Wane irin waya ya dace ka saya?
amsar tana cikin me zakayi da wayar, mukan Sami matsala wajan siyan waya bamu san me zamuyi da ita ba Ko kuma wana irin sabon abu tazo da shi ba a'a kawai mai tsada ce to tana da kyau. Ba haka bane akwai Karin kudi na sunan kamfanin waya, domin zaka samu waya ta kamfanin Samsung da ta kamfanin HTC sunfi kowane kamfani tsada bayan akwai kamfanunuwa wadanda suke wayoyi masu kyau da sauki irinsu xiami, plus1, infinix da sauransu. Mun gwammace mu Sai mai tsadar nan kawai Dan ace na rike waya mai tsada. Akwai Abubuwa masu amfani guda biyar da su suka fi komai amfani a waya wato RAM, PROCESSOR, GRAPHICS,CAMERA Sai kuma Operating system wani lokacin internal storage.
RAM.
RAM ana kiransa da random access memory wato memory ne da yake Shiga ko ina dan ganin waya ta tafi dai dai, kuma yana da matukar amfani a cikinta domin shine yake bayyana me waya take da karfin yi, me zata iya dauka na application domin akwai game da zaka ga nauyinsu kadai yakai 5GB kasan dole in aka ce RAM dinka karami ne bazasuyi ba ko kuma kaga hasalima wayar tana daddakirewa wato tana slow in kayi sa'a yayi kenan. A wannan zamani yawanci wayoyin da akeyi suna zuwa da RAM Wanda ba ya gaza da 1GB sai dai in yan China ne wato wadanda basu da kyau domin duk operating system da yakai 4.0 a wayar Android dole yana bukatar wannan RAM din. Dan haka Ina bada shawara ka dinga tambaya
Ko kuma ka Shiga settings> Apps> running a kasa zaka ga yawan ram din nawa Akai amfani da shi da kuma nawa ya rage.
Ko kuma ka Shiga settings> Apps> running a kasa zaka ga yawan ram din nawa Akai amfani da shi da kuma nawa ya rage.
PROCESSOR.
Processor wani abu ne da ake sawa ajikin injin waya wanda yake temakawa wajan saurin aiki, suna tafiya tare ko yaushe da RAM domin processor baza ta bada saurin da ake bukata ba matukar ba a saka mata RAM din da yadace da ita ba misali. Akwai tsarin sa processor biyu ko hudu da akeyi yanzu wato dual core, ko kuma quad core. Amma in kasa wannan processor din bakasa RAM din da yakai 1GB ba kwarai wayar bazatai saurinba domin kamar jiki Ba lafiya amma zuciya tanasan ai tafiya kaga wannan bazai yiwuba so shima anan haka yake. Yadda zaka gane ya karfin Processor dinka take shine zaka Shiga settings> About phone/tablet> device information zaka ga yawan RAM da kuma Karfin Processor ana aunashi da alamar GHz kuma da yawan su a cikin wayar wato biyu ne ko hudu.
GRAPHICS.
Graphics yana nufin kyan zane da fitar kaloli a jikin waya. Manyan wayoyi sukan bada graphics mai matukar kyau da zaka ga screen yayi kyau kana kallo kamar gaske in kana game kamar ka zaro mutum domin 2D da 3D sun fita yadda ya kamata. Kasancewarsa wani abu da yawanci masu game ne suka fi damuwa da shi amma mutane suna san ganin screen yayi kyau. Kana gane kyan graphics daga screen amma yadda karfin sa yake sai an sa application kamar Antutu benchmark ko CPU-z zasu gayama kyan graphics din wayarka. Ana auna shi a pixels.
CAMERA
kasancewar muna zamanin da photo yazama wani abu mai matukar amfani yasa camera a waya mai kyau take dadawa waya mutunci. Kasancewar abune mai sauki wajan gane karfin camera domin ana rubutawa a bayan waya kasan camera din ya karfinta yake ko da babu zaka iya dubawa in ka Shiga Camera> settings> picture size. Zaka ga kafin camera yawanci Yana farawa daga 5MP wato mega pixels zuwa 13MP Wanda yanzu shi yafi kowanne karfi.
OPERATING SYSTEM (OS)
Kasancewar kullum ana kara gyara Android operating system shiyasa kasamu babba zai kara bayyana me waya zata iya akwai application da zaka ga in os dinka yayi kasa da 4.0 baya dauka. Misali Emoji smiles basayi har sai OS dinka yakai 4.4 wato KitKat shi yasa ka samu sabo shi zaifi, zaka iya duba Wana irin operating system ne a waya in ka Shiga settings> about tablet/phone > Android version. Zaka danna Android version sau uku da sauri Dan ya nuna Maka sunan OS din.
Sunan Android Operation system
Android donuts 1.6
Android Eclair 2.0
Android Froyo 2.2
Android Ginger Bread 2.3
Android Honey Comb 3.0 na tablets ne kawai
Android ice cream sandwich 4.0
Android Jelly Beans 4.1- 4.3
Android KitKat 4.4
Android Lollipop 5.0
Android Eclair 2.0
Android Froyo 2.2
Android Ginger Bread 2.3
Android Honey Comb 3.0 na tablets ne kawai
Android ice cream sandwich 4.0
Android Jelly Beans 4.1- 4.3
Android KitKat 4.4
Android Lollipop 5.0
Internal Storage
Internal storage shine iya adadin GB da waya take dauke da shi Ba tare da kasa memory card bawayoyin sukan zo da wani wae da zaka sa photo, Waka da videos a cikin wayarka. Domin wasu basu cika san amfani da memory Ba shi yasa sunfi san amfani da waya mai babban internal storage yawanci Yana farawa daga 2GB zuwa 32GB wasu wayoyin har 64GB, 128GB. Zaka iya duba adadin internal storage in ka Shiga settings> storage.
No comments:
Post a Comment