Ads

Thursday, 6 June 2019

MUHIMMANCIN ILIMIN COMPUTER 2

Abun kamar almara. Dawo bangaren “na duke tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya taras” wato noma da kiwo, wadannan sana’o’i a wannan zamani za ka ga yadda na’urar Computer ta ke taimakawa wajen ganin inganci gona da abinda manomi zai shuka, da yadda ake yin taki, da yadda ake fitar da magungunan kwari, da dai makamantansu. A yau akwai Computoci wadanda suke sarrafa kayan gona, kamar irin computer da take tsotse ruwan jikin tumatiri ta kyafeshi a cikin dan kankanin lokaci, babu ruwanka da shanya da makamantansu. Idan kuwa muka zo bangaren kasuwanci, ai abin ba a cewa komai, ka duba hada-hada irin ta banki yadda abubuwa suka saukaka, a da, babu yadda za ka je wani banki ka ajiye kudi sannan kaje irin wannan banki ka cire kudinka, ballantana ace kaje wani gari ko kuma kaje wata kasa, ai babu hali. Amma a wannan zamani da ilimin computer ya yawaita, bama ka saka kudi a cikin account dinka ba, hatta saye da sayarwa za ka yi a duk inda kake so a duniya, kuma a kawo maka inda kake so, ba tare da kaje wurin ba, ko kayi magana dasu baki da baki ba, ta Computer za a gama komai, su nuna maka irin kayan da suke da su, da farashinsu, su kuma gaya maka idan har ka siya wadannan kaya kwana kaza za suyi daga kasa kaza zuwa kasa kaza. Koma ga kananan ‘yan kasuwanmu masu sayar da kayan taro da sisi sannan kuma masu son su kididdige cinikinsa, to, kaga abinda yafi dacewa da su itace Computer. Domin itace wacce komai yawan cinikin da akayi a rana ko shekara idan aka ce ta kawo lissafinsa za ta kawo ba tare da wani bata lokaci ba. Ba lissafi kadai za ta iya yi maka ba, hatta irin ribar da kake son ka samu zata fitar maka, zaka gaya mata kudin kaya, ka gaya mata kudin dako, ka gaya mata kudin abincinka da yaran shagonka, ka gaya mata adadin yawan kayan da ka siyo, ita kuma ta baka mamaki wajen fitar maka da taswirar yadda za ka sami cikakkiyar riba. Kai hatta abubuwan da ka siyar a baya ita Computer zata iya fitar maka da bayanai na ban mamaki, kamar ta gaya maka a shekaru talatin da ka ke kasuwanci shekara kaza kafi cin riba, sannan wata kaza kafi cin riba, sannan ta fitar maka da shekarar da kafi faduwa da rashin ciniki, sannan ta gaya maka kwastomanka da yafi kowa siyan kaya awurin ka da wanda ya siya kaya sau daya da sanda suka yi kasuwanci na karshe da abinda suka siya da kuma kudin da suka biya.


Sabo da haka, idan ka lura za ka ga cewar Computer wata makami ce da mutane suke amfani da ita wajen tafiyar da alamuransu na yau da kullum, sannan a wannan zamani da muke ciki a yanzu zai wahala dan adam yace zai gujewa amfani da Computer, domin na farko kusan mafi yawan mutane suna amfani da wayar tafi da gidanka (GSM), ga amfani da ATM wajen fito da kudi, da dai makamantansu, ballantana wanda yake da akwatin email, ko kuma yana amfani da dandali irin su Facebook ko twitter, ballantana wanda yake aikin jarida ko ma’aikacin asibiti da dai dukkan wanda rayuwarshi ta shafi harka da Computer. “Bama a nan gizo ke saka ba” ka duba yadda duk mutumin da yayi karatun zamani komai zurfin karatun da yayi sai ka ga ya hada da na Computer, kuma zai yi wahala ace mutum yana da ilimin Computer ko yaya yake yaje neman aiki ace ba a sa sunan shi a cikin wadanda za a tantance ba, musamman ace ya karanta wani fanni mai mahimmanci, ko kuma wata babbatar ma’aikatar da ta kera wani program ko hardware sun bashi shaidar cewar shi kwararre ne (Certification). Kamar mutumin da ya karanta fannin kasuwanci ya sami daraja ta biyu (Second Class) amma gashi ya iya amfani da Computer har yana da shaidar kwarewa akan Excel ko Peachtree wanda su wadannan software suna taimakawa wajen warware matsalar kasuwanci. To zai yi wahala yaje neman aiki ya zamanto ga wanda yake da daraja ta farko (First Class) amma bashi da wancan ilimin ace ba a dauke shi ba. Irin wadannan misalai suna da yawa, kamar mutumin da ya karanta fannin zane-zanen gidaje sannan ya zamanto bai iya amfani da computer ta fannin zane ba, kaga zai yi wahala a ce ga wanda ya karanta irin kwas na shi kuma ya san daya daga cikin program da ake zane dasu ace wancan aka dauka ba shi ba. To ashe idan har gaskiya ne Computer ta kewaye kusan ko ina a harkar mu ta yau da kullum, babu abinda ya fi dacewa illa mutum ya fahimci yadda zai sarrafa wacce yake tare da ita, ko da kuwa yaya kankantarta yake. Na san mutane da yawa ba da son ransu suke son a ce su kai aikin sirrinsu wajen Business Center ba, wajen da babu sirri, ba ka san waye zai karanta sirrinka ba, ga shi kuma kana da Computer a gida ko kuma a ofis amma abin bakin ciki ba ka iya sarrafa ta ba. Ka duba wani abin haushi “nama na jan kare” zaka samu hatta waya a wannan lokaci zaka ga mutane da yawa basu iya sarrafa ta ba, sai dai idan an turo musu da sako su kira wani ya duba musu. Bama wannan shine ya fi ban takaici ba, hatta ATM wanda ba a son wani ya san lambobinka guda hudu da kake amfani da su na sirri ka ciro kudi, sai kaga mutum duk sanda zai ciro kudi sai ya nemo wani sannan ya ciro mishi. Ashe idan haka ne ilimin sanin yadda zaka sarrafa Computer wajibi ne.

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...