Ads

Monday, 10 June 2019

DUNIYA MAKARANTA


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto

****Ka aurar da danka duk sadda kake so. Ka aurar da 'yarka duk sadda ta samu miji.
Idan Macce ta samu mijin tsara ba daidai ne ayi masa jinkiri ba.
****Idan Alqur’aninka ya yi qura ka zargi kanka. Duk wanda ya kwana uku bai
karanta Alqur’ani ba lallai ne zuciyarsa za ta bushe.

****Idan ka mutu ma'aikatarka za ta dauki wani ma'aikaci, matarka za ta auri wani namiji, dukiyarka za ta samu wani mamallaki ba kai ba. Ba Abin da za ka je lahira da shi sai aikinka. Gyara lahirarka, kada kyalkyalin duniya ya ruxe ka.

****Ababe uku suna da wuya amma suna da amfani. Kyauta a cikin talauci, da kamun kai a lokacin kadaici, da fadin gaskiya a gaban wanda kake tsoro.
****A lokacin da kake karami kana ganin laifin manya idan suka yi maka gyara, amma da ka girma sai ka gane su ne daidai. A lokacin kana makaranta kana ganin laifin malamai idan suka matsa ka bi doka, da ka zama Malam sai ka gano ashe su ne daidai.
Ka riqa ba da uzuri ga wanda ba matsayin ku daya da shi ba, wataqila watarana za ka
gano shi ne daidai.

No comments:

Post a Comment

FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...