Ads

Tuesday, 11 June 2019

FA'IDODIN ALBASA
************************
Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayyen Fiyayyu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyansa har zuwa ranar sakamako.

Kamar shekaru biyu ko uku da suka gabata, Zauren Fiqhu ya kawo muku wata gajeriyar fadakarwa dangane da abubuwan amfani ko fa'idodin da albasa ke dauke dashi. To in shaAllah awannan karon  zamu sake lekawa ne mu gano wasu daga cututtukan da akan iya magancesu ta hanyar amfani da albasa :

1. Albasa tana karfafa garkuwar jikin Dan Adam, tana kuma magance Quraje ajikin fatar Dan Adam idan ana shafa ruwanta akan kuraje sukan warke cikin kankanin lokaci in sha Allahu.

2. Albasa tana kashe kwayoyin chutar dake rayuwa acikin bakin Dan Adam. Wanda yake fama da yawan kurajen baki, ko ciwon hakori akai-akai  ya samu albasa kamar yanka biyu ko uku ya rika taunawa har tsawon minti biyu ko uku. In sha Allahu za'a dace.

3. Idan kana fama da matsalar toshewar numfashi ko ciwon mura mai tsanani ko kumburewar cikin hanci, ko zazzabi, ka samu albasa ka daka, ka matse ruwan ka rika gogawa acikin hancinka har tsawon kwanaki uku. In sha Allahu zaka samu waraka.

4. Idan kuma ciwon kai ne ko zazzabi ka shafa ruwan albasar akan goshinka da ha'barka.

5. Wanda ke fama da matsalar hawan jini ya rika shan cokali guda na man albasa a kullum bayan cin abincin dare. In sha Allahu jinin zai rika daidaituwa.

6. Hakanan masu fama da ciwon wuya ko makogoro ko Qirji ya rika shan ruwan albasa ko manta, kuma yana shafawa awajen dake ciwon.

7. CIWON SUGAR (DIABATES) -  Albasa tana taimakawa wajen daidaita sukari ajikin dan Adam. Wato tana kunshe ne da wani sinadarin da ake kira Glucosine. Wanda yayi kama da sinadarin Insulin irin wanda masu ciwob sugar suke bukata.

Idan kana fama da wannan matsalar ka rika samun albasa 'yar Madaidaiciya kana ci kullum da safe kafin cin abinci. In sha Allahu zaka ji dadin jikinka.

8. Wanda cikinsa ya Qulle ko ya 'daure ya zamanto ba ya iya yin ba-haya saboda basur ko wata chutar, ya nemi albasa ya yanka yaci, sannan yasha nono ko madara daga baya. In sha Allahu sauki zai samu.

9. Wanda ke fama da matsalar "Prostate Cancer" wanda ke sanya fitsarin mutum ya makale har ba ya iya yinsa, ya nemi albasa ya yankata Qanana ya zuba ta acikin Khal Tuffah (Jan ruwan Khal).

Ya barshi har tsawon kwanaki uku ajere sannan ya fara shan rabin rabin kofi (¼ cup) kullum da sassafe har tsawon kwana goma. In sha Allahu wannan ciwon zai bar jikinsa kuma zai samu lafiya da ikon Allah.

Daga zauren fiqhu

Monday, 10 June 2019

ABOKIN HIRA


WATA BALARABIYA MAI FAHIMTA

Wannan ita kuma Balarabiya ce aka yi mai tsananin hankali da fahimta. Tana
tare da mijinta da ‘ya’yansu guda biyu Macce da Namiji. Akwai kuma surukarta;
mahaifiyar shi mijin nata a tare da su amma ta tsufa sosai, jiki ya yi rauni, gani ya
ragu. Saboda tsananin son da take yi ma dan nata sai ta riqa zaunar da shi domin su
yi labari amma shi ba ya fahimtar maganarta da kyau, kuma baya son irin labaran
da take kawowa. Al’adar larabawa a wancan lokaci kamar Fulani suke; yawo suke yi a cikin daji, su sauka nan yau, gobe su sauka can. Watarana sun yi niyyar tashi sai ya ce ma matarsa, ki shirya kayanki amma yau nan za mu bar Umma ta zauna nan ko za ta samu wasu da za su kula ta, ko kuma idan namun daji sun zo su cinye ta a huta.
Matar nan ba ta yi ma sa musu ba, kuma ta aiwatar da abin da ya ce, amma sai ta yi wata dabara.
Bai san abin da ke gudana ba sai da suka sauka a wani masauki gajiya ta lullube shi ta ko ina yana neman hutawa, sai ya tambaye ta dan karamin yaronsa kamar yadda ya saba don ya rungume shi yana debe masa kewa har sa’adda bacci ya kwashe shi. Sai ta ce ma sa ai na bar yaron a can tare da Umma. “Tare da Umma?”
“Ba ki da hankali ne”? In ji shi. A cikin ruwan sanyi sai ta ce, a’a. Ai gaskiya ba mu da
buqata da shi. A bar shi kawai wasu ma za su kula da shi, ko kuma idan namun daji sun zo su cinye shi a huta. Sai ya yi shiru bai sake cewa komai ba. Sannan ta ce ma sa shakka wannan yaron idan ya girma zai jefa ka ne a juji, ko ya bar ka a tsohon
masauki don Kura da Damisa su cinye ka. A nan ne fa hankalinsa ya dawo ma sa. Bai sake cewa uffan ba, sai ya manta gajiya, ya ruga ya koma masaukinsu na farko in da tsohuwa da yaronsa suke. Isar sa ke da wuya sai ya tarar da tsohuwa rungume da jikanta tana yi ma sa wasa cikin nishadi da jin daxi. Ya karbi yaro ya sunbace shi,
sannan ya tashi tsohuwa ya riqa hannunta suka dawo zuwa sabon masauki.

Darussa:
- Iyaye ba abin wasa ba ne

- Duk abin da ka yi ma iyayenka shi ne ‘ya’yanka za su yi maka

- Macce ta gari jigon gida ce

 Dr. Mansur Sokoto

DUNIYA MAKARANTA


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto

****Ka aurar da danka duk sadda kake so. Ka aurar da 'yarka duk sadda ta samu miji.
Idan Macce ta samu mijin tsara ba daidai ne ayi masa jinkiri ba.
****Idan Alqur’aninka ya yi qura ka zargi kanka. Duk wanda ya kwana uku bai
karanta Alqur’ani ba lallai ne zuciyarsa za ta bushe.

****Idan ka mutu ma'aikatarka za ta dauki wani ma'aikaci, matarka za ta auri wani namiji, dukiyarka za ta samu wani mamallaki ba kai ba. Ba Abin da za ka je lahira da shi sai aikinka. Gyara lahirarka, kada kyalkyalin duniya ya ruxe ka.

****Ababe uku suna da wuya amma suna da amfani. Kyauta a cikin talauci, da kamun kai a lokacin kadaici, da fadin gaskiya a gaban wanda kake tsoro.
****A lokacin da kake karami kana ganin laifin manya idan suka yi maka gyara, amma da ka girma sai ka gane su ne daidai. A lokacin kana makaranta kana ganin laifin malamai idan suka matsa ka bi doka, da ka zama Malam sai ka gano ashe su ne daidai.
Ka riqa ba da uzuri ga wanda ba matsayin ku daya da shi ba, wataqila watarana za ka
gano shi ne daidai.

WONDERFULL LESSON

TOMATOES!!!!!!!!!!!!!!!!

🍅A teacher asked her students to bring some tomatoes in a plastic bag to school.
🍅Each tomato was to be given the name of a person whom that child hates.
🍅So, the number of tomatoes would be equal to the number of persons they hate.
🍅On a pre-determined day, All the children brought their tomatoes well addressed.
🍅Some had two, some had three and some had five, some even had 20 tomatoes in accordance with the number of people they hated.
🍅The teacher then told them they had to carry the tomatoes with them everywhere they go for two weeks.
🍅As the days passed the children started to complain about the decay and smell of the tomatoes.
🍅The students who had many tomatoes complained it was very heavy to carry and the smell was too much.
🍅After a week, the teacher asked the students “How did you feel this week?”
🍅The children complained of the awful smell and heavy weight of the tomatoes, especially those who carried several tomatoes.
🍅The teacher said, “This is very similar to what you carry in your heart when you don’t like some people.
🍅Hatred makes the heart unhealthy and you carry that hatred everywhere.
🍅If you can’t bear the smell of spoilt tomatoes for a week, imagine the impact of bitterness on your heart as you carry it daily.”
🍅The heart is a beautiful garden that needs regular cleaning of unwanted weeds.
🍅 Forgive those who have angered you.
🍅This makes room for storing good things.
🍅Get Better, Not Bitter!!!
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto

****Gaskiya zuma ce. Akwai harbi amma tana da zaqi. Wanda aka buge shi da bulalar gaskiya bai fadi ba, ka sa masa ido, idan ya karasa gaba zai fadi.

****Ana ba da baya wani lokaci ba don tsoro ko jin girman kai ba. Sai don kauce ma karo da wanda bai dace ba. 

****Mai hankali idan ya yi magana sai ya kawo hujja. Wawa idan ya yi magana sai ya yi ta rantsuwa. Mai gaskiya ba ya buqatar rantse rantse. Gaskiya ba ta neman ado.

****Ana samun Rayuwa mai dadi ta hanyar barin wasu abubuwa fiye da yadda ake samun ta ta hanyar samun wasu.

****Wanda yake ba da turare ba za a rasa kamshi a hannunsa ba. Mai yin alheri ba zai rasa samun alheri ba

Saturday, 8 June 2019

Stop, Treat and Reverse Tooth Decay
By RelianceHMO
Tip Image
People once believed that tooth decay could not be treated or reversed, recent health studies now challenge this premise as wrong.

Research in nutrition has linked rejuvenated cavities to improved diet. Tooth decay mainly occurs when the teeth is frequently exposed to carbohydrates.

Bacteria in the mouth produce acids when consuming carbohydrates, this acid gradually damages the enamel of the tooth.



Ways to heal and reverse tooth decay

1. Minerals – Including minerals like calcium, phosphorous and magnesium in your diet will help you develop stronger teeth. Calcium especially strengthens the teeth; you can increase your calcium intake by consuming more yogurt, cheese and milk.



2. Avoid sugar – Try reducing or eliminating sugar from your diet. Sugar is food for bacteria; you can replace sugar with healthier options like honey.



3. Raw dairy products – Consume raw dairy products, they are rich in magnesium, calcium, phosphorus and fat soluble vitamins that are good for the teeth.

Milk, butter and cheese are some popular raw dairy foods.



4. Fat soluble vitamins – Deficiency in fat soluble vitamins is a cause of tooth decay. Ensure your diet is rich in fat soluble vitamins. Cod liver oil is a source of vitamins A, D and E.

Consume more broccoli, spinach and bone marrow as sources of vitamin K. Vitamin D can be acquired from eggs, milk and early morning sunshine
5 Ways You Can Prevent Malaria
By RelianceHMO
Tip Image
Today is World Malaria Day!

Malaria is a major public health concern in Africa because hundreds of thousands of people still die from it every year, with pregnant women, children under 5 years of age and those living with HIV/AIDs being the most affected groups.



In addition, malaria in pregnancy contributes to pregnant women developing complications like miscarriage, stillbirth, giving birth prematurely, anaemia in the woman (her blood drops to a dangerously low level)



Below are 5 ways you can prevent malaria



Proper Use of Insecticide-Treated Nets

Insecticide-treated nets, when used correctly, prevents the mosquito carrying the malaria-causing parasite from coming in contact with your body. Long-lasting insecticide-treated nets are distributed free of charge to pregnant women and new nursing mothers in many health centres in Nigeria and many other African countries.



Assess the malaria risks when traveling – Get an antimalarial ( when necessary)

A lot of people report getting malaria during a trip. Whenever you are visiting an area with a high risk of contracting malaria.

Some preventative medications might need to be taken up to two risks before traveling. While others can be taken on arrival.

Please consult a doctor about preventative medications before visiting a high-risk area.



Indoor Residual Spraying

This is the application of an effective insecticide to the inside of houses, on the walls and other surfaces that can serve as a resting place for mosquitoes carrying the malaria-causing parasite.

This malaria prevention method is not common, but it has been shown to be very effective. Once sprayed, it can last for about 6 months, during which mosquitoes that rest on the sprayed surfaces will die. When combined with the use of insecticide-treated nets, this malaria prevention method is very effective.



Go for long sleeves

Avoid wearing short clothing in the evening and at night. Wearing long sleeve shirts and trousers reduces the area of skin exposed. Travellers to mosquito-prone areas can also treat their clothes with permethrin in order to increase protection.



Proper Treatment of Malaria

While preventing contact with mosquitoes carrying the malaria-causing parasite is the best way to tackle malaria, effective treatment is very important for those who get bitten by these mosquitoes and come down with malaria.

Many people stop taking their anti-malarial medication once the symptoms disappear because they feel they have recovered and there is no need to complete the drugs. This is wrong and dangerous because it can lead to drug resistance

ABOKIN HIRA


KISHIYA BAYAN MUTUWA

Wani mutum ne suna zaune suna tadi da matarsa sai kawai ta tambaye shi,
yaushe ne za ka yi aure idan na mutu? Sai ya yi murmushi, ya ce ma ta, ba zan yi aure
ba sai qabarinki ya bushe. Ta ce, ka yi ma ni alqawarin haka? Sai ya ce, eh.
A kwana a tashi ajali ya cim ma matarsa, ta yi jinya kadan sannan ta ce ga garinku. Da aka zo jana’izarta sai ya tuna da alqawarin da ya yi ma ta. Don haka bayan sati daya duk sai ya je ya ziyarci qabarinta ya yi ma ta addu’a. Amma abin ban mamaki shi ne a kullum in ya zo sai ya tarar da qabarinta danye kamar jiya ne aka binne ta. Sai da aka yi shekaru yana haka, rannan sai ya yi kicibis da qanenta ya zo maqabartar da ruwa a jarka. Ya ce, me za ka yi ne halan? Ya ce, ina zartar da wasiyyar ‘yar uwata ne. Ya ce, me ta yi maka wasici da shi ne? Ya ce, ai ta roqe ni ne bayan kowane kwana biyu in kwarara ruwa a qabarinta.

Darasi: Kishi kumallon mata, ko suna kabari suna jin zafin sa. Mu tausaya masu
Dr. Mansur sokoto

DUNIYA MAKARANTA

****Duniya rana biyu ce. Ta farko taka ce, ta biyu ta dan uwanka. A ranarka kada ka yi rowa. A ranar dan uwanka kada ka yi raki.

****Yarda da kai ba girman kai ba ne. Kuskure daya ba ya nuna mai mugunta. Girma ba a babbar riga yake ba. Mai girma shi ne wanda ake so, kuma ake samun alheri a wurin sa.

****Kada ka raina kanka don wani ya fi ka iyawa. Koma wani fanni ka nemi taka kwarewa. Kowa da irin hikimar da Allah ya ba shi.

****Sarki abin girmamawa ne a garin sa. Malami abin girmamawa ne a garin kowa.

****Babbar bishiya ta fi ba da inwa fiye da yadda take ba da 'ya' ya.

Friday, 7 June 2019

DUNIYA MAKARANTA

****Duniya rana biyu ce. Ta farko taka ce, ta biyu ta dan uwanka. A ranarka kada ka yi rowa. A ranar dan uwanka kada ka yi raki.

****Yarda da kai ba girman kai ba ne. Kuskure daya ba ya nuna mai mugunta. Girma ba a babbar riga yake ba. Mai girma shi ne wanda ake so, kuma ake samun alheri a wurin sa.

****Kada ka raina kanka don wani ya fi ka iyawa. Koma wani fanni ka nemi taka kwarewa. Kowa da irin hikimar da Allah ya ba shi.

****Sarki abin girmamawa ne a garin sa. Malami abin girmamawa ne a garin kowa.

****Babbar bishiya ta fi ba da inwa fiye da yadda take ba da 'ya' ya.
BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA DR GUMI !!


#DR#IBRAHIM_DISINA_(HAFIZAHULLAH)
Da fatan ka tashi lafiya, Yaya Iyalai? Allah ya kareka da kariyarka ya fadada kirjinka don fahimtar sakon dan almajiri .
Malam ,
Allah ya jikan Sheikh Abubakar Gumi, tsawon rayuwarsa abinda ke bude karatun littafin Bukari da shi shine : `` karatun hadisi da aiki da shi shine zaman lafiyar musulmai´´
Abin mamaki ne kwarai ga Malamin da ke danganta kansa da Sunnar Annabi amma ka sameshi lokaci bayan lokaci yana wurgi da maganar Annabi sallallahu alaihi wasallam! Bayan Allah ya ambata cikin Alqur`ani cew: du wanda bai mika wuya gaba daya ga matsayar annabi kan lamura ba (Sunnah) ba, baiyi imani na gaskiya baa.
Fuskar Dr gumi da yanayin shigarsa da kujerar da ke gabatar da darasi, da yana martaba dukkan maganganun Annabi da ya fi kwarjini!
Hadisin Sittusshawwal dai ingantacce ne Abu dawud, Tirmizy, ibn Hibban kai har ya shigo daya daga cikin mafi ingancin littafi; Sahihu muslim, Sahabin da ya rawaiceshi kuma shine mai masaukin Manzon Allah a garin madina Abu Ayyubal ansary Khalid bn Zaid bn Kulaib (Haladu farin tsoho na madina) da yaron gidan Manzon Allah Thauban dss.Hadisin dai ingantacce ne!!
Ko iya nan kadai aka tsaya bai kamata, a sanya maganar wani ko da sahabi ne tayi gogayya da maganar Annabi ba, Ballantana ma, Manyan Malaman malikiyya cikinsu har wanda ya fi kowa yiwa Littafin da Dr ya ciro maganar Malik cikinsa(muwadda) Wato Ibn Abdulbarr Annumary yace Imam Malik ba karan tsaye ya ke yiwa Hadisin Sittushshwal ba, domin ba yanda Malik zai yi haka, Wanda shi ke cewa : ``Ko bayansa in hadisi ya inganta shine fahimtarsa´´ sannan hadisin mabubbuarsa garin madina ne ace malik bai sanshi baa.
Rashin kyamatar azimin situshshawal itace fahimtar mayan Malaman Malikiyya tare da dora zance malik kan manufarsa ta gaskiya, Wannan kuma ba sabon abu bane cikin shari`ar Musulunci ta dakatar da mutane da tsaresu kan wani aikin da yake daidai ne bisa asali amma saboda gudun takurawa mutane ko lokaci baiyi ba da za su fahimta sai a barshi zuwa lokacin da tsoron hakan ya gushe;
(1) Annabi ya guji dorawa mutane yin Aswaki kowace sallah duk da hakan sunnah ne!
(2) Ya guji rushe Ka`aba da ginata kan tushenta na zamani Annabi Ibrahim gudun mai zai je ya zo!
(3) Kin da annabi yayi na ci gaba da fitowa Sallar Tarawiy don gudun kar a maidawa mutan ta zamo tilas.
Imam Malik tsoronsa gudun kar wassu su dauka yana cikin Ramalana, Wannan kuma ba shi kadai ne ya tsoraci haka baa, Abu Yusuf dalibin Abu hanifa shima ya fahimci haka, suma a mazhabar Hanafiyya sun nemi turashicikin tsakiyarbwatan shawwal da rashin azumtarsa daf bayan kammala ramalana don a banbanceshi daga Ramadan, irin wannan aka ambata a ruwayar da Ibnu Mubarak ya yiwa Hadisin, Amma duk Malaman har Imam Malik ba wanda ya ce Bidi`a ce sai Dr Gumi, Wanda bana ganin yana jin yafi sauran malaman Nigeria fahimtar Malikiyya balle manyan malamai da wassu sun kusa shekara dubu da rasuwa irinsu Ibnu Abdulbarr wandanda suka bawa maganar malik ma`ana mai kyau!!
Abin tausayi ne ace ka zamo munbarin fada da Hadisan Annabi, Sai mutum ya kasa fahimtar inda malamin ya dosa? Tarihi ya tabbatar duk mai fada da Hadisan annabi baya kammalawa Lafiya, Mahmood abu Rayya a wannan zamani abin daukar izina ce!
Abu Rayyah da ya rubuta littafi don karyata Hadisai, karshen a bandaki ya mutu a wulakance, Sannan ofishin jakadancin Iran a kasashe daban daban su ke raba littatafansa kyauta duk da bai shiga shia`a baa, Hakannan yau Makiya sahabban Annabi su suka fi kowa tallata zancen Dr Gumi, Manufarsu sa shakku ga gabadayan Hadisan Annabi. Ina fatan kar makiya Sunnah su ringa fakewa bayan katobararka don yakar Sunnar Annabi.
Gaskiya ne a nesanta yin situshshawal daga zarar kammala ramadan don kar wassu su zaci har yanzu ana Ramadan ne , Amma wanda ya tantance ya yi azuminsa don a rubuta masa kamar shekara yayi yana Azumi, wannan kamar yadda ba a yiwa Ramadan tare haka kar a yi masa rakiya!!
A karshe shi fa Imam Malik din ya na azumtar situshshawwal a karan kansa kamar yadda dan kanwarsa kuma almajirinsa Mudarrif Ibn Abdullahi bn Mudarrif bn Sulaiman Alhilaly ya rawaito kamar yanda malamai da yawa suka ambata cikinsu akwai Alqurduby cikin Almufhim da Bajy a Almuntaqa.
Ibrahim Disina

Thursday, 6 June 2019

HAKKOKIN MANZON ALLAH (SAWW) - ZAUREN FIQHU WHATSAAPP 1 & 3.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Salatin Allah da amincinsa su Qara tabbata abisa Na farko kuma Qarshen Manzanni.

Shugabanmu Annabi Muhammadu, tare da dukkan iyalan gidansa nutsuwar al'ummah, Da Sahabbansa taurarun shiriya.

Yau zamu ci gaba ne daga wajen da muka tsaya acikin Darasinmu mai taken:

HAKKOKIN MANZON ALLAH (saww).

Mun tsaya ne, Ko ince zamu tashi ne akan maganar sabanin da Malamai sukayi akan sanya Sunan Ma'aiki (saww) ko kuma sanya alkunya irin tasa (saww).

Idan ance "ALKUNYARSA" muna nufin lafazin "ABUL QASIMI".

Imam Sharfuddeen An-Nawawy (rahmatullahi alaihi) yace:

Malamai sunyi sabani akan halarci ko rashinsa dangane da sanya ALKUNYAR ABUL QASIMI har izuwa Mazhabobi 3.

1. MAZHABIN SHAFI'IYAH: Imam Muhammad bn Idrees Ash-Shafi'iy -Mai mazhabar kenan - (rah) yana cewa:

"Bai halatta ga wani mutum ya sanya ma kansa Alkunya da ABUL QASIM.

Sawa'un sunansa MUHAMMADU ne ko kuma wanu Sunan daban".

Ku lura fa, Imam Shafi'iy (ra) ya fadi haka ne domin KIYAYE MARTABAR MANZON ALLAH (SAWW) ba wai wani dalili daban ba.

Daga cikin Manyan Almajiran Imam Shafi'iy wadanda suka ruwaito wannan Qaulin daga gareshi kuma suka tafi akai, akwai Manyan Hafizan hadisi da kuma Fuqaha'u Irinsu:

• Imam Abubakrin Albaihaqiy.

• Abu Muhammad Albaqhwiy. (aduba cikin littafinsa Attahzeeb).

• Ibnu Asakira (mai shahararren littafin hadisin  nan na Tareekhu Damashqa).

2. MAZHABIN MALIKIYYAH : Imamu Malik (rah) yace:

"Ya halatta kowanne mutum yayi Alkunyah da Abul Qasim, ko sunansa MUHAMMAD ne, ko kuma wani Sunan daban".

Yace wannan hadisin da Ma'aiki (saww) yace "KU SANYA MA 'YA'YANKU SUNANA AMMA KAR KU SANYA ALKUNYAH NA" - wannan haramci ya tsaya ne kadai alokacin rayuwar Ma'aiki (saww).

3. HANAFIYYAH da HAMBALIYYAH : su kuma sunce:

"Ya halatta kowa ya sanya ALKUNYAH ta ABUL QASIM amma banda masu suna MUHAMMAD.

AL-IMAM ABUL QASIM ARRAFI'IY yace wannan ra'ayin shine mafi dacewa.

Ko ba komai idan aka duba za'a samu akwai Manya manyan Maluman Musulunci masu irin wannan Alkunyah din. Kuma irin wannan yana faruwa tun zamanin Sahabbai. Da ace wani abun haramci ne, da tuntuni an haramta.

Shima wancan hadisin da yazo da maganar hanawar, ya kebanci lokacin da Ma'aiki (saww) yake raye ne. Saboda Yahudawa sun kasance suna amfani da wannan damar domin cutar da Musulunci.

Aduba AL-AZKAR na Imam Nawawy, mujalladi na 1 shafi na 670.

ALQADHY IYADH BN MUSA (RAH) ya fada acikin littafin ASH-SHIFA cewa:

Allah ya ambaci Manzonsa (saww) acikin littafinsa da sunan  AHMADU da kuma MUHAMMADU. Sannan yana daga cikin abubuwan da Allah ya kebanceshi dasu cewa'
Kalmar Sunansa ma YABO ne agareshi (saww).

Kuma sunayensa sun tattaro Asraru na cikar godiya ga Allah.

Masanan harshen larabci suka ce:

Idan ka dauki kalmar  "AHMADU" zaka ga cewa "AF'ALU" ce. Wato tana nufin "KAIWA MUTUKA WAJEN GODIYA GA UBANGIJI".

Idan kuma ka dauki kalmar "MUHAMMADU" zaka ga cewa: Ita kuma "MUFA'ALUN" ce.

Wato tana nufin KAIWA MUBALAGHA (MAQURA) WAJEN YAWAITA GODIYA KO KUMA YABO GA UBANGIJI (SWT).

Insha Allahu gobe zamu dora daga nan inda muka tsaya.

YA ALLAH KA QARA MANA SON MANZON ALLAH (SAWW) DA TSANTSAR KOYI DA HALAYENSA DA AYYUKANSA, DA KUMA SON MASOYANSA.

Sallu alqn Nabiyyi wq sallimu tasleeman.

DAGA ZAUREN FIQHU (31/05/2014)

Musha Dariya----- SHEHU DAMASU FADA AKAN GURMI

Lokacin da Shehu Jaha yana alkalanci a birnin Aku Shahar, sai ga wasu mutane sun zo gabansa suna rikici kamar sa naushi juna. Da suka gurfana gabansa ya daka musu tsawa ya ce, “me yake tafe da ku? Kun san nan kotu ce, ba a mana wargi anan!”
Daya daga ciki ya mike ya ce, “Allah ya gafarta Malam wannan gurmina ne aka dauke min yau kwana uku ina nemansa na ganshi a hannun wannan mutumin yana kadawa ana ba shi kudi. Na zo gabanka ne domin a karbar min kayana.” Alkali Shehu Jaha ya dubi wanda ake kara ya ce, “ka ji abin da ake kararka da shi. Haka ne? Dauke masa ka yi?” Mutumin ya ce, “gafarta Malam na tabbata dai ba nawa ba ne, amma shi ma ba nasa ba ne, tunda tsinta na yi a wuri kaza.”
Alkali ya ce da mai kara, “kana da shaidu? Kuma da wata alama a jikin gurmin naka?” Mai kara ya ce, “eh daga wuyan gurmin akwai inda aka yi ‘yar k’ofa inda ake dura mai saboda ya yi laushi, sannan daga kasansa akwai wata alamar maciji da na zana. Har ila yau akwai shaidu mutum biyu da suka san wannan gurmin nawa ne tun da jimawa.”
Alkali ya sa aka duba gurmi aka ga alamun da ya fada haka suke, sannan aka shigo da shaidu suka shaida tabbas gurmi mallakinsa ne. Ba tare da bata lokaci ba alkali Shehu Jaha ya sa aka kwace gurmi daga hannun daya aka mikawa mai shi. Sai kuwa wanda aka kwace gurmin daga hannunsa ya yi farat ya ce, “Allah ya gafarta Malam ban yarda da shaidun wadannan mutanen ba. Domin na farko yaron mai dafa giya ne, na biyu kuma dan wankin gidan karuwai ne.”
Shehu Jaha ya ce, “Shaidu sun cika yadda ake bukata, domin kayan banza mutanen banza ne ke shaida akansu. Da alk’urani ne ko wani abin kirki ba za mu karbi shaidunsu ba.”

SALATUL MAKRUB (Sallar Yayewar Damuwa)- Daga Zauren Fiqhu

Hadisi daga Hasanul Basariy daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace:



“Akwai wani mutum daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww) daga cikin Al-Ansar (Mutanen Madeenah) ana kiransa da suna “ABU MU’ALLAQ” (ra). Ya kasance shi Attajiri ne yana yin kasuwanci da dukiyarsa da kuma ta mutane.



Yana zuwa garuruwa daban-daban. Ya kasance shi mutum ne mai yawan ibadah kuma mai yawan tsantseni (kyamar haram).



Wata rana ya fita domin kasuwancinsa sai ya hadu da wani ‘Dan fashi wanda yasha ‘damara da makamai kala-kala a jikinsa. Sai ‘dan fashin yace masa “Ajiye dukkan abinda ke tare dakai domin ni kasheka zanyi”.



Sai yace masa “Mai yasa kake son zubda jinina alhali ga dukiyar nan kaje kayi sha’aninka da ita?”.



Sai ‘dan fashin yace “Amma dukiya kam zata zama tawa. Amma ni dai babu abinda nake sai zubda jininka”.



Sai Abu Mu’allaq (ra) yace “To tunda ka Qi sai ka kasheni, amma ina so ka kyaleni inyi sallah raka’a hudu”.



Sai ‘Dan fashin yace “Sallaci duk abinda kaso”. (Amma dai sai na kasheka).



Sai Sahabin nan (Abu Mu’allaq) yayi alwala ya sallaci raka’a hudu. Yana daga cikin addu’o’in da yayi acikin sujadarsa ta raka’ar karshe yana cewa:



“يا ودود يا ذاالعرش المجيد يا فعال لما يريد ، أسألك بعزك الذي لا يرام وملكك الذي لا يضام وبنورك الذي ملأ أركان عرشك أن تكفيني شر هذا اللص، يا مغيث أغثني، يا مغيث أغثني ، يا مغيث أغثني.”



“Ya Wadood Ya Dhal ‘Arshil Majeed, Ya Fa’alun Lima Yureed! As’aluka bi-izzikal ladhee la yuraamu, Wa Mulkikal ladhee la yudhaamu, Wa bi nurikal ladhee mala’a arkaana ‘arshika, an takfiyanee sharra hadhal Lissi.



Ya Mugheethu agithnee, Ya Mugheethu agithnee, Ya Mugheethu agithnee”.



“Ya Wadood Ya Ma’abocin Al’arshi mai girma, Ya mai aikata abinda yai nufi, ina rokonka don Buwayar nan taka wacce ba’a samu, da Mulkin nan naka wanda (acikinsa) ba’a zalunci, Kuma don Hasken nan naka wanda ya cika rukunan Al’arshinka.



(Ina rokonka) Ka isar min daga sharrin wannan ‘dan fashin. Ya Mai kawo ‘dauki, ka kawo min ‘dauki. Ya Mai kawo ‘dauki, ka kawo min ‘dauki. Ya mai kawo ‘dauki ka kawo min ‘dauki!”.



Yayi wannan addu’ar har sau uku. Sai ya hangi wani Mutum akan doki ya taho aguje. A hannunsa akwai wani mashi, ya ‘dora akan goshin dokinsa.



Yayin da ‘dan fashin nan ya hangeshi a tafe, sai shima ya taho wajensa. Suna haduwa sai ya soke ‘dan fashin nan da mashinsa. Nan take ya kasheshi.



Sannan ya juyo wajen Sahabin nan yace masa “Tashi”.



Sai Sahabin yace masa “Mahaifina da Mahaifiyata fansa ne a gareka! Shin wane ne kai? Gashi Allah ya taimakeni da kai”.



Sai mutumin yace masa “Ni Mala’ika ne daga cikin Mala’ikun sama ta-hudu. Yayin da kayi addu’ar nan da farko sai naji Kofofin sammai sunyi wata irin Qara!.



Sannan kayi addu’ar nan karo na biyu sai naji Mala’ikun sammai sunyi wani irin gunji.



Sannan kayi addu’ar nan a karo na uku sai naji ance lallai wannan addu’ar wani wanda ke cikin damuwa ne. Don haka sai na roki Allah yayi min izini in jibinci kisan wannan ‘dan fashin”.



Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace “Kayi sani cewa duk wanda yayi alwala yayi sallah raka’a hudu sannan yayi wannan addu’ar, lallai za’a amsa masa. Ko yana cikin damuwa ne, ko ba acikin damuwa yake ba”.



– Amma idan kai zakayi akan wata bukatarka, zaka cire daidai wajen “An takfiyanee sharra hadhal Lissi” din nan. Sai ka fadi bukatunka awajen sannan kace “Ya Mugheethu agithnee” sau uku.

YADDA ZAKA TSAYAR DA WAYARKA TA ANDROID DAGA YI MAKA TALLAR ADS A SAMAN SCREEN 

Yawancin masu amfani da wayar android suna fama da irin wannan matsalar Wanda wannan matsalar ta kasance daya daga cikin abubuwan dasuke takurawa mai amfani da wayar ta android.. Ta Kasance tana samun Matsaloli kamar Haka; 1- Mak'alewa (hooking) 2- Yin zafi (Heating) 3- Bude data Da kanta (Always Data On) 4- Cin Megabyte Da sauri tare da Fitowar Talloli.
Mafi yawancin masu amfani da wayar ta android sun kasance suna aiki da software wadda aka sani da ''Ad blocker'' wadda ke taimaka musu wurin tsaida Talloli ma'ana ''advertisements'' sedai kuma (RAM) din wayar zaiyi kasa sosai sai wayarka taringa yin slow…
MAGANIN MATSALAR
[note= Idan Kana SoN Kashawo kan wannan matsalar to da farko ka Tabbatar da Kayi] Rooting na wayar taka, Domin Tsayar da Wannan Tallolin. Kabi wadannan Matakan A Tsanake.. ◆ Ka Sauko da wannan File Din Maisuna ''hosts'' Ta Hanyar wannan link dinDownload Host.pdf
File Din Zakaga Yazo maka a matsayin ''hosts.pdf'' saika canza sunan zuwa ''hosts'' kawai kada kasanya .pdf din a gaban sunan. Yanzu saika yi copy na file din maisuna ''hosts'' zuwa cikin Folder ' Ta hanyar Amfani da Root File explorer buda root explore dinka sai kaje polder system saika sanyashi anan shikkenan. Idan ka sanyashi a folder amman kaga yaki yi, to saika goge Tsohon file din na cikin folderSaika sake kwafar file din ka turashi zuwa cikin folder. ● Yanzu saikayi reboot din wayar taka, Shikenan Ka Gama! Na Gwada kuma yana Aiki Lafiya Kalau… A Android Kitkat v4.4.2 Yana Tsaida Tallolin websites, apps, games da duk wani makaman cin hakan! Amman Fa kabi sannu kwarai da gaske a lokacin da kake sanya File din a cikin folder
Allah ya bamu sa,a

SABULUN GAYRAN FATA SA LAUSHIN SA DAKUMA MAGANIN TABO

Sabulun gyaran fata,salaushinsa dakuma maganin tabo

Kisamu sabulun salo,wato ghana soap,kisami madara,leman tsami dakuma kurkur da haska amarya,kisamu sabulun broonze bashida tsada ana saidashi a irinsu sahad,departmental stores haka saikuyi kokari kunemi sabulun caramel shima duk acikin kayan hadine to kisamu kihada sabulun duka ki daddakasu kokuma ki yanyankasu siri siri saiki gwamutsasu sannan saikikawo kurkur daidai misali ki juye kisamu haska amarya daidai misali shima ki juye.
haska amarya da kurkur agidagen gyaran jiki ake samunshi saikihadeshi asabulun kibuge sannan wasu sunasa nescafe domin yanasan laushin fata inkinaso kisaka inbakyaso saiki barshi saikijuye madararki ki buga saikikawo ruwan leman tsaminki dakika matse shima ki juye,idan kikai hakan saiki bugesu sosai su hade,zakiga yayi ruwa ruwa amman ba komai bane,saiki juye wannan hadin cikin container mai murfi ki rinka wanka dashi wannan hadin yanamugun gyara fata,ba bleaching yakeyiba,gyarafata yake yanakuma maganin kujaren fata dakuma kurajen fuska yana mugun gyaran jiki sosai kuma yanada kyau ku rinka shafa sabulunnan kamar anasaura awa daya kiyi wanka yanadakyauma kisamu ganyen magariya busasshe ki daka kizuba akan sabulun dakika hada kikara bugewa bakaramin kyau zakiba duk tabon dake jikinki saikinnema kinrasasu mata ayi kokari agyara fata dan miji yakalla yaji dadi yanasa tsansin fata dakuma laushinsa

ANFANIN NA'A NA'A GA LAFIYAR DAN ADAM

Na'a-na'a [Peppermint/mentha piperita or mint] wata shuka ce mai albarka da ake amfani da ita a matsayin maganin gargajiya. Ganyen na'a-na'a kore ne, kamshin ta nada karfi, tana da kamshi mai dadin gaske da filebo mai sanyaya rai. Na'a-na'a nada sinadarin 'minti' ( wato 'menthol') mai sanyaya rai da lafiyar jikin dan adam. Akanyi amfani da na'a na'a wajen sarrafa wasu kayan amfanin gida da muke siya na yau da kullum, wato kayan amfani da muke siya a kasuwa kamar irinsu makilin (toothpaste), sabullai (soaps), man-shafawa (creams and vaselines), cingam (chewing gum), sinadarin wanke baki (mouthwash) , magungunan shafawa (ointments), da sauransu , saboda kamshinta da amfaninta ga jikin dan adam.
Bincike ya nuna cewa, shukar na'a-na'a dai ta samune asali ta hanyar auren-shuka , wato auren shuka mai suna 'watermint' da turanci da kuma wata shukar mai suna 'spearmint'. Bincike ya nuna cewa na'a na'a tazo ne daga kasashen turawa da larabawa. Mutanen wadannan kasashen da muka ambata kanyi amfani da ganyen na'a-na'a cikin abinci da kuma wajen shayi, a matsayin ganyen-shayi (tea leaves) haka kuma, akwai man -na'a na'a ( peppermint oil) da ruwanta (peppermint water) a kasuwa domin amfani na daban-daban.
Bincike ya nuna cewa na'a-na'a nada amfani da yawa ga lafiyar dan adam. Wasu daga cikin amfaninta ga jikin mutum sune:
1. Tana magance matsalar bacin-ciki da rashin fitar bahaya maisa tsugunni
a bayi.
(Ayi shayin na'a-na'a ko azuba manta cikin shayi marar madara.)
2. Tana saukake narkewar abinci
3. Maganin tuka
4. Maganin gudawa
5. Maganin mura da tari [da kuma mura mai damun makoshi - wato 'sore throat']
(ayi amfani da man na'a-na'a ko ganyen , a tafasa ganyen ayi shayi marar madara
, haka kuma, za'a iya amfani da man na'a-na'a cikin ruwan zafi, ayi turiri,
a lullube da mayafi).
6. Maganin ciwon-kai ( a shafa manta wajen da kai ke ciwo).
7. Maganin ciwon-jiki ( a shafa manta ga jijiyoyin jiki dake ciwo
ko wajen dake damunka da ciwo, zata sanyaya, insha Allahu).
8. Maganin ciwon-hakori (ayi amfani da man na'a-na'a da auduga,
a diga man ga auduga , sa'annan a lika ga hakori mai ciwon).
9. Maganin kaikayi
10. Korar sauro ( a shafa man na'a-na'a ga jiki -
hannuwa da kafafu , sauro zai gujesu)
11. Kashe tsutsar ciki
12. Taimakawa hanta wajen aiki
13. Rage yawan damuwa
- tana sanyaya rai da hana damuwa
( a tafasa ganyen
na'a-na'a ayi shayi, ko manta a zuba cikin kofin shayi , safe da yamma).
14. Tana taimakawa kwalwa wajen rike karatu da
kaifin fahimta (ayi shayi da ganyen na'a-na'a a rinka sha da zuma).
15. Tana sanya girki yayi kamshi - filebo ( ayi amfani da ganyen wajen girki).
Hakan zai taimaka wajen son cin abincin (appetite), musamman ga wanda
baya son cin abinci.
16. Tana maganin ciwon-ciki , musamman ga mata masu matsalolin al'ada.
17. Da sauransu.

YADDA ZAKA RAGE CIN MB A WAYARKA KIRAR ANDROID

Duk mai amfani da wayar android, ya kwan da sanin kwasar MB balle kudi, wanda 10MB bata isar mai android yin facebook na 6hrs. Cin MB android yasa mutanan mu basa kaunatarta sosai, to ga yadda zaka rage mata barnar MB. Idan kana bukatar rage ma android naka cin MB, saika bi wadannan matakan. 1. Ka bude "Menu" na wayarka. 2. Sannan kaje "Settings". 3. Ka tafi can kasa, ka zabi "Account and sync settings" 4. Ka cire zabin da ke kan "Background data". Ka maida shi babu zabi, zasu yi maka gargadi, kawai ka manta da su, ka cire alamar zabi. Zaka samu saukin jan MB ga android naka cikin sauki, batare da tana daka wawa ba. Allah yasa mu dace.

ANFANIN MADARA GA JIKIN DAN ADAM

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan fili na kwalliya. Madara na dauke da sinadaren da ke saurin gyara fata.
Yawan bai wa yara madara na dada kaifin basira ga yaro.
Bayan haka, shan madara na sanya fata sulbi da laushe da kuma kare fata daga gautsi.

• A sami madara sannan a kwaba ayaba. A zuba ruwan madarar da ayabar ta dan yi kauri kadan sannan a rika shafawa a fuska
na tsawon minti goma sha biyar a rana sannan a wanke. Yin hakan na sanya sulbin fuska.
A sami madaran gari sannan a kwaba shi da ruwa sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sannan a gauraya a rika shafawa a
fuska kafin a shiga wanka a kullum domin samun hasken fata.

• Madara na goge dukanin daudar fuskar; za a iya samin rabin kofin madara sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke.
Bayan hakan, sai a shafa a fuska da wuya a jira na tsawon minti 2 zuwa 3 kafin a wanke da ruwan dumi.

• Madara na sanya fata sulbi domin hakane ya kamata a rika amfani da shi a matsayin cleanser ; a samo auduga sannan sai a tsoma a cikin madarar ruwa. Sai a rika goge fuskar da ita, sannan sai a jira ta bushe kafin a wanke, yin hakan na rage maikon fuska kuma da sanya fuska taushi da sulbi.

• Za a iya amfani da madara a gashi domin kara wa gashi lafiya. Musamman lokacin sanyi, gashi . Sai a zuba madara a gashi ya taba tsagun kai, sai a jira na dan minti
kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.
Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin hakan na hana fashewar fuska saboda sanyi.
*YADDA ZAKA KIRA LANBAR WATA KASAR CHIKIN KUDI MAI SAUKI*

assalamu alaikum barkanmu da warhaka ya ibada Allah yakarbi ibadummu amin🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲

Yau nazomana da yadda zaka kira lanbar wata kasar chikin kudi mai sauki saka makon wasu sunaso sukira lanbar wata kasar akwai wanda kakeso kakira mutum dayane ko sunada yawa amma farashin yai kudi dayawa hakan sai yakarya maka kwarin guywa wajen kasa kiran nasu

to sauki yazo maka sai kaduba achikin wa'innan kasashen in akwai daya daga chiki sai kaimin magana ta akwatin sakona nagaya maka yadda abin yake  amma kafinnan akwai abubuwan daya kamata ache kanadasu kafin kamori wannan damar sune kamar haka
👇👇👇👇👇👇👇
(1)wayarka yakasanche version 5 che zuwa sama

(2)yakasanche wayarka tana da 3g H+

(3)yakasanche inda kake akwai service din 3g h+

(4)yakasanche alokachi dazakayi kiran kanada data wachche zatayi komai

kuma shi wannan tsarin wanda kakeso kakira ba dole sai yanada wa'innan abubuwan dana zayyana ba, abinda kawai ake bukata shine kawai yakasanche layinshi yana kan Waya koda nokia mai fitalache

ga sunayen kasashen kamar haka
👇👇👇👇👇👇👇
Albania Algeria Argentina Australia Benin Brazil Cambodia Cameroon anadd Chile China Costa Rica Cyprus Ecuador EI Salvador Habasha Fiji Faransa Gambia Jamus Ghana Girka Guatemala Haiti Honduras Hong Kong Indonesia Italy Jamaica Japan Kenya Kuwait Malaysica Mexico Marokko Myanmar Nepal New Zealand Nicaragua Pakistarn Philippines Poland Portugal Puerto Rico Romania Saudi Arabia Singapore Afrika ta Kudu Koriya ta Kudu Spain i Lanka Taiwan Thailand Vietnam CTurkey Uganda Ƙasar Saudi Arabia United Kingdom America Vietnan

MUHIMMANCIN ILIMIN COMPUTER 2

Abun kamar almara. Dawo bangaren “na duke tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya taras” wato noma da kiwo, wadannan sana’o’i a wannan zamani za ka ga yadda na’urar Computer ta ke taimakawa wajen ganin inganci gona da abinda manomi zai shuka, da yadda ake yin taki, da yadda ake fitar da magungunan kwari, da dai makamantansu. A yau akwai Computoci wadanda suke sarrafa kayan gona, kamar irin computer da take tsotse ruwan jikin tumatiri ta kyafeshi a cikin dan kankanin lokaci, babu ruwanka da shanya da makamantansu. Idan kuwa muka zo bangaren kasuwanci, ai abin ba a cewa komai, ka duba hada-hada irin ta banki yadda abubuwa suka saukaka, a da, babu yadda za ka je wani banki ka ajiye kudi sannan kaje irin wannan banki ka cire kudinka, ballantana ace kaje wani gari ko kuma kaje wata kasa, ai babu hali. Amma a wannan zamani da ilimin computer ya yawaita, bama ka saka kudi a cikin account dinka ba, hatta saye da sayarwa za ka yi a duk inda kake so a duniya, kuma a kawo maka inda kake so, ba tare da kaje wurin ba, ko kayi magana dasu baki da baki ba, ta Computer za a gama komai, su nuna maka irin kayan da suke da su, da farashinsu, su kuma gaya maka idan har ka siya wadannan kaya kwana kaza za suyi daga kasa kaza zuwa kasa kaza. Koma ga kananan ‘yan kasuwanmu masu sayar da kayan taro da sisi sannan kuma masu son su kididdige cinikinsa, to, kaga abinda yafi dacewa da su itace Computer. Domin itace wacce komai yawan cinikin da akayi a rana ko shekara idan aka ce ta kawo lissafinsa za ta kawo ba tare da wani bata lokaci ba. Ba lissafi kadai za ta iya yi maka ba, hatta irin ribar da kake son ka samu zata fitar maka, zaka gaya mata kudin kaya, ka gaya mata kudin dako, ka gaya mata kudin abincinka da yaran shagonka, ka gaya mata adadin yawan kayan da ka siyo, ita kuma ta baka mamaki wajen fitar maka da taswirar yadda za ka sami cikakkiyar riba. Kai hatta abubuwan da ka siyar a baya ita Computer zata iya fitar maka da bayanai na ban mamaki, kamar ta gaya maka a shekaru talatin da ka ke kasuwanci shekara kaza kafi cin riba, sannan wata kaza kafi cin riba, sannan ta fitar maka da shekarar da kafi faduwa da rashin ciniki, sannan ta gaya maka kwastomanka da yafi kowa siyan kaya awurin ka da wanda ya siya kaya sau daya da sanda suka yi kasuwanci na karshe da abinda suka siya da kuma kudin da suka biya.


Sabo da haka, idan ka lura za ka ga cewar Computer wata makami ce da mutane suke amfani da ita wajen tafiyar da alamuransu na yau da kullum, sannan a wannan zamani da muke ciki a yanzu zai wahala dan adam yace zai gujewa amfani da Computer, domin na farko kusan mafi yawan mutane suna amfani da wayar tafi da gidanka (GSM), ga amfani da ATM wajen fito da kudi, da dai makamantansu, ballantana wanda yake da akwatin email, ko kuma yana amfani da dandali irin su Facebook ko twitter, ballantana wanda yake aikin jarida ko ma’aikacin asibiti da dai dukkan wanda rayuwarshi ta shafi harka da Computer. “Bama a nan gizo ke saka ba” ka duba yadda duk mutumin da yayi karatun zamani komai zurfin karatun da yayi sai ka ga ya hada da na Computer, kuma zai yi wahala ace mutum yana da ilimin Computer ko yaya yake yaje neman aiki ace ba a sa sunan shi a cikin wadanda za a tantance ba, musamman ace ya karanta wani fanni mai mahimmanci, ko kuma wata babbatar ma’aikatar da ta kera wani program ko hardware sun bashi shaidar cewar shi kwararre ne (Certification). Kamar mutumin da ya karanta fannin kasuwanci ya sami daraja ta biyu (Second Class) amma gashi ya iya amfani da Computer har yana da shaidar kwarewa akan Excel ko Peachtree wanda su wadannan software suna taimakawa wajen warware matsalar kasuwanci. To zai yi wahala yaje neman aiki ya zamanto ga wanda yake da daraja ta farko (First Class) amma bashi da wancan ilimin ace ba a dauke shi ba. Irin wadannan misalai suna da yawa, kamar mutumin da ya karanta fannin zane-zanen gidaje sannan ya zamanto bai iya amfani da computer ta fannin zane ba, kaga zai yi wahala a ce ga wanda ya karanta irin kwas na shi kuma ya san daya daga cikin program da ake zane dasu ace wancan aka dauka ba shi ba. To ashe idan har gaskiya ne Computer ta kewaye kusan ko ina a harkar mu ta yau da kullum, babu abinda ya fi dacewa illa mutum ya fahimci yadda zai sarrafa wacce yake tare da ita, ko da kuwa yaya kankantarta yake. Na san mutane da yawa ba da son ransu suke son a ce su kai aikin sirrinsu wajen Business Center ba, wajen da babu sirri, ba ka san waye zai karanta sirrinka ba, ga shi kuma kana da Computer a gida ko kuma a ofis amma abin bakin ciki ba ka iya sarrafa ta ba. Ka duba wani abin haushi “nama na jan kare” zaka samu hatta waya a wannan lokaci zaka ga mutane da yawa basu iya sarrafa ta ba, sai dai idan an turo musu da sako su kira wani ya duba musu. Bama wannan shine ya fi ban takaici ba, hatta ATM wanda ba a son wani ya san lambobinka guda hudu da kake amfani da su na sirri ka ciro kudi, sai kaga mutum duk sanda zai ciro kudi sai ya nemo wani sannan ya ciro mishi. Ashe idan haka ne ilimin sanin yadda zaka sarrafa Computer wajibi ne.

MUHIMMANCIN ILIMIN COMPUTER

Ko ba a gwada ba an san linzami yafi karfin bakin kaza, domin mahimmancin computer da iliminta ya wuce a ce mutum bai sani ba. Domin ko ba a fada maka ba lura da yadda ta mamaye kusan mafi yawanci abubuwan mu na yau da kullun. tun daga makarantunmu, ma’aikatunmu kasuwancinmu, asbitocinmu, gidajen yada labarai da makamantansu, dukkanin su za ka samu a na amfani da ita Computer.

Kusan a wannan zamani, computer ta samar da sauki wajen tafiyar da alamura ga dan adam. Kama daga rubutun takardar wasika zuwa takardar sanarwa ta wajen aiki ko takardar notice, takardar biyan albashi da lissafin kudaden kasa dayin kasafin kudi, hada da harkar hada- hada, da bayanai na kididdiga da fitar da kudade a bankuna, duk computer ta kawo sauki ta kowanne fanni.

Haka kuma computer ta samar da sauki wajen tafiyar da harkar banki, ka duba ATM yanda yake, computer take karbar cheque ko kuma ta baka kudi, ko kuma ta cireshi. Ga wadanda suke sayan kaya a kasashen waje suna amfani da computer wajen duba yanayin kayan su da kuma sannin a wane wuri kayan suke da kuma lokacin da kayan zasu iso. Ta bangaren kasuwanci, idan ka zuba wa computer bayanan harkar kasuwancin ka, kayan daka siyo, ka ware mata kudaden wahalhalunka, kama daga kudin abinci, kudin sallamar ma’aikata, kudin dauko kaya, kudin shago da kudin wuta za ta fitar maka da ribarka ko kuma faduwarka a dan kankanin lokaci.

Haka za ta iya a jiye maka wasu mahimman bayannanka bayan tsawo shekaru idan ka nemi ta fitar maka za ta fito maka da su. Haka da zamu koma wajen fanin kula da lafiya ana amfani da computer wajen binciko yanayin cuta da mazauninta a jikin dan adam, ba tare da likita ya tambaye shi ba, hakanan ana iya bincikar cikin da mace take dauke da shi a gane lafiyar shi ko rashin lafiyar shi da yanayin kwanciyar shi, duk a cikin dan kankanin lokaci. Dawo bangaren makarantu zaka samu suna amfani da computer wajen saukaka bincike da nazarin darussa ga yara. Sukan yi amfani da ita computer ta wajen kimiyya da fasaha don gano adadi da kididdiga. Ana samun na’ura da take dauke da muhimman takardu ga daliban fiye da dubu dari uku wanda zai yi wahala a sami wani laburari a karamar makaranta dake de littafi daban daban har dubu goma.

Ta hanyoyin sadarwa computer tana taimakawa gidajen jarida, da na watsa labarai wajen gyare gyaren tarin rubutu, video da sauti wanda a dan kankanin lokaci sai su gyara ayyukansu don watsawa don haka da taimakon computer ba sa bukatar sai sun shiga studio kafin su dauki bayanan da za su watsa. Haka nan sadarwa da aka samu ta yin amfani da wayoyin ta fi da gidanka(salula) za ka iya rabuta wasika ka aika, zaka iya aje alama ta tunatarwa, zaka iya daukar hoto ko video zaka iya yin lissafi da dai makamatansu ciki dan kankanin lokaci ba tare da wahala ba. Kasancewar ci gaban internet ya mamaye dukkan fannonin rayuwar dan adam a yau ba ta tafiya yadda ya kamata sai da internet ilimin computer shine sinadarin cin moriyar internet Idan kuwa muka duba bangaren tsaro, a zamanin da, zaka samu yana da wahala a gano file (kundin) na laifi da mutum yayi bayan an kai shi kotu, amma yanzu da zarar an saka bayanan shi, nan take za a samu, ka duba irin Computer da take bincikan ‘yan yatsu da fuskar wanda ake zargin shi da laifi, ko da yake yanzu ne aka fara irin wannan tsari a wannan kasa ta mu Najeriya.

Haka idan ka duba hatta cikin motoci da abubuwan hawa kamar jirgin sama, da jirgin kasa da jirgin ruwa za ka samu akwai computer a jikinsu, daga abinda yake sarrafa yanayin zafi ko sanyin abin hawa computer dake ciki take tafiyar da shi. Ballantana uwa uba ire-iren abubuwan hawa da ake kerowa na zamani a yanzu akwai motar da ake samun computer a cikin ta wacce duk inda wannan motar take a duniya za a iya kashe ta ko kuma a kunna ta, haka nan jirgin sama muna da labarin jirage irin na yaki wanda kasahen da suka ci gaba suke da su wadanda babu matuki a cikinsu, computer da ke ciki ita take sarrafa su, wanda ko da abokanen gaba sun harbo wannan jirgin to ba za a rasa rai ba. Computer ta kawo sauki ga masu ayyuka irin wanda a da sai an dauki tsawon lokaci ko kwanaki kafin ace an kammala su. Misali abin da ya shafi lissafin dukiya don fitar da gado an sami sauki mai yawa ,idan ka duba Computer da take rabon gado wanda duk abinda mutum ya mallaka komai yawansu, komai yawan wanda za su gaje shi, da zarar an gama zuba mata bayanan dukiyar da magadan sakon biyar yayi yawa ta gama raba wannan gado kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fadi ayi ba tare da ta rage wani abu ko ta karashi ga wani ba. Mu koma bangaren kere-kere shima Computer tana taka mahimmiyar rawa wajen kere- keren abubuwa wanda a zamanin da, sai an sami karti majiya karfi suke iya kera wannan abun. Idan muka koma harkar zane zane, yanzu an kai fagen da idan ka nuna fili kace ga girmanshi, kana son bishiya kaza, filawa kaza, kana kuma son mota irin kaza, ga irin fenti da kake so, ga irin kofofi da dai dukkan abinda za ka fadi da ya kamata a ganshi, kana gama lissafi wanda zai zana maka gidan yana kwafewa a ‘yar karamar takarda a hannunshi, da zarar ya gama zana gidan sai yayi amfani da daya daga cikin program na Computer ta gina wannan gida a cikin ta kamar yadda kace kana son, ka ganshi kamar da gaske babu wani abu da za ka ce ba na gaske bane, wanda idan kace kana son a bude maka cikin gidan kaga yadda kujeru da bayi da kayan kichin suke duka za ka gani. Kuma idan aka gama gina maka gidan na zahiri za ka ga babu bambanci tsakanin na cikin Computer da naka na waje.

YADDA ZAKA DAWO DA ABUBUWAN DAKA GOGE AKAN WAYARKA TA ANDROID

Kamar yadda wasun mu suka sani, computer tana da wani software mai suna (recycle bin). Ita ma wayar android tana da nata mai suna (dumpster). Shi wannan Application yana da Amfani kamar haka:- 1. Yana baka damar dawo da duk wani abu da ka goge, wanda ya kunshi Apps, audious, videos, folder, da sauran su. 2. A duk lokacin da ka goge abu zaka samu space a memory ka na adadin girman abunda ka goge. 3. Zaka iya sauraron audio da ka goge, ko kallon videon daka goge, ba tare da ka dawo dashi kan memoryn ka ba. 4. Duk abunda ka goge inka tashi dawo dashi zai dawo dashi cikin foldern da yake a Da. 5. Zaka iya goge abubuwa a memory ko a phone. 6. Yana amfani a rooted da unrooted android. Saide wannan Application yana cika, akwai adadin abuwan da yake dauka. domin sauko da wannan app din shiga wannan link din:- http://dumpster-recycle-bin.en.uptodown.com/ android/download Idan ka saqqo da shi saika bude shi za kaga arrow, saika danna arrown nan. Idan ka gama danna arrow din, zai fita (exit) da kanshi, in kuma bai fita ba saika fita da kanka. Sai ka kashe wayar ka sannan ka kunna ko kayi restart. Saika gwada goge abu, kaje ka bude wannan application din, zakaga abun da ka goge sai ka danna akan shi, za kaga abubuwa uku play, restore, delete. Restore shi ne dawo da abunda ka goge, delete kuma gogeshi kwata-kwata a wayar, play kuma shine kunna abun. Allah ya bada sa,a@

DUNIYA MAKARANTA

****Babu Abin da yake tabbas a duniya sai Canji. Komai ka gani a yau watarana zai canja daga yadda ka san shi. Komai yana canjawa ban da sarautar Allah.

****Ruwan gulbi da na teku duk ba su iya kashe wutar lahira. Amma hawayenka za su iya. Hawayen tsoron Allah ko na tausayin bayinsa su ke kashe wutar azabar Allah.

****Maganin ciwo haquri. Maganin wauta kawaici. Maganin gajiya bacci. Maganin matsala addu'a

****Kwaqwalwar mutum kamar lema ce. Ba ta aiki sai an bude ta.

****Ka riqe gaskiya, kada yawan mabiya ya rude ka. Shaidan ya fi kowa yawan
mabiya, amma ba za su hana shi shiga wuta ba.
Dr mansur sokoto

YAU MA KUNU ZA A SHA

Wata amarya ce aka kai ta dakinta. Aka dauki wani dan lokaci ‘yan uwanta suna zuwa suna taya ta girki. Daga bisani da suka rage sai ta fara yin girki da kanta.
Ango kuwa sai santi yake yi saboda dadin abincinta.
Watarana kawai sai ya so ya birge abokansa, ya nuna masu irin sa’ar mata da
ya yi wacce ta iya girki. Don haka sai ya sanar da ita tun da dare cewa, gobe da rana
zai zo da abokansa don su ci abinci a cikin gidansa.
Da aka wayi gari zai fita ya sake tuna mata cewa, yau fa akwai baqi. Sannan ya kawo kudin cefane ya ba ta, ya fita zuwa nasa sha’ani. Ita kuma saboda quruciya bayan da ta gama dama kunun safe sai ta kwanta ta yi ta bacci abinta. Tashin ta kawai sai ta ji ladan yana kiran sallar azahar. Kamar ba a yi komai ba sai ta share ta ci gaba da sha’aninta.
Jim kadan Ango ya shigo gida cikin murna da doki ya yi sallama ta amsa masa.
Sai kawai ya ga ta canja fuska. Lafiya kuwa? Ta ce, ba komai. Kin kammala aikin
abincin dai? “Ni fa kunu kawai na yi”. “Kunu”? Ta ce, “Eh, shi nake sha’awar sha”. Bai ce ma ta uffan ba, ya kada kai ya fita.
Amarya dai ta san ba ta yi daidai ba. Amma kuma tana jiran hukuncin da
maigida zai yanke mata. Amma kuma me zai iya yi a yanzu? Farawa da iyawa,
amarya da ragga! Da marece ya yi ta neme shi kudin cefane, sai ya ce “Ai kunu za mu sha”. A ranta ta ce, wannan kam ai ba komai. Ya ma fi sauqin damawa. Aka wayi gari aka sha kunu, da rana kunu, da dare ma kunu. Haka aka kwana uku duk sadda ta nemi kudin cefane sai ya ce ma ta “Ai kunu za mu sha”. Da ta gaji da haquri da shan kunu sai ta arce zuwa gidansu.
Da mahaifinta ya gan ta a gida sai abinya ba shi mamaki. Nan take ya buga ma mijinta waya yana tambayar sa ko lafiya ya kawo ta gida a yanzu? Ya ce, Baba ni ma ban san ta tafi ba. Amma dai ka ji ka ji yadda aka yi. Sai ya ce, to shikenan, ka bar ta kawai ba sai ka zo daukar ta ba. Da lokacin fitar sa ya yi sai uwargida ta nemi kudin cefane, sai ya ce “Ai gidan nan yau kunu za a sha”. Da yamma ma ya ce “Kunu za a sha”. Haka suka yi wasu kwana biyu tana shan kunu a gidan iyayenta bayan ta
kwana uku shi take sha a gidan mijinta. Da ta ga cewa, babu sarki sai Allah sai ta
sulale ta komawar ta gidan mijinta. Shi kuma sai ya yi kamar bai san akwai wani abu ba, ya yi maraba da ita, suka gaisa, sannan ya ce ta tashi ta dora masa ruwan zafi yana son zai sha kunu! Ai kuwa sai ta fashe da kuka. Sannan ta durqusa tana ba shi haquri tana roqon gafarar sa. Suka shirya, ba ta sake yin irin wancan ganganci ba.
Darussa:
- Akwai hanyoyi da yawa na magance matsala ba sai da fushi ko zagi ba.

- Maigida shi ne takobin daga. Idan babu hadin kansa gida ba zai yi kyau ba.

- Aure akwai dadi, amma fa in an dace da iyaye masu mutunci

Wednesday, 5 June 2019

DUNIYA MAKARANTA


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto

****Rayuwa tana ba ka wata dama a kullum sunan ta "Gobe". Abin da ya gagare ka a yau sai ka hari gobe da shi. Gobe ma rana ce.

****Kowane mutum yana da wani rubutu a goshinsa wanda ido bai ganin sa amma masu hankali suna karanta shi. Abin da aka rubuta shi ne: "Ka kula da ni. Ka ba ni muhimmanci". 

****Ka je duk inda kake so. Ka buya duk inda kake so. Amma kada ka manta komai dadewa sai ka tafi wajen Allah. A yau ake aiki, gobe ranar sakamako ce.
****Wasu mutane ba ka iya tuna farkon haduwar ka da su, amma sukan zama jigo a rayuwarka. Sanin Maza jari ne.

****Ka zama kai kadai ya fi kana tare da wanda bai dace ba. Nemi abokin kwarai.
Zama da madaukin kanwa shi ke sa farin kai. 

DUNIYA MAKARANTA

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto


****Mutum yakan shiga wani yanayi sai ya dauka cewa karshensa ya zo kenan. Amma daga bisani sai ya gane cewa, wannan shi ne farkon jin dadin sa a duniya. Da yawa kofar da kake zaton ta a kulle idan ka tura ta za ka same ta a bude tana jiran isowar ka. Kada ka yanke kauna daga alheri. In da rai da rabo.

****Yi kokari ka mayar da wuninka kyakkyawa duk halin da ka samu kanka a cikin
sa. Idan ka ki ko ka so za ka wuni a cikin sa.

****Magana mafificiya ita ce ambaton Allah. Kyauta mafificiya ita ce ka yi ma wani addu'a. Rana mafificiya ita ce wadda ba ka saba ma Allah ba a cikin ta.

****Ababe masu daraja ba su cika maimaituwa a rayuwar dan Adam ba. Shi ya sa kowane mutum uwa daya kacal gare shi


****Wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Wanda ya sa wani kuka Allah zai sa shi kuka. Duk wanda ya shuka alheri zai ga alheri a rayuwarsa da bayan mutuwar sa.
Idan kuwa ka shuka sharri to sharrin ne za ka girba komai dadewa.

DUNIYA MAKARANTA

****Mutunta Mutum ba ya nuna kana son sa. Amma yana nuna kana da Tarbiyya. Ba sai wanda ake so ake mutuntawa ba.


****Sau da yawa mutum yake murmushi amma ransa na cikin jin zafi. Domin ya yi
amanna cewa, bayan wuya sai dadi.


****Mai ba da haquri ba lalle ne ya zama mai laifi ba. Wani lokaci iya zama da jama'a ke sa ka ba su haquri alhalin ka fi su gaskiya.


****Wasu Manya a qasashen waje suke yin karatu. Idan ba su da lafiya a qasashen waje suke shan magani. A can ne kuma suke shan iska. Abu daya ne suke yi a cikin qasarsu, shi ne sata. Kishin qasa shi ma addini ne.


****A da, malamai ba su damu da abin duniya ba. Masu duniya na bin su da ita don neman iliminsu. A yau malamai ke bin masu duniya don neman ta daga wurin su.
Wannan ya sa masu duniya gudu su bar masu iliminsu.

DUNIYA MAKARANTA


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto
****Idan ka saki hawayenka a kan filo ka sake su a banza. Tashi ka kwarara su a tabarmar sallarka. Idan ka yi haka, ka kai kara wurin mai share maka su.
****Darasin da ya fi kowanne zafi a rayuwa shi ne sanin cewa, ba dukkan mutane ne suke son ka da alheri ba.

****Kada ka himmatu wajen yawaita abokai. Zabi na kirki ka manta da saura.
****Abu uku muna da buqatar su a kullum: Jarunta don canja abin da ake iya canjawa. Da Haquri don jure abin da ba a iya canjawa. Da Hikima don samar da canji mai ma'ana.
****Macce ta fi son ta zama mai kyau fiye da ta zama mai basira. Saboda maza sun fi amfani da idanunsu fiye da amfanin da suke yi da hankulansu

DUNIYAN MAKARANTA


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto

****Idan za ka aiki dan saqo kada ka aiki wawa. Nemi mai hankali da basira. Idan har ba ka samu ba, to ka je da kanka.

****Idan mutane suka guje ka a lokacin da ka shiga jarrabawar rayuwa to ka kwantar da hankalinka. Allah bai kore maka su ba sai don yana son ya ishe ka.

****Kada ka damu idan ka yi kuskure sannan ka gyara. Daga kurakuranka ne kake karanta rayuwar duniya. 
****Idan ka samu alheri, yi godiya. Idan sharri ya same ka, yi haquri. Idan ni'ima ta girma ya kamata godiyarta ta girma.

****Motsin da ya fi kowane sauqi gare ka shi ne motsa harshenka. Amma kuma ya fi kowane hatsari da cutarwa a gare ka idan ba ka kiyaye shi ba.

DUNIYAN MAKARANTA

*Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto*

****Ni'imomin duniya guda uku ne: Matar kwarai, da makwaucin kirki da da mai albarka.


****Damuwa kamar hadari ce. Idan ta kankama sai ruwa ya sauka.


****Idan ka mutu aka dauko ka ba za a kira ka da sunanka ba, sai dai ace a dauko janaza. Idan an sauke ka cikin kabari ba za a kira sunanka ba sai dai ace a kawo Mutum.
Daga nan sunanka ya vace sai dai a ce “Marigayi”.


****Duniya kamar ruwan teku ce. Duk ka kara sha za ka kara qishi.


****Wanda duk ba ka da buqata da shi tsaranka ne. Wanda kake da buqata da shi maigidanka ne. Wanda duk kake kyautata ma sa zai zamo kamar bawanka.

DUNIYA MAKARANTA

*Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto*

****Nasararka ba ita ce wadda mutane suke fadi ba. Babbar nasararka ita ce
kyakkyawan aikinka wanda Allah kadai ne ya san shi.


****Matsalarka ba ita ce wadda maqiyanka suke fadi ba. Babbar matsala a gare ka ita ce wadda ke tsakanin ka da Allah amma mutane ba su sani ba.


****Mamaki: Idan muka yi sadaka da Naira 500 sai mu gan su da yawa, amma idan muka je da su kasuwa sai su dawo yan kadan. Idan muka yi awa biyu muna ibada sai mu gan su da yawa, amma idan muka yi su a kallon movie ko wasar qwallo sai mu ga sun dawo ‘yan kadan. Idan muna addu'a sai mu kasa dadewa amma idan muna fira sai bakinmu ya bude sosai. Idan muna karanta Alqur’ani sai mu qosa nan take, amma idan
muna chatin sai mu rasa sanin inda lokaci ya tafi. Anya kuwa wannan ba alama ce ta raunin imaninmu ba? Aljanna fa akwai tsada. Mu sabunta imani.


****Yin abubuwa guda uku yana sa ayi wasu uku: Kallo yana sa ayi Zina, jayayya tana sa ayi fada, fushi yana sa ayi wauta.
****Kyauta tana kawo soyayya, kunya tana kawo alheri, tsafta tana ba da lafiya.


🎶 How to stop listening Music?
-----------------------------------
1. Make a sincere TAWBAH (repentance), ask Allah to help you, strength you and make you steadfast.
2. Delete all the songs from all your devices, and replace them with Quran recitation, Duas, Islamic lectures, Islamic apps, and Nasheeds.

3. Whenever you're about to listin to music, remind yourself that "ALLAH IS WATCHING ME"
Should I disobey my Lord by such a worthless sin, pleasing shaytaan?

4. Music leads one to go astray, distract him from the "REMEMBERANCE OF ALLAH"
Keep him thinking Haram, and takes him away from his Creator.

5. Remind yourself that: "MUSIC IS THE VOICE OF SHAYTAAN"
Just like water and oil do not mix, QURAN and music cannot stay in the same heart together. It's either the word of Allah or shaytaan.
YOU CHOOSE!

6. There is nothing more soothing and peaceful than the recitation of the Quran. And if you find calm in music then you know that you can NEVER find it.
How can we expect "PEACE, consolation and happiness"
Is something Allah has prohibited?

7." The least that can be said about Music is that listing to it is a sign of "FUSSAQ" (open sinners) "
"Music is the alcohol of the soul. "

8. As Prophet Muhammad ﷺ
said; "From among my followers there will be some people who will consider illegal sexual intrercourse, the wearing of silk, the drinking of alcoholic drinks and use of musical instruments, as LAWFUL. "

9. Allah has made everything crystal clear for us, now it's upon us whether we follow our desires or follow our lord. "The love for Allah is that when your heart wills to please Allah over your desires, even when the whole world is hell bent on displeasing Him. "

{Poultry Farming } Easy Investment You Can Start With Very Little Capital

Easy investment You can Start With very little Capital The high demand for chicken meat and eggs has really proven that Poultry farming in Nigeria is indeed a very lucrative business. The business of rearing of chicken and producing eggs for sale has created an opportunity for some
*Young graduates,
*Retired civil servants and
*others to earn regular income and also
provide employment for *countless number of Nigerians....
The major buyers of Chicken meat and eggs in the country are fast-food companies like
*Mr. Biggs,
*Tantalizer,
*Tasty-Fried Chicken and
*UAC followed by
*Hotels,
*Restaurants and
*Then the various house hold nationwide.
----------
A visit to any of the major markets will reveal to you that frozen chicken is still been
smuggled by some traders into Nigeria from neighboring countries like the republic of
Benin. The reason why this trend is prevalent is because most of the poultry farms in Nigeria operates on a small scale and can’t meet up with the increasing daily demand for chicken meat and eggs. So, if you are desirous of earning regular income with peace of mind, then investing in commercial poultry is the wisest business decision you can ever make.

YADDA AKE FARA KIWON KAJI


Fara kiwon kaji ba wani abu bane, amma noman kaji wani bangaren samun arziki ne na musamman. Zaka zama manomi, kuma zaka zama dan kasuwa, musamman idan ka tantance wani irin amfanin gona kake so ka girbe.

Sana’ar noman kaji ya kasu kashi biyu: ‘Yan kwai, wato kaji da ake kiwon su domin su samar da kwai, ko kuma ‘Yan nama wato brola, kaji na ci. Kowanne ka zaba, dolen-dole sai ka yanke shawarwari na shugabanci da kuma kasuwanci idan har kana so ka samu riba. Ga yadda zaka yi.

1. Ka rubuta tsarin sana’ar: Wannan shine fitilar da zai nuna maka hanyar da ka nufa a wannan sana’a. Duka shirin ka, da burin ka, da kuma yadda zaka cimma wannan buri na rubuce a wannan tsari. Wannan rubutu zai agaza maka wajen fahimtar yadda zaka tafiyar da sana’ar ka daga bangaren manomi, kana kuma daga bangaren ma’aikaci, kuma lauya da akanta duk zasu iya karanta wa su fahimci inda ka dosa.

2. Mallaki fili, jari da kayan aiki: Idan baka da wadannan abubuwa, babu yadda za’a yi kayi kiwon kaji har ka samu riba. Kana bukatar gidan da zaka zuba kajin a ciki, ya danganta da yadda kake so kayi. A cikin keji zaka zuba su, ko a fili zaka kyale su suyi ta yawo? Za kuma ka iya bukatar fili domin girbe abincin da zaka baiwa dabbobin. Kana bukatar kayan aiki domin shara, gyare-gyare da girbe amfanin gona.

3. Ka tantance wadanni irin kaji zaka girbe: To dama akwai kaji iri biyu da aka fi sani, da ‘yan kwai, da ‘yan nama. To akwai kuma wasu da ba’a jin su sosai, kamar kwan da ba’a ci, sai dai a kyankyashe su domin zama ‘yan kwai, ko ‘yan nama. Mafi yawancin lokuta, sana’ar kyakyasar kwai zaman kanta take yi, haka zalika kiwon ‘yan kananan kaji. Akwai kuma bangaren yanka kaji shima, idan har kana sha’awa. Akwai gonakin kaji masu yawa dake da bangarori da yawa.

4. Ka san me aka fi so a inda kake: Idan wajen da kake jama’a sun fi son kaji masu yawo a waje, ba a cikin keji ba, to gwamma ka mayar da hankali akan yadda zaka yi wannan kiwo a maimaikon na keji da ba’a sha’awa.

5. Ka gabatar da kanka ga kwastomomi da sauran jama’a: Ka tallata kanka ta hanyar sanar da su cewa kana sayar da kwai ko nama. Mafi yawancin lokuta, tallata abu da baki yafi rahusa kuma har yanzu shine hanya mafi tasiri wajen talla. Idan kana so, zaka iya biyan kudi a gidan radiyo ko jarida ko wata kafa a tallata sana’ar ka.

6. Ka rubuta duka tsare-tsaren kudi da yadda kudi ke shiga da fita: Kana bukatar wannan domin fahimtar ko kana samun riba, ko kuma a’a.

Tuesday, 4 June 2019

MANYAN APPS GUDA 5 DA SUKE BATAMA WAYA

Idan aka ce "APP" (APPLICATION) ko "APK" (Android Package Kit) shine abubuwan da wayar ANDROID take amfani da shi don saukake aiki da wayar wajen tafiya kai tsaye ga abinda kake so Ka sarrafa a wayarka, kuma ana sa shi a waya har ma ayi musanyansu daga waya zuwa waya.
Duk wayar ANDROID tana bukatar APK ko APPs don tafiyar da wayar, domin su ne za su taimakawa mai wayar wajen jin dadin amfani da wayar.
   Akwai APPs masu yawan gaske da mai ANDROID zai iya amfani da su kamar na GAME, MUSIC, SOCIAL MEDIA, BANKING, BROWSERS,  da dai sauransu masu yawa.
   Amma kuma bayan wadannan APPs masu amfani Ga mai ANDROID akwai wadanda suke ba su da amfani sosai, sai dai ma cutar da wayar maimakon amfanarwa.
   Wasu daga cikin wadannan APPs din suna cutar da waya kai tsaye, wasu kuma a hankali suke cutar da wayar ba tare da mai wayar ya sani ba, sai bayan ta samu matsala.
   Ga wasu daga cikinsu guda biyar kamar yadda bincike ya nuna:

(5) UC BROWSER
   UC BROWSER yana daya daga cikin shahararrun APPs da ake yawan amfani da su a wayar ANDROID. Play store ta nuna ya samu saukewa (download) fiye da miliyan 500, dalili kuwa bai wuce saurin sauke abu da yake yi, da kuma ci-gaba (acceleration) da yake da shi, da kuma kyakkyawan shafi mai tsari.
Bayan amfanin da yake da shi, akwai matsaloli kamar haka:
  -Yana daukar bayanai kamar contacts, SMS da location.
  -Ana tuhumarsu da sayar da bayanan sirri na mutanen da ke amfani da shi ga wasu mutane a waje, kamar IMEL, IMSI da wasu bayanan ga kamfanin ALIBABA ba tare da izinin mai wayar ba kuma babu tsaro (encryption).
 Ta dalilin haka kuwa bayananka za su fita waje ga wasu mutane da za su iya maka kutse (hacking), su sace password din Ka ba tare da Ka sani ba.

SHAWARATA... KA CIRE SHI, KAYI AMFANI DA WASU BROWSERS DIN (Banda Dolphin browser, domin shi ma akwai irin wannan zargin akansu).

(4) CLEAN MASTER
 Bayanai akan wannan zai bada mamaki, domin yana da "reviews" a play store wajen miliyan 43 (duk da akwai wasu kamfanonin APPs da ke biyan kudi don su samu review).
Shi wannan APP kamfaninsa yayi alkawarin zai taimakawa mai amfani da shi wajen shareware da goge abubuwan da ba su da amfani (junk files) a ma'adana (memory), da kuma da ba waya damar samu sarari (space), da kuma karin sauri wajen shiga yanar gizo (internet browsing).
   Matsalar da ake samu da shi ba wani na damuwa ba ce, sai dai duk ayyuka da yake yi sabbin wayoyin ANDROID suna dauke da shi, ba ka bukatar sai Ka saka APP mai yin irin wannan aikin.
Idan kana bukatar share ire-iren wadannan abubuwa marasa amfani, Ka shiga...Settings>Apps>Storage >Clear Cache.... Shi Kenan Ka samu lafiya.
   Bayan wannan kuma idan Ka kunna datarka, zai rika fito da wasu shafuka (ads) wadanda ba ka da alaka da su, sai dai su cinye maka datar kuma su hana wayarka sauri wajen shiga yanar gizo, kuma yana adana wadannan bayanai a cikin wayarka ba tare da ka sani ba, a boyeyyen wajen cikin ma'adanarka (memory).

SHAWARA TA... KA CIRE SHI 

(3) DU BATTERY SAVER
 Tun wajen shekarar 2012 aka kirkiro wannan APP din, kuma ya samu karbuwa sosai, domin yana da saukewa (downloading) fiye da miliyan 100.
Kuma masu APP din sun yi shi ne don ya taimaka wajen yin chajin batirin waya da sauri (fast charging), da kuma sanya waya yin sauri (speed). 
   Amma wannan duk yaudara ce kawai, domin abubuwan da ke sanya waya saurin chaji sune kamar haka:
  -Ya zamanto wayarka tana goyon bayan chaji da sauri (support fast charging)
  -Amfani da chaja mai sauri musamman wanda waya ta zo da shi.
 Amma babu wani APP da zai sa wayarka saurin chaji.
   Wata Marsala kuma ita ce, wannan APP din kodayaushe a bude take, wanda hakan na jawo shanye chajin waya maimakon ragewa, kuma yana amfani da datar wayarka in dai a bude take wajen fito da shafukan ba Ka gayyato su ba (ads) da za su iya sa wayarka saibi (slow) wajen bude yanar gizo.
    Magana ta gaskiya ita ce, duk wasu APPs da ke nuna za su taimaka maka wajen rage shan batir, ko sa wayarka sauri (speed), ko rage fili (space) a ma'adana (memory), ba su da amfani, domin duk wadannan tsarin an sanya su a yanzu tun daga kamfani.

SHAWARA TA.... KA CIRE SHI 


(2) ES FILE EXPLORER
Yayin wannan bincike na yi mamakin shigowar wannan APP cikin jerin masu matsala, ba don komai na sai don amfaninsa ga mai wayar ANDROID da kuma yadda mutane suka tasirantu da shi.
A wannan zamanin, sabbin wayoyi da ke fitowa sun zo da irin tsarin da wannan APP yake dauke da shi, ba Ka da bukatarshi a yanzu, Sai dai ya cike maka ma'adana (memory) kawai.
   Kamar yadda na gabatar akan wasu APPs din, shima akwai matsaloli kamar haka:
-Yana bullo shafuka (ads) da kanshi
-Yana tura bayanai ga wasu wurare ba tare da izini ba, wanda hakan na ba da dama ga masu kutse (hackers) su shiga su maka barna a wayarka.

Idan har Ka matsu da yin amfani da file manager app, to Ka yi amfani da "FILE GO" wanda kamfanin GOOGLE masu manhajar ANDROID suka kirkiro, ya fi inganci da kuma tsaro ga wayarka.

SHAWARA TA... KA CIRE SHI 


(1) ANTI VIRUS APPs
  Kusan duk APPs da ke da tsarin anti virus suna da mantsaloli da yawa fiye da amfanarwa. Ga shi kuma mutum da zarar ya sayi waya, tunanin farko ita ce sanya anti virus akan wayar. Abinda mutane ba su sani ba shine tsarin manhajar ANDROID (operating system) ta yi dabam da tsarin manhajar (windows) na'ura mai kwakwalwa (computer).
  Manhajar ANDROID ba ta bukatar anti virus don samun kariya da kuma tsaro ga wayar.
 Kusan duk APPs na anti virus sukan tambayi izini (permission), bayan an ba su, sukan samu cikekken dama (access) ga dukkan bayanai da ke cikin wayarka tun daga kan kira (calls), sakonni (messages), bayanan sauran APPs din da ke wayarka, da passwords, da kuma duk wasu ajiyayyen fayil (file) a wayarka, kuma sukan tura irin wadannan bayanai ga wasu kamfanoni ba tare da izinin mai wayar ba.
   Idan kana bukatar wayarka ta samu fili (space), kuma ta daina zafi (heat), saibi (delay) to Ka kauracewa irin wadannan APPs din na anti virus. Akwai APP a "GOOGLE PLAY STORE" mai suna "PLAY PROTECT FUNCTION", Ka sauke shi, Ka dora (install) a wayarka, da yardar Allah Ka samu tsaro mai inganci, domin masu manhajar ANDROID wato "GOOGLE" su suka kirkiro shi.


SHAWARA TA.... KA CIRE SHI...KA NEMI WANDA YA DACE.

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...