Ads

Friday, 7 June 2019

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA DR GUMI !!


#DR#IBRAHIM_DISINA_(HAFIZAHULLAH)
Da fatan ka tashi lafiya, Yaya Iyalai? Allah ya kareka da kariyarka ya fadada kirjinka don fahimtar sakon dan almajiri .
Malam ,
Allah ya jikan Sheikh Abubakar Gumi, tsawon rayuwarsa abinda ke bude karatun littafin Bukari da shi shine : `` karatun hadisi da aiki da shi shine zaman lafiyar musulmai´´
Abin mamaki ne kwarai ga Malamin da ke danganta kansa da Sunnar Annabi amma ka sameshi lokaci bayan lokaci yana wurgi da maganar Annabi sallallahu alaihi wasallam! Bayan Allah ya ambata cikin Alqur`ani cew: du wanda bai mika wuya gaba daya ga matsayar annabi kan lamura ba (Sunnah) ba, baiyi imani na gaskiya baa.
Fuskar Dr gumi da yanayin shigarsa da kujerar da ke gabatar da darasi, da yana martaba dukkan maganganun Annabi da ya fi kwarjini!
Hadisin Sittusshawwal dai ingantacce ne Abu dawud, Tirmizy, ibn Hibban kai har ya shigo daya daga cikin mafi ingancin littafi; Sahihu muslim, Sahabin da ya rawaiceshi kuma shine mai masaukin Manzon Allah a garin madina Abu Ayyubal ansary Khalid bn Zaid bn Kulaib (Haladu farin tsoho na madina) da yaron gidan Manzon Allah Thauban dss.Hadisin dai ingantacce ne!!
Ko iya nan kadai aka tsaya bai kamata, a sanya maganar wani ko da sahabi ne tayi gogayya da maganar Annabi ba, Ballantana ma, Manyan Malaman malikiyya cikinsu har wanda ya fi kowa yiwa Littafin da Dr ya ciro maganar Malik cikinsa(muwadda) Wato Ibn Abdulbarr Annumary yace Imam Malik ba karan tsaye ya ke yiwa Hadisin Sittushshwal ba, domin ba yanda Malik zai yi haka, Wanda shi ke cewa : ``Ko bayansa in hadisi ya inganta shine fahimtarsa´´ sannan hadisin mabubbuarsa garin madina ne ace malik bai sanshi baa.
Rashin kyamatar azimin situshshawal itace fahimtar mayan Malaman Malikiyya tare da dora zance malik kan manufarsa ta gaskiya, Wannan kuma ba sabon abu bane cikin shari`ar Musulunci ta dakatar da mutane da tsaresu kan wani aikin da yake daidai ne bisa asali amma saboda gudun takurawa mutane ko lokaci baiyi ba da za su fahimta sai a barshi zuwa lokacin da tsoron hakan ya gushe;
(1) Annabi ya guji dorawa mutane yin Aswaki kowace sallah duk da hakan sunnah ne!
(2) Ya guji rushe Ka`aba da ginata kan tushenta na zamani Annabi Ibrahim gudun mai zai je ya zo!
(3) Kin da annabi yayi na ci gaba da fitowa Sallar Tarawiy don gudun kar a maidawa mutan ta zamo tilas.
Imam Malik tsoronsa gudun kar wassu su dauka yana cikin Ramalana, Wannan kuma ba shi kadai ne ya tsoraci haka baa, Abu Yusuf dalibin Abu hanifa shima ya fahimci haka, suma a mazhabar Hanafiyya sun nemi turashicikin tsakiyarbwatan shawwal da rashin azumtarsa daf bayan kammala ramalana don a banbanceshi daga Ramadan, irin wannan aka ambata a ruwayar da Ibnu Mubarak ya yiwa Hadisin, Amma duk Malaman har Imam Malik ba wanda ya ce Bidi`a ce sai Dr Gumi, Wanda bana ganin yana jin yafi sauran malaman Nigeria fahimtar Malikiyya balle manyan malamai da wassu sun kusa shekara dubu da rasuwa irinsu Ibnu Abdulbarr wandanda suka bawa maganar malik ma`ana mai kyau!!
Abin tausayi ne ace ka zamo munbarin fada da Hadisan Annabi, Sai mutum ya kasa fahimtar inda malamin ya dosa? Tarihi ya tabbatar duk mai fada da Hadisan annabi baya kammalawa Lafiya, Mahmood abu Rayya a wannan zamani abin daukar izina ce!
Abu Rayyah da ya rubuta littafi don karyata Hadisai, karshen a bandaki ya mutu a wulakance, Sannan ofishin jakadancin Iran a kasashe daban daban su ke raba littatafansa kyauta duk da bai shiga shia`a baa, Hakannan yau Makiya sahabban Annabi su suka fi kowa tallata zancen Dr Gumi, Manufarsu sa shakku ga gabadayan Hadisan Annabi. Ina fatan kar makiya Sunnah su ringa fakewa bayan katobararka don yakar Sunnar Annabi.
Gaskiya ne a nesanta yin situshshawal daga zarar kammala ramadan don kar wassu su zaci har yanzu ana Ramadan ne , Amma wanda ya tantance ya yi azuminsa don a rubuta masa kamar shekara yayi yana Azumi, wannan kamar yadda ba a yiwa Ramadan tare haka kar a yi masa rakiya!!
A karshe shi fa Imam Malik din ya na azumtar situshshawwal a karan kansa kamar yadda dan kanwarsa kuma almajirinsa Mudarrif Ibn Abdullahi bn Mudarrif bn Sulaiman Alhilaly ya rawaito kamar yanda malamai da yawa suka ambata cikinsu akwai Alqurduby cikin Almufhim da Bajy a Almuntaqa.
Ibrahim Disina

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...