Ads

Tuesday, 4 June 2019

MANYAN APPS GUDA 5 DA SUKE BATAMA WAYA

Idan aka ce "APP" (APPLICATION) ko "APK" (Android Package Kit) shine abubuwan da wayar ANDROID take amfani da shi don saukake aiki da wayar wajen tafiya kai tsaye ga abinda kake so Ka sarrafa a wayarka, kuma ana sa shi a waya har ma ayi musanyansu daga waya zuwa waya.
Duk wayar ANDROID tana bukatar APK ko APPs don tafiyar da wayar, domin su ne za su taimakawa mai wayar wajen jin dadin amfani da wayar.
   Akwai APPs masu yawan gaske da mai ANDROID zai iya amfani da su kamar na GAME, MUSIC, SOCIAL MEDIA, BANKING, BROWSERS,  da dai sauransu masu yawa.
   Amma kuma bayan wadannan APPs masu amfani Ga mai ANDROID akwai wadanda suke ba su da amfani sosai, sai dai ma cutar da wayar maimakon amfanarwa.
   Wasu daga cikin wadannan APPs din suna cutar da waya kai tsaye, wasu kuma a hankali suke cutar da wayar ba tare da mai wayar ya sani ba, sai bayan ta samu matsala.
   Ga wasu daga cikinsu guda biyar kamar yadda bincike ya nuna:

(5) UC BROWSER
   UC BROWSER yana daya daga cikin shahararrun APPs da ake yawan amfani da su a wayar ANDROID. Play store ta nuna ya samu saukewa (download) fiye da miliyan 500, dalili kuwa bai wuce saurin sauke abu da yake yi, da kuma ci-gaba (acceleration) da yake da shi, da kuma kyakkyawan shafi mai tsari.
Bayan amfanin da yake da shi, akwai matsaloli kamar haka:
  -Yana daukar bayanai kamar contacts, SMS da location.
  -Ana tuhumarsu da sayar da bayanan sirri na mutanen da ke amfani da shi ga wasu mutane a waje, kamar IMEL, IMSI da wasu bayanan ga kamfanin ALIBABA ba tare da izinin mai wayar ba kuma babu tsaro (encryption).
 Ta dalilin haka kuwa bayananka za su fita waje ga wasu mutane da za su iya maka kutse (hacking), su sace password din Ka ba tare da Ka sani ba.

SHAWARATA... KA CIRE SHI, KAYI AMFANI DA WASU BROWSERS DIN (Banda Dolphin browser, domin shi ma akwai irin wannan zargin akansu).

(4) CLEAN MASTER
 Bayanai akan wannan zai bada mamaki, domin yana da "reviews" a play store wajen miliyan 43 (duk da akwai wasu kamfanonin APPs da ke biyan kudi don su samu review).
Shi wannan APP kamfaninsa yayi alkawarin zai taimakawa mai amfani da shi wajen shareware da goge abubuwan da ba su da amfani (junk files) a ma'adana (memory), da kuma da ba waya damar samu sarari (space), da kuma karin sauri wajen shiga yanar gizo (internet browsing).
   Matsalar da ake samu da shi ba wani na damuwa ba ce, sai dai duk ayyuka da yake yi sabbin wayoyin ANDROID suna dauke da shi, ba ka bukatar sai Ka saka APP mai yin irin wannan aikin.
Idan kana bukatar share ire-iren wadannan abubuwa marasa amfani, Ka shiga...Settings>Apps>Storage >Clear Cache.... Shi Kenan Ka samu lafiya.
   Bayan wannan kuma idan Ka kunna datarka, zai rika fito da wasu shafuka (ads) wadanda ba ka da alaka da su, sai dai su cinye maka datar kuma su hana wayarka sauri wajen shiga yanar gizo, kuma yana adana wadannan bayanai a cikin wayarka ba tare da ka sani ba, a boyeyyen wajen cikin ma'adanarka (memory).

SHAWARA TA... KA CIRE SHI 

(3) DU BATTERY SAVER
 Tun wajen shekarar 2012 aka kirkiro wannan APP din, kuma ya samu karbuwa sosai, domin yana da saukewa (downloading) fiye da miliyan 100.
Kuma masu APP din sun yi shi ne don ya taimaka wajen yin chajin batirin waya da sauri (fast charging), da kuma sanya waya yin sauri (speed). 
   Amma wannan duk yaudara ce kawai, domin abubuwan da ke sanya waya saurin chaji sune kamar haka:
  -Ya zamanto wayarka tana goyon bayan chaji da sauri (support fast charging)
  -Amfani da chaja mai sauri musamman wanda waya ta zo da shi.
 Amma babu wani APP da zai sa wayarka saurin chaji.
   Wata Marsala kuma ita ce, wannan APP din kodayaushe a bude take, wanda hakan na jawo shanye chajin waya maimakon ragewa, kuma yana amfani da datar wayarka in dai a bude take wajen fito da shafukan ba Ka gayyato su ba (ads) da za su iya sa wayarka saibi (slow) wajen bude yanar gizo.
    Magana ta gaskiya ita ce, duk wasu APPs da ke nuna za su taimaka maka wajen rage shan batir, ko sa wayarka sauri (speed), ko rage fili (space) a ma'adana (memory), ba su da amfani, domin duk wadannan tsarin an sanya su a yanzu tun daga kamfani.

SHAWARA TA.... KA CIRE SHI 


(2) ES FILE EXPLORER
Yayin wannan bincike na yi mamakin shigowar wannan APP cikin jerin masu matsala, ba don komai na sai don amfaninsa ga mai wayar ANDROID da kuma yadda mutane suka tasirantu da shi.
A wannan zamanin, sabbin wayoyi da ke fitowa sun zo da irin tsarin da wannan APP yake dauke da shi, ba Ka da bukatarshi a yanzu, Sai dai ya cike maka ma'adana (memory) kawai.
   Kamar yadda na gabatar akan wasu APPs din, shima akwai matsaloli kamar haka:
-Yana bullo shafuka (ads) da kanshi
-Yana tura bayanai ga wasu wurare ba tare da izini ba, wanda hakan na ba da dama ga masu kutse (hackers) su shiga su maka barna a wayarka.

Idan har Ka matsu da yin amfani da file manager app, to Ka yi amfani da "FILE GO" wanda kamfanin GOOGLE masu manhajar ANDROID suka kirkiro, ya fi inganci da kuma tsaro ga wayarka.

SHAWARA TA... KA CIRE SHI 


(1) ANTI VIRUS APPs
  Kusan duk APPs da ke da tsarin anti virus suna da mantsaloli da yawa fiye da amfanarwa. Ga shi kuma mutum da zarar ya sayi waya, tunanin farko ita ce sanya anti virus akan wayar. Abinda mutane ba su sani ba shine tsarin manhajar ANDROID (operating system) ta yi dabam da tsarin manhajar (windows) na'ura mai kwakwalwa (computer).
  Manhajar ANDROID ba ta bukatar anti virus don samun kariya da kuma tsaro ga wayar.
 Kusan duk APPs na anti virus sukan tambayi izini (permission), bayan an ba su, sukan samu cikekken dama (access) ga dukkan bayanai da ke cikin wayarka tun daga kan kira (calls), sakonni (messages), bayanan sauran APPs din da ke wayarka, da passwords, da kuma duk wasu ajiyayyen fayil (file) a wayarka, kuma sukan tura irin wadannan bayanai ga wasu kamfanoni ba tare da izinin mai wayar ba.
   Idan kana bukatar wayarka ta samu fili (space), kuma ta daina zafi (heat), saibi (delay) to Ka kauracewa irin wadannan APPs din na anti virus. Akwai APP a "GOOGLE PLAY STORE" mai suna "PLAY PROTECT FUNCTION", Ka sauke shi, Ka dora (install) a wayarka, da yardar Allah Ka samu tsaro mai inganci, domin masu manhajar ANDROID wato "GOOGLE" su suka kirkiro shi.


SHAWARA TA.... KA CIRE SHI...KA NEMI WANDA YA DACE.

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...