Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto
****Mutum yakan shiga wani yanayi sai ya dauka cewa karshensa ya zo kenan. Amma daga bisani sai ya gane cewa, wannan shi ne farkon jin dadin sa a duniya. Da yawa kofar da kake zaton ta a kulle idan ka tura ta za ka same ta a bude tana jiran isowar ka. Kada ka yanke kauna daga alheri. In da rai da rabo.
****Yi kokari ka mayar da wuninka kyakkyawa duk halin da ka samu kanka a cikin
sa. Idan ka ki ko ka so za ka wuni a cikin sa.
****Magana mafificiya ita ce ambaton Allah. Kyauta mafificiya ita ce ka yi ma wani addu'a. Rana mafificiya ita ce wadda ba ka saba ma Allah ba a cikin ta.
****Ababe masu daraja ba su cika maimaituwa a rayuwar dan Adam ba. Shi ya sa kowane mutum uwa daya kacal gare shi
****Wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Wanda ya sa wani kuka Allah zai sa shi kuka. Duk wanda ya shuka alheri zai ga alheri a rayuwarsa da bayan mutuwar sa.
Idan kuwa ka shuka sharri to sharrin ne za ka girba komai dadewa.
No comments:
Post a Comment