Ads

Wednesday, 5 June 2019

YADDA AKE FARA KIWON KAJI


Fara kiwon kaji ba wani abu bane, amma noman kaji wani bangaren samun arziki ne na musamman. Zaka zama manomi, kuma zaka zama dan kasuwa, musamman idan ka tantance wani irin amfanin gona kake so ka girbe.

Sana’ar noman kaji ya kasu kashi biyu: ‘Yan kwai, wato kaji da ake kiwon su domin su samar da kwai, ko kuma ‘Yan nama wato brola, kaji na ci. Kowanne ka zaba, dolen-dole sai ka yanke shawarwari na shugabanci da kuma kasuwanci idan har kana so ka samu riba. Ga yadda zaka yi.

1. Ka rubuta tsarin sana’ar: Wannan shine fitilar da zai nuna maka hanyar da ka nufa a wannan sana’a. Duka shirin ka, da burin ka, da kuma yadda zaka cimma wannan buri na rubuce a wannan tsari. Wannan rubutu zai agaza maka wajen fahimtar yadda zaka tafiyar da sana’ar ka daga bangaren manomi, kana kuma daga bangaren ma’aikaci, kuma lauya da akanta duk zasu iya karanta wa su fahimci inda ka dosa.

2. Mallaki fili, jari da kayan aiki: Idan baka da wadannan abubuwa, babu yadda za’a yi kayi kiwon kaji har ka samu riba. Kana bukatar gidan da zaka zuba kajin a ciki, ya danganta da yadda kake so kayi. A cikin keji zaka zuba su, ko a fili zaka kyale su suyi ta yawo? Za kuma ka iya bukatar fili domin girbe abincin da zaka baiwa dabbobin. Kana bukatar kayan aiki domin shara, gyare-gyare da girbe amfanin gona.

3. Ka tantance wadanni irin kaji zaka girbe: To dama akwai kaji iri biyu da aka fi sani, da ‘yan kwai, da ‘yan nama. To akwai kuma wasu da ba’a jin su sosai, kamar kwan da ba’a ci, sai dai a kyankyashe su domin zama ‘yan kwai, ko ‘yan nama. Mafi yawancin lokuta, sana’ar kyakyasar kwai zaman kanta take yi, haka zalika kiwon ‘yan kananan kaji. Akwai kuma bangaren yanka kaji shima, idan har kana sha’awa. Akwai gonakin kaji masu yawa dake da bangarori da yawa.

4. Ka san me aka fi so a inda kake: Idan wajen da kake jama’a sun fi son kaji masu yawo a waje, ba a cikin keji ba, to gwamma ka mayar da hankali akan yadda zaka yi wannan kiwo a maimaikon na keji da ba’a sha’awa.

5. Ka gabatar da kanka ga kwastomomi da sauran jama’a: Ka tallata kanka ta hanyar sanar da su cewa kana sayar da kwai ko nama. Mafi yawancin lokuta, tallata abu da baki yafi rahusa kuma har yanzu shine hanya mafi tasiri wajen talla. Idan kana so, zaka iya biyan kudi a gidan radiyo ko jarida ko wata kafa a tallata sana’ar ka.

6. Ka rubuta duka tsare-tsaren kudi da yadda kudi ke shiga da fita: Kana bukatar wannan domin fahimtar ko kana samun riba, ko kuma a’a.

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...