FA'IDODIN ALBASA
************************
Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayyen Fiyayyu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyansa har zuwa ranar sakamako.
Kamar shekaru biyu ko uku da suka gabata, Zauren Fiqhu ya kawo muku wata gajeriyar fadakarwa dangane da abubuwan amfani ko fa'idodin da albasa ke dauke dashi. To in shaAllah awannan karon zamu sake lekawa ne mu gano wasu daga cututtukan da akan iya magancesu ta hanyar amfani da albasa :
1. Albasa tana karfafa garkuwar jikin Dan Adam, tana kuma magance Quraje ajikin fatar Dan Adam idan ana shafa ruwanta akan kuraje sukan warke cikin kankanin lokaci in sha Allahu.
2. Albasa tana kashe kwayoyin chutar dake rayuwa acikin bakin Dan Adam. Wanda yake fama da yawan kurajen baki, ko ciwon hakori akai-akai ya samu albasa kamar yanka biyu ko uku ya rika taunawa har tsawon minti biyu ko uku. In sha Allahu za'a dace.
3. Idan kana fama da matsalar toshewar numfashi ko ciwon mura mai tsanani ko kumburewar cikin hanci, ko zazzabi, ka samu albasa ka daka, ka matse ruwan ka rika gogawa acikin hancinka har tsawon kwanaki uku. In sha Allahu zaka samu waraka.
4. Idan kuma ciwon kai ne ko zazzabi ka shafa ruwan albasar akan goshinka da ha'barka.
5. Wanda ke fama da matsalar hawan jini ya rika shan cokali guda na man albasa a kullum bayan cin abincin dare. In sha Allahu jinin zai rika daidaituwa.
6. Hakanan masu fama da ciwon wuya ko makogoro ko Qirji ya rika shan ruwan albasa ko manta, kuma yana shafawa awajen dake ciwon.
7. CIWON SUGAR (DIABATES) - Albasa tana taimakawa wajen daidaita sukari ajikin dan Adam. Wato tana kunshe ne da wani sinadarin da ake kira Glucosine. Wanda yayi kama da sinadarin Insulin irin wanda masu ciwob sugar suke bukata.
Idan kana fama da wannan matsalar ka rika samun albasa 'yar Madaidaiciya kana ci kullum da safe kafin cin abinci. In sha Allahu zaka ji dadin jikinka.
8. Wanda cikinsa ya Qulle ko ya 'daure ya zamanto ba ya iya yin ba-haya saboda basur ko wata chutar, ya nemi albasa ya yanka yaci, sannan yasha nono ko madara daga baya. In sha Allahu sauki zai samu.
9. Wanda ke fama da matsalar "Prostate Cancer" wanda ke sanya fitsarin mutum ya makale har ba ya iya yinsa, ya nemi albasa ya yankata Qanana ya zuba ta acikin Khal Tuffah (Jan ruwan Khal).
Ya barshi har tsawon kwanaki uku ajere sannan ya fara shan rabin rabin kofi (¼ cup) kullum da sassafe har tsawon kwana goma. In sha Allahu wannan ciwon zai bar jikinsa kuma zai samu lafiya da ikon Allah.
Daga zauren fiqhu
Wannan website mun bude shi ne dan watsa duk abinda muka san insha Allahu zai anfani al'umma.
Ads
Tuesday, 11 June 2019
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...
-
Hadisi daga Hasanul Basariy daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace: “Akwai wani mutum daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww) daga cikin...
-
****Babu Abin da yake tabbas a duniya sai Canji. Komai ka gani a yau watarana zai canja daga yadda ka san shi. Komai yana canjawa ban da sar...
-
Lokacin da Shehu Jaha yana alkalanci a birnin Aku Shahar, sai ga wasu mutane sun zo gabansa suna rikici kamar sa naushi juna. Da suka gurfan...
No comments:
Post a Comment