Ads

Thursday, 6 June 2019

HAKKOKIN MANZON ALLAH (SAWW) - ZAUREN FIQHU WHATSAAPP 1 & 3.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Salatin Allah da amincinsa su Qara tabbata abisa Na farko kuma Qarshen Manzanni.

Shugabanmu Annabi Muhammadu, tare da dukkan iyalan gidansa nutsuwar al'ummah, Da Sahabbansa taurarun shiriya.

Yau zamu ci gaba ne daga wajen da muka tsaya acikin Darasinmu mai taken:

HAKKOKIN MANZON ALLAH (saww).

Mun tsaya ne, Ko ince zamu tashi ne akan maganar sabanin da Malamai sukayi akan sanya Sunan Ma'aiki (saww) ko kuma sanya alkunya irin tasa (saww).

Idan ance "ALKUNYARSA" muna nufin lafazin "ABUL QASIMI".

Imam Sharfuddeen An-Nawawy (rahmatullahi alaihi) yace:

Malamai sunyi sabani akan halarci ko rashinsa dangane da sanya ALKUNYAR ABUL QASIMI har izuwa Mazhabobi 3.

1. MAZHABIN SHAFI'IYAH: Imam Muhammad bn Idrees Ash-Shafi'iy -Mai mazhabar kenan - (rah) yana cewa:

"Bai halatta ga wani mutum ya sanya ma kansa Alkunya da ABUL QASIM.

Sawa'un sunansa MUHAMMADU ne ko kuma wanu Sunan daban".

Ku lura fa, Imam Shafi'iy (ra) ya fadi haka ne domin KIYAYE MARTABAR MANZON ALLAH (SAWW) ba wai wani dalili daban ba.

Daga cikin Manyan Almajiran Imam Shafi'iy wadanda suka ruwaito wannan Qaulin daga gareshi kuma suka tafi akai, akwai Manyan Hafizan hadisi da kuma Fuqaha'u Irinsu:

• Imam Abubakrin Albaihaqiy.

• Abu Muhammad Albaqhwiy. (aduba cikin littafinsa Attahzeeb).

• Ibnu Asakira (mai shahararren littafin hadisin  nan na Tareekhu Damashqa).

2. MAZHABIN MALIKIYYAH : Imamu Malik (rah) yace:

"Ya halatta kowanne mutum yayi Alkunyah da Abul Qasim, ko sunansa MUHAMMAD ne, ko kuma wani Sunan daban".

Yace wannan hadisin da Ma'aiki (saww) yace "KU SANYA MA 'YA'YANKU SUNANA AMMA KAR KU SANYA ALKUNYAH NA" - wannan haramci ya tsaya ne kadai alokacin rayuwar Ma'aiki (saww).

3. HANAFIYYAH da HAMBALIYYAH : su kuma sunce:

"Ya halatta kowa ya sanya ALKUNYAH ta ABUL QASIM amma banda masu suna MUHAMMAD.

AL-IMAM ABUL QASIM ARRAFI'IY yace wannan ra'ayin shine mafi dacewa.

Ko ba komai idan aka duba za'a samu akwai Manya manyan Maluman Musulunci masu irin wannan Alkunyah din. Kuma irin wannan yana faruwa tun zamanin Sahabbai. Da ace wani abun haramci ne, da tuntuni an haramta.

Shima wancan hadisin da yazo da maganar hanawar, ya kebanci lokacin da Ma'aiki (saww) yake raye ne. Saboda Yahudawa sun kasance suna amfani da wannan damar domin cutar da Musulunci.

Aduba AL-AZKAR na Imam Nawawy, mujalladi na 1 shafi na 670.

ALQADHY IYADH BN MUSA (RAH) ya fada acikin littafin ASH-SHIFA cewa:

Allah ya ambaci Manzonsa (saww) acikin littafinsa da sunan  AHMADU da kuma MUHAMMADU. Sannan yana daga cikin abubuwan da Allah ya kebanceshi dasu cewa'
Kalmar Sunansa ma YABO ne agareshi (saww).

Kuma sunayensa sun tattaro Asraru na cikar godiya ga Allah.

Masanan harshen larabci suka ce:

Idan ka dauki kalmar  "AHMADU" zaka ga cewa "AF'ALU" ce. Wato tana nufin "KAIWA MUTUKA WAJEN GODIYA GA UBANGIJI".

Idan kuma ka dauki kalmar "MUHAMMADU" zaka ga cewa: Ita kuma "MUFA'ALUN" ce.

Wato tana nufin KAIWA MUBALAGHA (MAQURA) WAJEN YAWAITA GODIYA KO KUMA YABO GA UBANGIJI (SWT).

Insha Allahu gobe zamu dora daga nan inda muka tsaya.

YA ALLAH KA QARA MANA SON MANZON ALLAH (SAWW) DA TSANTSAR KOYI DA HALAYENSA DA AYYUKANSA, DA KUMA SON MASOYANSA.

Sallu alqn Nabiyyi wq sallimu tasleeman.

DAGA ZAUREN FIQHU (31/05/2014)

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...