Ads

Thursday, 6 June 2019


YAU MA KUNU ZA A SHA

Wata amarya ce aka kai ta dakinta. Aka dauki wani dan lokaci ‘yan uwanta suna zuwa suna taya ta girki. Daga bisani da suka rage sai ta fara yin girki da kanta.
Ango kuwa sai santi yake yi saboda dadin abincinta.
Watarana kawai sai ya so ya birge abokansa, ya nuna masu irin sa’ar mata da
ya yi wacce ta iya girki. Don haka sai ya sanar da ita tun da dare cewa, gobe da rana
zai zo da abokansa don su ci abinci a cikin gidansa.
Da aka wayi gari zai fita ya sake tuna mata cewa, yau fa akwai baqi. Sannan ya kawo kudin cefane ya ba ta, ya fita zuwa nasa sha’ani. Ita kuma saboda quruciya bayan da ta gama dama kunun safe sai ta kwanta ta yi ta bacci abinta. Tashin ta kawai sai ta ji ladan yana kiran sallar azahar. Kamar ba a yi komai ba sai ta share ta ci gaba da sha’aninta.
Jim kadan Ango ya shigo gida cikin murna da doki ya yi sallama ta amsa masa.
Sai kawai ya ga ta canja fuska. Lafiya kuwa? Ta ce, ba komai. Kin kammala aikin
abincin dai? “Ni fa kunu kawai na yi”. “Kunu”? Ta ce, “Eh, shi nake sha’awar sha”. Bai ce ma ta uffan ba, ya kada kai ya fita.
Amarya dai ta san ba ta yi daidai ba. Amma kuma tana jiran hukuncin da
maigida zai yanke mata. Amma kuma me zai iya yi a yanzu? Farawa da iyawa,
amarya da ragga! Da marece ya yi ta neme shi kudin cefane, sai ya ce “Ai kunu za mu sha”. A ranta ta ce, wannan kam ai ba komai. Ya ma fi sauqin damawa. Aka wayi gari aka sha kunu, da rana kunu, da dare ma kunu. Haka aka kwana uku duk sadda ta nemi kudin cefane sai ya ce ma ta “Ai kunu za mu sha”. Da ta gaji da haquri da shan kunu sai ta arce zuwa gidansu.
Da mahaifinta ya gan ta a gida sai abinya ba shi mamaki. Nan take ya buga ma mijinta waya yana tambayar sa ko lafiya ya kawo ta gida a yanzu? Ya ce, Baba ni ma ban san ta tafi ba. Amma dai ka ji ka ji yadda aka yi. Sai ya ce, to shikenan, ka bar ta kawai ba sai ka zo daukar ta ba. Da lokacin fitar sa ya yi sai uwargida ta nemi kudin cefane, sai ya ce “Ai gidan nan yau kunu za a sha”. Da yamma ma ya ce “Kunu za a sha”. Haka suka yi wasu kwana biyu tana shan kunu a gidan iyayenta bayan ta
kwana uku shi take sha a gidan mijinta. Da ta ga cewa, babu sarki sai Allah sai ta
sulale ta komawar ta gidan mijinta. Shi kuma sai ya yi kamar bai san akwai wani abu ba, ya yi maraba da ita, suka gaisa, sannan ya ce ta tashi ta dora masa ruwan zafi yana son zai sha kunu! Ai kuwa sai ta fashe da kuka. Sannan ta durqusa tana ba shi haquri tana roqon gafarar sa. Suka shirya, ba ta sake yin irin wancan ganganci ba.
Darussa:
- Akwai hanyoyi da yawa na magance matsala ba sai da fushi ko zagi ba.

- Maigida shi ne takobin daga. Idan babu hadin kansa gida ba zai yi kyau ba.

- Aure akwai dadi, amma fa in an dace da iyaye masu mutunci

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...