Ads

Wednesday, 5 June 2019

DUNIYA MAKARANTA


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto

****Rayuwa tana ba ka wata dama a kullum sunan ta "Gobe". Abin da ya gagare ka a yau sai ka hari gobe da shi. Gobe ma rana ce.

****Kowane mutum yana da wani rubutu a goshinsa wanda ido bai ganin sa amma masu hankali suna karanta shi. Abin da aka rubuta shi ne: "Ka kula da ni. Ka ba ni muhimmanci". 

****Ka je duk inda kake so. Ka buya duk inda kake so. Amma kada ka manta komai dadewa sai ka tafi wajen Allah. A yau ake aiki, gobe ranar sakamako ce.
****Wasu mutane ba ka iya tuna farkon haduwar ka da su, amma sukan zama jigo a rayuwarka. Sanin Maza jari ne.

****Ka zama kai kadai ya fi kana tare da wanda bai dace ba. Nemi abokin kwarai.
Zama da madaukin kanwa shi ke sa farin kai. 

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...