Ads

Saturday, 8 June 2019

ABOKIN HIRA


KISHIYA BAYAN MUTUWA

Wani mutum ne suna zaune suna tadi da matarsa sai kawai ta tambaye shi,
yaushe ne za ka yi aure idan na mutu? Sai ya yi murmushi, ya ce ma ta, ba zan yi aure
ba sai qabarinki ya bushe. Ta ce, ka yi ma ni alqawarin haka? Sai ya ce, eh.
A kwana a tashi ajali ya cim ma matarsa, ta yi jinya kadan sannan ta ce ga garinku. Da aka zo jana’izarta sai ya tuna da alqawarin da ya yi ma ta. Don haka bayan sati daya duk sai ya je ya ziyarci qabarinta ya yi ma ta addu’a. Amma abin ban mamaki shi ne a kullum in ya zo sai ya tarar da qabarinta danye kamar jiya ne aka binne ta. Sai da aka yi shekaru yana haka, rannan sai ya yi kicibis da qanenta ya zo maqabartar da ruwa a jarka. Ya ce, me za ka yi ne halan? Ya ce, ina zartar da wasiyyar ‘yar uwata ne. Ya ce, me ta yi maka wasici da shi ne? Ya ce, ai ta roqe ni ne bayan kowane kwana biyu in kwarara ruwa a qabarinta.

Darasi: Kishi kumallon mata, ko suna kabari suna jin zafin sa. Mu tausaya masu
Dr. Mansur sokoto

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...