wa jama'a hudubar karshe inda yake cewa da su:

1. "Lalle Allah (SAW) ya ba ku duniya ne domin ku nemi lahira da ita. Bai ba ku ita ba don ku raja'a a kanta.

2. "Duniya mai karewa ce, lahira ce kadai mai wanzuwa har abada. Kada ku bari mai karewa (duniya) ta sanya muku girman kai. Kada kuma ku yarda ta dauke muku hankali har ku manta da mai wanzuwa (lahira).

3."Ku fifita abin da zai dawwama har abada a kan wanda zai kare, domin duniya mai yankewa ce, kuma zuwa ga Allah ne makoma take.

4. "Ku kiyaye dokokin Allah, domin ta haka ne za ku sanya shamaki tsakaninku da azabarsa, sannan ku sami tsanin da zai kai ku zuwa gare shi.

5. Ku kiyayi kishin Allah, ku kuma ci gaba da zama kanku a hade, kada ku rarrabu kungiya-kungiya: (Ku tuna ni'imar Allah da ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai ya hada tsakanin zukatanku, sai kuka zamo 'yan’uwan juna a sakamakon ni'imarsa.)".
[Dubi, Ibn Asaakir, Taarikhu Dimashk, juzi'i na 39, shafi na 238].
*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*

Ramadaniyyat (1440H) *[28]*

*Fiyayyar Al'umma A Bayan Kasa*

1. Allah Ta'ala yana cewa:
(Ku ne mafi alherin al'umma wadanda aka fitar ga mutane, kuna umarni da kyakkyawan aiki, kuma kuna hana mummuna aiki, kuma kuna yin imani da Allah) [Ali Imaran, 110]

2. Ya kamata al’ummar Musulmi su fahimci cewa, su ne fiyayyu a cikin duk wata al’umma da aka taba yi a bayan kasa, don su fahimci kimarsu da darajarsu, kuma su gane cewa, sun fito ne don su ja ragamar tafiyar sauran al'ummu. Kuma nufin Allah shi ne alheri ya yi jagoranci a bayan kasa ba sharri ba, a bayan kasa, don haka ya kamata su zama koyaushe su ne masu bayarwa, ba masu karba ba. Kuma abin da za su bayar na akida da ilimi da halayya da tsarin rayuwa ya zama mai inganci ne.

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...