Ads

Monday, 10 June 2019

ABOKIN HIRA


WATA BALARABIYA MAI FAHIMTA

Wannan ita kuma Balarabiya ce aka yi mai tsananin hankali da fahimta. Tana
tare da mijinta da ‘ya’yansu guda biyu Macce da Namiji. Akwai kuma surukarta;
mahaifiyar shi mijin nata a tare da su amma ta tsufa sosai, jiki ya yi rauni, gani ya
ragu. Saboda tsananin son da take yi ma dan nata sai ta riqa zaunar da shi domin su
yi labari amma shi ba ya fahimtar maganarta da kyau, kuma baya son irin labaran
da take kawowa. Al’adar larabawa a wancan lokaci kamar Fulani suke; yawo suke yi a cikin daji, su sauka nan yau, gobe su sauka can. Watarana sun yi niyyar tashi sai ya ce ma matarsa, ki shirya kayanki amma yau nan za mu bar Umma ta zauna nan ko za ta samu wasu da za su kula ta, ko kuma idan namun daji sun zo su cinye ta a huta.
Matar nan ba ta yi ma sa musu ba, kuma ta aiwatar da abin da ya ce, amma sai ta yi wata dabara.
Bai san abin da ke gudana ba sai da suka sauka a wani masauki gajiya ta lullube shi ta ko ina yana neman hutawa, sai ya tambaye ta dan karamin yaronsa kamar yadda ya saba don ya rungume shi yana debe masa kewa har sa’adda bacci ya kwashe shi. Sai ta ce ma sa ai na bar yaron a can tare da Umma. “Tare da Umma?”
“Ba ki da hankali ne”? In ji shi. A cikin ruwan sanyi sai ta ce, a’a. Ai gaskiya ba mu da
buqata da shi. A bar shi kawai wasu ma za su kula da shi, ko kuma idan namun daji sun zo su cinye shi a huta. Sai ya yi shiru bai sake cewa komai ba. Sannan ta ce ma sa shakka wannan yaron idan ya girma zai jefa ka ne a juji, ko ya bar ka a tsohon
masauki don Kura da Damisa su cinye ka. A nan ne fa hankalinsa ya dawo ma sa. Bai sake cewa uffan ba, sai ya manta gajiya, ya ruga ya koma masaukinsu na farko in da tsohuwa da yaronsa suke. Isar sa ke da wuya sai ya tarar da tsohuwa rungume da jikanta tana yi ma sa wasa cikin nishadi da jin daxi. Ya karbi yaro ya sunbace shi,
sannan ya tashi tsohuwa ya riqa hannunta suka dawo zuwa sabon masauki.

Darussa:
- Iyaye ba abin wasa ba ne

- Duk abin da ka yi ma iyayenka shi ne ‘ya’yanka za su yi maka

- Macce ta gari jigon gida ce

 Dr. Mansur Sokoto

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...