*Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto*
****Nasararka ba ita ce wadda mutane suke fadi ba. Babbar nasararka ita ce
kyakkyawan aikinka wanda Allah kadai ne ya san shi.
****Matsalarka ba ita ce wadda maqiyanka suke fadi ba. Babbar matsala a gare ka ita ce wadda ke tsakanin ka da Allah amma mutane ba su sani ba.
****Mamaki: Idan muka yi sadaka da Naira 500 sai mu gan su da yawa, amma idan muka je da su kasuwa sai su dawo yan kadan. Idan muka yi awa biyu muna ibada sai mu gan su da yawa, amma idan muka yi su a kallon movie ko wasar qwallo sai mu ga sun dawo ‘yan kadan. Idan muna addu'a sai mu kasa dadewa amma idan muna fira sai bakinmu ya bude sosai. Idan muna karanta Alqur’ani sai mu qosa nan take, amma idan
muna chatin sai mu rasa sanin inda lokaci ya tafi. Anya kuwa wannan ba alama ce ta raunin imaninmu ba? Aljanna fa akwai tsada. Mu sabunta imani.
****Yin abubuwa guda uku yana sa ayi wasu uku: Kallo yana sa ayi Zina, jayayya tana sa ayi fada, fushi yana sa ayi wauta.
****Kyauta tana kawo soyayya, kunya tana kawo alheri, tsafta tana ba da lafiya.
Wannan website mun bude shi ne dan watsa duk abinda muka san insha Allahu zai anfani al'umma.
Ads
Wednesday, 5 June 2019
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
FA'IDODIN ALBASA ************************ Da Sunan Allah mai sadar da rahama zuwa ga bayinsa, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayye...
-
Hadisi daga Hasanul Basariy daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace: “Akwai wani mutum daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww) daga cikin...
-
****Babu Abin da yake tabbas a duniya sai Canji. Komai ka gani a yau watarana zai canja daga yadda ka san shi. Komai yana canjawa ban da sar...
-
Lokacin da Shehu Jaha yana alkalanci a birnin Aku Shahar, sai ga wasu mutane sun zo gabansa suna rikici kamar sa naushi juna. Da suka gurfan...
No comments:
Post a Comment