*Dr. Muhd Sani Umar R/lemo*
Ramadaniyyat (1440H) *[12]*
*Al-Imam Ibn Abi Zaid Al-Kairawani Da Sufayen Zamaninsa*
1. Kamar yadda Allah (SWT) ya ba wa annabawa mu'ujizoji domin tabbatar da gaskiyar annabcinsu, hakanan yake gudanar da wasu karamomi a hannun wasu bayinsa nagari, domin nuna girman matsayinsu a wurinsa da taimaka musu a kan wani lamari da ya shafi addaninsu ko rayuwarsu.
2. Ahlusunna duka sun yi imani da karamomin waliyyan Allah, saboda abu ne da ya tabbata a Alkur'ani da hadisan Manzon Allah (SAW) masu yawa. Babu mai ja a kan haka sai mabiya ilimin Falsafar Girikawa da Mu'utazilawa da wasu daga cikin Ash'ariyya.
3. Sukan wani babban malamin Sunna da tuhumarsa da cewa bai yarda da karamar waliyyan Allah ba suka ne ga ingancin akidarsa ta Sunna. Wannan kuma shi ne abin da ya faru ga babban malamin nan na fikihun Mazhabar Malikiyya, watau Abu Muhammad Abdullah dan Abu Zaid Al-Kairawani marubucin lilttafin 'Risala' shahararren littafin fikihun nan a kasar Hausa da sauran duniyar Musulmi.
4. Yadda al'amarin ya faru kuwa shi ne, akwai wani malami mai da'awar Sufanci ana kiransa da suna Abdurrahim As-Sikilli. Shi wannan wani mutum ne mai nuna walittaka, yana kuma da'awar yana da wasu karamomi, wanda hakan ya kai shi ga da'awar ganin Allah ido-da-ido a matsayin karama, aka kuma samu wasu suka fara gaskata shi.
5. Ganin yadda wannan mutum ya fara wuce iyaka da zurmewa cikin bata ya sanya Imam Ibn Abi Zaid Al-Kairawani ya rubuta littattafai biyu don yi masa martani, na farko mai suna "Kitabul Kashf". Na biyu kuma "Kitabul Istizhar" inda ya bayyana karyar waccan da'awar ta wancan sufin malami.
6. Bayyanar wadannan littafai guda biyu ke da wuya sai magoya bayan wannan malami daga cikin sufaye da wasu masu danganta kansu da ilimin hadisi, suka shiga sukan Imam Ibn Abi Zaid da tuhumar sa da cewa yana karyata karamar waliyyai bai yarda da ita ba. Suka rubuta takarda zuwa ga shehin malamin nan na kasar Bagadaza a lokacin watau Abubakar Al-Bakillani, suna bukatar ya fadi wani abu game da wannan lamari. Al-Bakillani ya rubuta littafinsa mai suna "Al-Fark bainal Mu'ujizat Wa Karamatil Auliya'.." idan ya tabbatar da gaskiyar Karamar waliyyai, ya kuma wanke Ibn Abi Zaid daga zargin da ake yi masa, ya nuna cewa Ibn Abi Zaid ba yana inkarin karamomi ba ne, yana sukan masu wuce gona da iri ne wajen da'awar karamar karya irin su Aburrahim As-Sikilli.
7. Wannan bayani na Al-Bakillani shi ne ya rufe bakin duk wani mai sukan Ibn Abi Zaid, hakar 'yan bid'a na ganin sun rusa kadarinsa ta kasa cim ma ruwa, Allah ya ci gaba da yada hasken iliminsa har yau har gobe insha Allah.
[Dubi, Alkadhi Iyadh, Tartibul Madarik, juzu'i na 4, shafi na 492-497, da Wansharisi, Al-Mi'iyarul Mu'urib, juzu'i na 2, shafi na 392].
Wannan website mun bude shi ne dan watsa duk abinda muka san insha Allahu zai anfani al'umma.
Ads
Monday, 3 June 2019
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...
-
Hadisi daga Hasanul Basariy daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace: “Akwai wani mutum daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww) daga cikin...
-
****Babu Abin da yake tabbas a duniya sai Canji. Komai ka gani a yau watarana zai canja daga yadda ka san shi. Komai yana canjawa ban da sar...
-
Lokacin da Shehu Jaha yana alkalanci a birnin Aku Shahar, sai ga wasu mutane sun zo gabansa suna rikici kamar sa naushi juna. Da suka gurfan...
No comments:
Post a Comment